تسجيل الدخول

مشاهدة النسخة كاملة : muhimman fatawowi daga mal jamilu zarewa: hukuncin auren kanwar mahaifi wacce su ke kaka daya da shi


طاهر جبريل دكو
_16 _March _2015هـ الموافق 16-03-2015م, 07:04 AM
ZA KA IYA AURAN KANWAR MAHAIFINKA ! !!

Tambaya :
Assalamu Alaykum malan ina da tambaya kamar haka: Kakana wanda ya haifi babana yana da Qani wanda suke baba daya amma ba mamarsu daya ba, toh zan iya auren diyarsa? na kasa fahimtar amsar, don Allah a taimaka min na bashi amsa zuwa safiya,nagode,

Amsa :
To dan'uwa ya halatta ka aure ta, saboda kamar yadda malamai suke cewa : duk makusantan mutum ya haramta ya aure su sai nau'i hudu kawai ya halatta ya aura , wato : 'ya'yan baffa, 'ya'yan gwaggo, sai 'ya'yan kawu da 'ya'yan inna, kaga ita wannan da kake so ka aura tana makwafin 'yar baffa ne, don haka sai ya halatta a aure ta.
Allah ne mafi sani.

Don neman Karin bayani duba : Majmu'ul fataawah na Ibnu-taimiyya 32\62 .