طاهر جبريل دكو
_30 _March _2015هـ الموافق 30-03-2015م, 12:37 AM
LIMANCIN KURMA ! ! !
Tambaya :
Assalamu alaikum, malam, menene hukuncin bin kurma wanda ba ya ji sallah?
Amsa :
To dan'uwa limancin kurma bai inganta ba, harma wasu malaman sun hakaito ijma'i akan haka, saboda kurma ba zai iya tsayar da wasu daga cikin rukunan sallah ba, kamar kabbarar harama da karatun fatiha da sallama, don haka binsa sallah zai jawo sallar wadanda suke binsa ta zama ba ta cika ba.
Saidai wasu malaman sun tafi akan cewa, ya halatta ya yiwa kurame irinsa limanci.
Allah ne mafi sani.
Don neman Karin bayani duba : Sharhul-kabir na Abdurrahman dan khudaamah 2\38.
Jamilu Zarewa
15\2\2015