تسجيل الدخول

مشاهدة النسخة كاملة : Muhimman fatawowi daga mal jamilu zarewa: Hukuncin kyauta da ribar banki (interest


طاهر جبريل دكو
_16 _March _2015هـ الموافق 16-03-2015م, 07:20 AM
HUKUNCIN KYAUTA DA RIBAR BANKI (INTEREST) !

Tambaya :

Don Allah ya halatta idan banki sun bawa mutum kudin ruwa yayi kyauta da su kamar iyayensa ko yan uwa na jini?

Amsa :
To dan'uwa Allah madaukakin sarki ya haramta riba kuma ya kwashe mata abarka kamar yadda aya ta: 276 a suratul Bakara take nuni zuwa hakan, saidai malamai suna cewa idan ya zama, babu bankin musulunci a gari ya kuma zama dole sai ya ajjiye kudinsa a bankunan da suke ta'amuli da riba, to bai halatta ya ci abin da ya amsa ba na kudin ruwa, amma kuma zai iya gina hanya da su, ko ya baiwa talakawa da miskinai, haka nan zai iya biyawa wasu bashi da su, ko ya gina makarantu, saboda idan aka barwa banki, za su iya taimakawa arna da su, ka ga sai barna ta faru.
Allah ne ne mafi sani.

Don neman Karin bayani duba : Fataawaa Al-islamiyya 2/407.

Jamilu Zarewa
14\2\2015.