ÇáãÓÇÚÏ ÇáÔÎÕí ÇáÑÞãí

ãÔÇåÏÉ ÇáäÓÎÉ ßÇãáÉ : Muhimman fatawowi na malam jamilu zarewa kashi na bakwai


ØÇåÑ ÌÈÑíá Ïßæ
_2 _February _2015åÜ ÇáãæÇÝÞ 2-02-2015ã, 02:45 AM
(97) YAUSHE AKE YIWA YARO KACIYA ? (Dr. Jamilu Zarewa)

Tambaya : Assalamu alaikum malam, ina tambaya ne akan yiwa yaro kaciya shekara nawa ya kamata ayi masa ?.
Amsa : To malam babu wani hadisi ingantacce wanda ya kayyade wani lokaci da za’a yiwa yaro kaciya, saidai malamai suna cewa : babbar manufar yin kaciya ita ce katanguwa daga najasar da za ta iya makalewa a al’aura, wannan ya sa ya wajaba a yiwa yaro kaciya dab da balagarsa, saboda idan ya balaga shari’a za ta hau kan shi kuma tsarkinsa ba zai cika ba, in ba’a yi masa kaciyar ba, daga cikin ka’aidojin malamai shi ne duk abin da wajibi ba zai cika ba sai da shi, to shi ma ya zama wajibi, amma mustahabbi ne ayi masa, tun yana dan karami, saidai wasu malaman sun karhanta yin kaciya ranar bakwai ga haihuwa, saboda akwai kamanceceniya da yahudawa a ciki. Alllah ne mafi sani, Don neman karin bayani duba Fathul-bary : 10/349

(96) SHIN SAYYADINA UMAR YA TABA BINNE ‘YARSHI ? (Dr. Jamilu Zarewa)
Tambaya : Assalamu alaikum malam, shin don Allah ina gaskiyar lamarin da ake cewa : Umar yana kuka wataran kuma sai a ga yana dariya, har aka tambaye shi, sai yake cewa : ya tuna ‘yarsa da ya rufe a zamanin jahiliyya shi ne yake kuka ?
Amsa : To dan’uwa tabbas wannan maganar ta yadu a wajan masu wa’azi da masu huduba akan minbarai, saidai ba ta da tushe, kuma karya ce, saboda abubuwa kamar haka : 1. Masana tarihi sun tabbatar da cewa : matar Umar R.A ta farko a rayuwarsa, ita ce Zainab ‘yar Maz’un wacce ta Haifa masa Hafsan da Annabi s.a.w. ya aura, don haka Hafsa ita ce babbar ‘yarsa, kuma da ita ake masa alkunya, don haka idan bai rufe babba ba daga cikin ‘ya’yansa, ta yaya zai bunne wacce ta zo daga baya ?, tare da cewa : ita kan ta Hafsan an haife ta ne kafin a aiko Annabi s.aw. da shekara biyar, ka ga kenan abin da ta riska na jahiiliyya ba shi da yawa . 2. Wacce ake cewa Umar ya bunneta da ranta, gaba daya littatafan tarihi ba su fadi labarinta ba, ko su kirga ta a cikin ‘ya’yansa ba. 3. Sannan kabilar Adiy wacce Umar ya fito daga cikinta ba su shahara da binne ‘ya’ya mata ba, a zamanin jahiliyya. 4. Dogon bincike ya nuna cewa : babu wannan kissa kwata-kwata a cikin littattafan Ahlussunah, asalinta daga littatafan ‘yan shi’a aka cirota, don haka su ne suka kirkire ta, dama kuma sun saba yin kage ga sahabban Annabi s.aw.
Allah ne mafi sani .
Don neman Karin bayani duba : Dirasa nakdiyya fi shaksiyati Umar 1/111.
ÏÑÇÓÉ äÞÏíÉ Ýí ÔÎÕííÉ ÚãÑ Èä ÇáÎØÇÈ æÓíÇÓÊå ÇáÅÏÇÑíÉ 1/111-112

(95) HUKUNCIN DAUKAR HOTO (Dr. Jamilu Zarewa)
Lawal Adam (http://saninmadafa.com/author/lawaladam/) December 20, 2014 In Fatawowi (http://saninmadafa.com/category/fatawowi/)
Tambaya : Malam menene hukuncin daukar photo graph kamar na kyamara da waya da sauran su ?
Amsa : To ‘yar’uwa Annabi s.aw. yana cewa : “Wadanda suka fi kowa tsananin azaba ranar alkiyama su ne masu suranta mutane kamar yadda Bukhari ya rawaito a hadisi mai lamba ta : 5950, a wani hadisin kuma yana cewa : “Duk mai suranta mutane yana cikin wuta” kamar yadda Muslim ya rawaito a hadisi mai lamba ta : 2110. Saidai malaman wannan zamani sun yi sabani akan wacce irin sura ake nufi a cikin wannan hadisin, shin Photograph zai shiga ciki, ko kuwa ? 1. Akwai wadanda suka tafi akan cewa kowacce irin sura da ake yi ta shiga ciki, don haka bai halatta a dau kowanne irin hoto ba, in ba na lalura ba kamar Pasport ko hoton da ake bukata saboda tabbatar da wani abu . 2. Ya halatta a dauki photo graph, saboda ya zo a wasu hadisan da suke haramta daukar sura cewa : “Su ne wadanda suke kwaikwayon halittar Allah” kamar yadda ya zo a Bukhari a lamba ta : 5610, Shi kuma photo grapp babu kwaikwayon halittar Allah a cikin shi, saboda inuwa ce kawai ake dauka, don haka sai ya halatta, tunda ba sura ce ta hakika ba, sai ya zama daidai yake da mudubi, kuma babu sabani wajan halaccin amfani da mudubi, saboda ganin sura . Zance mafi inganci shi ne rashin yawaita daukar hoto, saboda hotuna na daga cikin hanyoyin da suka jawo aka bautawa wasu, sannan kuma dalilan wadanda suka haramta Photograpp suna da karfi, fita kuma daga sabanin malamai yana da kyau . Don neman karin bayani duba Alminhajj na Nawawy 14\81 da kuma Fataawallajna Adda’ima mai lamba ta : 5807, da fataawa Ibnu-uthaimin lamba ta : 151. Allah ne mafi sani .

(94) AZUMIN ASHURA BA YA KANKARE DUKKAN ZUNUBAI (Dr. Zarewa)
Tambaya :
Malam ina da tambaya, Irin ayyuka na azumin ashura arfa, Misali na ashura kaffarane na shekarar da ta gabata, Shin malam yana kankare manyan zunubai irin su shirka, mua’mala da kudin ruwa da sauransu, Malam yaya maganar magabata game da tambayata ?

Amsa :
To dan’uwa hadisi ya tabbata daga Annabi s.a.w cewa : Azumin ashura yana kankakare zunubin shekara daya” kamar yadda Muslim ya rawaito a hadisi mai lamba ta : 1162.
Malamai magabata suna cewa azumin ashura da na Arfa suna kankare kananan zunubai ne kawai, amma manya sai an tuba Allah yake gafarta su, sun kafa hujja da fadin Annabi s.a.w, inda yake cewa : “Salloli guda biyar da Ramadhana zuwa Ramadhana suna kankare abin da yake tsakaninsu, mutukar an bar manyan zunubai” Muslim a hadisi mai lamba ta : 233 .
Wannan hadisin yana nuna cewa : sallolin farilla da azumin Ramadhana ba sa kankare manyan zunubai, ka ga kuwa ta yaya azumin nafila kamar na ashura da na ranar Arfa zai kankare su ?

Wannan ita ce maganar Nawawy a littafinsa Alminhaj sharhin sahihi Muslim a 4/308, da kuma Ibnul-kayyim a littafinsa : Aljawabul-kafy shafi na : 13 .

Allah ne mafi sani .