طاهر جبريل دكو
_16 _March _2015هـ الموافق 16-03-2015م, 06:28 AM
HUKUNCIN ADDU'A TSAKANIN HUDUBAR JUMA'A TA FARKO DA TA BIYU !!
Tambaya:
Assalamu alaikum mal ya gida ya kuma dawainiya dafatan kowa lfy Allah yasa haka ameen, mal ina da tambaya ne akan halaccin addu'a da akeyi tsakanin huduban farko da na karshe, Allah yasaka alkhairi.
Amsa :
To dan'uwa Annabi s.a.w. yana cewa: " A ranar juma'a akwai wani lokaci wanda babu wanda zai dace da shi, ya roki Allah a lokacin , face sai ya amsa masa" kamar yadda Bukhari ya rawaito a hadisi mai lamba ta: 893.
Malamai sun yi sabani game da wannan lokacin zuwa wajan zantututuka arba'in, kamar yadda Ibnu Hajar ya hakaito a Fathul-bary, 2\419, daga cikin wadannan maganganun akwai cewa : tsakanin hudubobin juma'a guda biyu lokacin yake fadowa.
Don haka wasu malaman suke ganin mustahabbancin yin addu'a tsakanin hudubobi biyu, saboda musulmi zai iya dacewa da wancan lokacin mai falala.
Allah ne mafi sani.
Jamilu Zarewa
2\3\2015
DAGA HANNU A MAKABARTA YAYIN ADDU'A GA MATATTU ! ! ! !
Amsa:
Tanbaya malam.Malam meye hukuncin mutun in yamutu in an kaishi makabarta wasu suke daga hannu suna addua sai su shafa su tafi, nama wani malami tambaya ya ce ba daidai ba ne, ni kuma tunanina daga hunnun ayi addua shine mafi rinjaye, malam menene gaskiya ?
Amsa:
To dan'uwa ya tabbata a hadisin Muslim mai lamba ta : 974 cewa : Annabi s.a.w. ya ziyarci makabartar Baki'a ya kuma daga hannu har sau uku yayin addu'a ga mamatanta"
Hadisin da ya gabata yana nuna mustabbancin daga hannu yayin addu'a ga mamaci a makabarta.
Nawawy yana cewa Akwai hadisai da yawa wadanda suka zo akan daga hannu yayin addu'a, don haka duk wanda ya iyakance wuraren da Annabi s.a.w. ya daga hannaye, ya yi mummunan kuskure" Almajmu'u 3\489.
Saidai malamai suna cewa : yin addu'ar jama'a da murya daya a makabarta na daga cikin bidi'o'in da ba su da asali.
Allah ne mafi sani
Jamilu Zarewa
2\3\2015
FALALAR DASA BISHIYA !
Tambaya :
Assalamu alaikum, Ya sheik shin idan mutum ya gina gidansa kuma ya dasa bishiyoyi a gidan nasa, duk wanda ya amfana da gidan da bishiyoyin yana da lada kamar, sadaqa mai-gudana yayi. ?
Amsa :
Tabbas dasa bishiya na daga cikin sadaka mai gudana, saboda fadin Annabi sa.w "Ba wani musulmi da zai dasa bishiya, wani mutum ko tsuntsu ya ci, face sai ya zamar masa sadaka, Muslim ya rawaito a hadisi mai lamba t a : 2904.