طاهر جبريل دكو
_23 _February _2015هـ الموافق 23-02-2015م, 12:43 AM
SHAFA FUSKA BAYAN KAMMALA ADDU'A ! !
Tambaya :
Malam menene hukuncin shafa hannu a fuska bayan gama addu'a.
Amsa:
To dan'uwa hadisi ya zo daga Umar- Allah ya yarda da shi- cewa: "Annabi s.a.w. idan ya daga hannayansa ya yi addu'a ba ya mayar da su, har sai ya shafa su a fuskarsa" Sunanu Attirmizi : 3386.
Wannan hadisin ya zo da hanyoyi masu yawa, saidai dukkansu suna da rauni, wannan yasa malaman hadisi suka yi sabani game da ingancin shi, Ibnu Hajara ya kyautata shi, saboda ya zo ta hanyoyi da yawa, kamar yadda ya bayyana haka a Bulugul-maraam a hadisi mai lamba ta : 1345.
Akwai wadanda suka raunana shi saboda suna ganin hanyoyin da yazo da su masu yawa, ba su kai su karfafe shi ya zama Hasan ba, wannan shi ne ra'ayin Ibnu Taimiyya kamar yadda ya bayyana haka a Majmu'ul fataawaa 22\509, haka Albani a Silsila Sahiha 2\146.
Malaman Fiqhu sun yi sabani game da shafar fuska bayan addu'a, wasu sun tafi akan mustabbancinsa, saboda sun gamsu da kyautatawar da Ibnu-hajar ya yiwa hadisin, kamar Ibnu Bazz a daya daga cikin fatawoyinsa, akwai kuma wadanda suka tafi akan cewa ba za'a ayi ba, saboda rashin ingancin hadisan da suka zo akan haka.
Abin da na fahimta a wannan mas'alar shi ne ba za'a aibanta wanda ya shafa fuskarsa ba bayan addu'a, tunda yana da magabata .
Allah ne mafi sani
JAMILU ZAREWA
3\2\2015.
DAGA HANNU LOKACIN ALKUNUT ! ! !
Tambaya :
Assalamu Alaikum, Malam Jamilu, akwai hujja akan daga hannaye lokacin yin alqunut a sallah, musamman alqunut ta lokacin masifa ? nagode
Amsa :
To dan'uwa, zance mafi inganci shi ne mustahabbancin daga hannu yayin alkunutu, saboda Annabi s.a.w. ya daga hannu a sallar asuba lokacin da ya yi addu'a ga wadanda suka kashe mutum saba'in makaranta, kamar yadda Dabrani ya rawaito a Mu'ujamussagir a hadisi mai lamba ta : 111, kuma Albani ya inganta shi a Irwa'ul-galil 2\181.
Sannan an rawaito hakan daga Umar da Usman da Ibnu Mas'ud, da Abu-hurairah .
Don neman Karin bayani duba Attalkis na Ibnu Hajar 2\40
Allah ne mafi sani.
BACCIN BAYAN SALLAR ASUBA ! !
Tambaya :
Assalamu alaikum, malam INA da wata tambaya shin menene hukuncin yin bacci bayan sallar asuba? Allah ya taimaki malam!
Amsa :
To malam babu wani hadisi ingance wanda ya hana bacci bayan sallar asuba, saidai bayan sallar asuba lokaci ne mai albarka, wannan yasa Annabi s.a.w. idan ya yi sallar asuba baya tashi daga wurin sallar sai rana ta fito, haka ma sahabbansa Allah ya yarda da su, kamar yadda Muslim ya rawaito a hadisi mai lamaba ta : 670, kuma Annabi s.a.w yana cewa : "Allah ka sanyawa al'umata albarka a cikin jijjifinta" Tirmizi a hadisi mai lamba ta : 1212, kuma ya kyautata shi.
Wannan yake nuna cewa lokaci ne mai albarka, wanda bai dace da bacci ba, wannan ya sa ko da rundunar yaki Annabi s.a.w. yake so ya aika, yakan aikata ne a farkon yini saboda albarkar lokacin.
Wasu daga cikin magabata, sun karhanta yin baccin bayan sallar asuba, Urwatu dan Zubair yana cewa : "Idan aka ce min wane yana baccin safe na kan guje shi' kamar yadda Ibnu Abi-shaiba ya ambata a Musannaf dinsa 5\222.
Ya kamata ka shagala da neman ilimi ko kosuwanci a irin wannan lokacin.
Allah ne mafi sani .