طاهر جبريل دكو
_16 _March _2015هـ الموافق 16-03-2015م, 06:39 AM
NA KARBI KYAUTA DAGA KARUWA , KO YA HALATTA NA AMFANA DA ITA ?
Tambaya:
assalam,malam akwai hujjar da ta kore kar6ar kyauta daga karuwa ?
Amsa:
Tabbas Annabi s.aw. ya haramta cin kudin karuwa, wanda ta samu ta hanyar karuwanci, kamar yadda hakan ya zo a hadisi mai lamba : 1567, wanda Muslim ya rawaito
Saidai malamai suna cewa : Duk wanda ya zama a cikin dukiyarsa akwai halal da haram, to idan ya maka kyauta za ka iya amsa, mutukar ba ka tabbatar daga haram ya dauko ya baka ba, saboda Annabi s.a.w. ya yi mu'amala da yahudawa kuma a cikin dukiyarsu akwai halal da haram, har ma ya mutu silkensa na yaki yana jingene a wajansu, Don neman Karin bayan duba Al-muhallah na Ibnu Hazm 6/184.
Allah ne mafi sani