ÇáãÓÇÚÏ ÇáÔÎÕí ÇáÑÞãí

ãÔÇåÏÉ ÇáäÓÎÉ ßÇãáÉ : Muhimman fatawowi na malam jamilu zarewa kashi na shida


ØÇåÑ ÌÈÑíá Ïßæ
_2 _February _2015åÜ ÇáãæÇÝÞ 2-02-2015ã, 02:44 AM
(101) AZUMI DA NIYYAR TUNKUDE BALA’IN BAMA-BAMAI (Dr. Jamilu Zarewa)
Tambaya ” Mal. Tambayar ita ce sarkin kano ya bada umarnin yin aximi guda uku saboda wannan iftila’in, Allah ya yaye mana shi, to yau ban yiba amma gobe ina so nayi shine nake so naji shin hakan ya samo asali ne a sunnah ? nagode mal.
Amsa : To malam azumi yana daya daga cikin ayyukan alkairin da za’a iya tawassuli da su don neman afuwa a wajan Allah, saboda yana daga cikin manyan ibadu, kuma Annabi s.a.w. ya kira azumi da cewa : Garkuwa ne, kamar yadda Nasa’i ya rawaito a hadisi mai lamba ta : 2217, sannan mai azumi idan ya yi addu’a, ana amsa masa, kamar yadda hakan ya tabbata a hadisin Tirmizi mai lamba ta : 2525, ka ga wadannan hadisan suna nuna cewa azumi zai iya tunkude musibar bama-bamai da ‘yan ta’adda. saidai ware wasu kwanaki na musamman saboda haka ba shi da asali, a shari’a, amma dai ana iya umartar mutane da su dage da addu’a da kuma duk abin da zai kusantar da su zuwa ga Allah, don samun kariya, kamar yadda za’a iya ce musu su hada da azumi, amma ba tare da an ware musu wasu kwanaki na musamman ba, saboda babu dalilin da ya tabbatar da haka, kuma ba’a samu magabata suna yi ba .
Allah mafi sani.

(99) SHIN YA HALATTA NA TAIMAKAWA CRISTER DA JINI ? (Dr. Jamilu Zarewa)
Tambaya : Assalamu alaekum! Malam dan girman Allah ko ya halatta mutum ya baiwa christa jini a asibiti, ganin cewar christan ya shiga wani hali kuma akwai sanayyah tsakanina da shi?
Amsa : To malam wannan mas’alar tana daga cikin mas’aloli sababbi wadanda ba’a san su ba a can baya, amma kuma Mujamma’u fiqhul-islamy da ke Makka a saminarsu ta takwas wacce aka yi a ranar 19-28 na janairun shekarar 1985, sun tabbatar da halaccin taimakawa crista da jini idan yana rashin lafiyar da ake bukatar hakan, mutukar ana zaman lafiya da shi, saboda hakan yana daga cikin tamakekeniyar da Allah ya yi umarni da ita, kamar yadda Allah yake cewa a cikin suratul-Mumtahanah aya ta : 8, “Allah ba ya hana ku ku kyautatawa kafiran da ba su yake ku ba” sannan hakan zai kara fito da alkairin da yake cikin musulunci, ta yadda wasu za su yi sha’awarsa . Amma idan akwai yaki tsakaninsa da musulmai to bai wajaba a ba shi ba, sai in ya kasance ribatacce ne a tsakanin musulmai, ko kuma ana tunanin hakan zai iya jawowa ya shiga musulunci . Allah ne mafi sani.
Don neman Karin bayani duba Fatawaa Nurun Aladdarb : 1/376.

(98) DALIBAI SUNA MIKEWA SABODA ZUWANA, KO YA HALATTA ? (Dr. Jamilu Zarewa)
Tambaya : Mal. Ina teaching practice ne yanzu, kuma idan na je aji yara suna mikewa damin gaishe ni, mal. na barsu su cigaba ko na dakatar da su ?
Amsa : To dan’uwa akwai malaman da suka ta fi akan cewa makaruhi ne a mikewa malami, akwai kuma wadanda suka haramta, akwai wadanda kuma suka halatta. Saidai maganar da ta fi ita ce bai hallata malami ya nemi a mike masa ba, saboda fadin Annabi s.a.w. ” Duk wanda ya so mutane su mike masa to ya tanaji wurin zamansa a wuta” kamar yadda tirmizi ya rawaito shi kuma ya kyautata shi a hadisi mai lamba ta : 2755, Albani kuma ya inganta shi a silsilatussahihah lamba ta : 5957. Amma idan aka mikewa malami ba tare da ya nema ba, to wannan babu laifi ga wanda ya mike da wanda aka mike saboda shi, domin ya zo a hadisi cewa : Annabi s.a.w. ya nemi mutanen Madina su mikewa Sa’ad, lokacin da ya gabato” kamar yadda Bukari ya rawaito a hadisi mai lamba ta :2878, wannan sai yake nuna halaccin mikewa ga mutane masu falala kamar malamai da manyan mutane, lokacin da suka gabato .
Don neman karin bayani, duba : Alminhaj na Nawawy 12/440, da Mirkataul mafaatiih sharhu mishkatil-masaabiih shafi na : 2972 BABU ALKIYAM . . Allah ma fi sani