المساعد الشخصي الرقمي

مشاهدة النسخة كاملة : muhimman fatawowi daga malam Jamilu zarewa hukuncin gadon dan zina


طاهر جبريل دكو
_30 _March _2015هـ الموافق 30-03-2015م, 12:49 AM
IDAN KWARTO YA DANGANTAWA KANSA DAN ZINA ZAI IYA CIN GADONSA ?

Tambaya :
Aslm.alkm. Dr. da Allah amin bayani akan dan zina, wanda an san hakikanin wanda ya yi cikin. shin zai ci gado?, za a iya ambatarsa da sunan wanda yayi cikin?,

Amsa:
To dan'uwa malamai sun yi sabani akan wannan mas'alar zuwa maganganu guda biyu :
1. Maganar mafi yawan malamai ita ce : dan zina ba'a danganta shi zuwa kwarto, don haka ba zai ci gadonsa ba, saboda fadin Annabi s.a.w. "Da na mai shimfida ne, shi kuma kwarto ba shi da hakki" kamar yadda Bukari ya rawaito a hadisi mai lamba ta : 6368.
2. Idan har matar ba ta da aure kuma wanda ya yi zinar ya danganta dan da aka samu ta wannan hanyar zuwa gare shi, kuma ba wanda ya ja da shi akan haka, to ya halatta a danganta masa dan, masu wannan maganar sun kafa hujja da cewa : hukuncin da Annabi s.a.w. ya yi na cewa : Yaro ana danganta shi ne ga mai shimfida, yana kasancewa ne ga matar aure, amma wacce ba ta da aure, idan ta yi zina, kuma kwarto ya ce ya ji ya gani, za'a iya danganta shi zuwa gare shi, Wannan shi ne ra'ayin Urwa da Ibnu Siiriin da Ishak dan Rahuya da Ibnul-kayyim .

Wannan yana nuna cewa duk matar da take da miji, idan aka yi zina da ita, to za'a dangantawa mijinta abin da aka samu, saboda hadisin da ya gabata, amma matar da ba ta da miji, to kwartonta zai iya danganta dan aka samu zuwa gare shi a maganar wasu malaman, in har ya danganta kuma, to zai dauki dukkan hukunce-hukuncen da ake bawa cikakken Da.

Allah ne mafi sani

Don neman Karin bayani duba : Zadul-ma'ad 5\374 .

JAMILU ZAREWA
18\2\2015