طاهر جبريل دكو
_16 _March _2015هـ الموافق 16-03-2015م, 07:13 AM
RABON GADO (2)
Tambaya :
Malam mace ce ta mutu ta bar babarta da 'yan'uwanta shakikai maza, da 'yan'uwanta wadanda suka hada uba daya, da baffaninta, don Allah yaya za'a raba gadon ?
Amsa :
To dan'uwa za'a kasa dukiyar gida shida, inda za'a baiwa uwa kashi daya, ragowar kashi biyar din kuma sai a baiwa 'yan'uwa shakikai, baffani da 'yan'uwan da aka hada uba daya da su ba sa cin gado, mutukar akwai 'yan'uwa shakikai maza .
Allah ne mafi sani.
Jamilu Zarewa
11\2\2015
RABON GADO (3)
Tambaya :
Aslm alkm. barka da iwar haka, ina da tambayoyi (2) Matata ta mutu ta bar ni da yaro da yara mata biyu, babanta, babarta da 'yan'uwanta maza 3 da mata 2, don Allah yaya rabon gadon abin da ta bari yake, sannan kayanta nasawa da kayan daki yana daga ciki abinda za'a rabawa magada. Allah ya saka da alkhairi.
Amsa :
To malam ina rokon Allah ya jikanta, za'a raba dukiyar gida sha biyu, a baka kashi uku a ciki, sai a bawa babarta kashi biyu, babanta shi ma kashi biyu, ragowar kashi biyar din sai a rabawa 'ya'yanta, za su raba abin da aka ba su kashi hudu. Namijin ya dauki kashi biyu kowacce mace ta dauki kashi daya, 'yan'uwanta ba za'a ba su komai ba, saboda yaranta sun ka tange su. Dukkan abin da ta bari za'a raba da shi, har kayan dakinta, tun da yana daga cikin abin da ta mallaka.
Allah ne mafi sani.
Jamilu Zarewa
13/2/2015