تسجيل الدخول

مشاهدة النسخة كاملة : muhimman fatawowi daga mal jamilu zarewa: wane sahabi ne mahaifinsa da kakansa da dansa duk sahabbai?


طاهر جبريل دكو
_16 _March _2015هـ الموافق 16-03-2015م, 06:52 AM
SAHABI, DAN SAHABI, JIKAN SAHABI, BABAN SAHABI ! ! !

Tambaya:
Aslm, don Allah akwai sahabin da kakansa sahabi ne, babansa sahabi, dansa kuma sahabi ?, ina son karin bayani malam ? .

Amsa:

To malam sahabin da yake kakansa sahabi, dansa sahabi, babansa sahabi, shi ne : Abdurrahman dan Abi-bakr bn Abi Khuhafah kamar yadda Ibnu Salah da Ibnul-jauzy suka ambata. Saboda mahaifinsa Abubakar sahabi ne, hakanan kakansa Abu khuhafah shi ma sahabi ne sannan dansa Muhammad sahabi ne, Ibnu Hajar yana cewa : Ba mu san mutum hudu da 'ya'yansu wadanda suka ga Annabi s.a.w ba sai wadannan.
Abin da yake nufi shi ne : Muhammad da mahaifinsa Abdurrahman da kakansa Abubakar da kakansa na biyu Abu-kuhafah dukkansu sun ga Annabi s,a,w, don haka su kadai suka samu wannan darajar, Allah ya kara musu yarda .
Don neman karin bayani duba tarjamar Muhammad Bn Abdurrahman Bn Abi-bakr Bn Abi-khuhafah a Usudul-gabah a lamba ta : 6083.