المساعد الشخصي الرقمي

مشاهدة النسخة كاملة : Muhimman fatawowi daga mal jamilu zarewa:wai me yasa musulunci ya hana musulma auran crista, amma ya halattawa musulmi auran crista


طاهر جبريل دكو
_16 _March _2015هـ الموافق 16-03-2015م, 07:17 AM
WAI ME YASA MUSULUNCI YA HANA MUSULMA AURAN CRISTA, AMMA YA HALATTAWA MUSULMI AURAN CRISTA ?

Tambaaya :
Malam wasu Arna ne suka mana tambaya a makaranta cewa : Yaya aka yi addinin musulunci ya halattawa namiji musulmi auran crister mace, amma ya hana a baiwa crister namiji auran musulma, malam mun rasa amsar da za mu ba su, shi ne muke so ka taimaka mana, don kar su samu hanyar da za su aibanta addininmu .

Amsa :
To yar'uwa sheik Addiyya mohd Salim ya yi kokari wajan warware wannan mushkilar a karashen tafsirin Adhwa'ul-bayan da ya yi, inda ambaci dalilai guda biyu, wadanda suka hukunta hakan :
1. Kasancewar musulunci shi ne yake yin sama, amma ba'a yin sama da shi, idan crister ya auri musulma, zai zama yana sama da ita, tun da namiji shi ne yake bawa mace umarni, idan ya aure ta, sabanin idan namiji musulmi ne ya auri mace crister, tun da shi zai zama a samanta .
2. Musulmi ya yi imani da Annabi Isa da kuma Injila, wannan zai sa idan ya auri crister ya girmama ta, Shi kuwa crister bai yi imani da Annabi Muhammad s.a.w. ba, don haka zai iya wulakanta musulma idan ya aure ta, tun da bai san darajar addinita ba, wanda hakan zai kai suka sa fahimtar juna, zaman auran ya ta'azzara.

Duba Adhwa'ul-bayan 8/164

Allah ne mafi sani .

Jamilu Zarewa
13/2/2015