ÊÓÌíá ÇáÏÎæá

ãÔÇåÏÉ ÇáäÓÎÉ ßÇãáÉ : Muhimman fatawowi na malam jamilu zarewa kashi na biyu kashi na hudu


ØÇåÑ ÌÈÑíá Ïßæ
_2 _February _2015åÜ ÇáãæÇÝÞ 2-02-2015ã, 02:23 AM
(105) ADADIN SHAHIDAI DA INGANCIN SHAHADAR WACCE TA MUTU A NAKUDAR CIKIN SHEGE ? (Dr. Jamilu Zarewa)
Tambaya : Assalamu alaikum Allah ya gafarta Mallam don Allah ina Matsayar Malamai akan wadannan Mas’aloli, tare da ambaton dalilai daga Qur,ani/Hadithi : Mutane nawa ne Ya tabbata a Alqur,ani/Hadithi Sunyi Mutuwar Shahada? Domin wani Dalibi abokina ya ce: Albani ya ya Ambaci : 9 a cikin AHKAMIL JANA’IZ na duba ban gani ba, sannan idan Mace ta Mutu ayayin haihuwar Cikin Shege, shin itama ta yi Shahada?
Amsa : To dan’uwa shahidai suna da yawa: sun haura guda tara : Ibnu- hajar yana cewa : “Mun tattara hadisan da suka yi bayani akan shahidai sai muka samu sama da nau’i ashirin, na shahidai, Fathul-bary 6\43 hakanan Suyudi a littafinsa mai suna : Abwabissa’adah fi asbabi assa’adah, ya kawo sama da guda talatin
Ka ga daga ciki, akwai wanda ya mutu a fagen daga, da wanda ya mutu da ciwon ciki, sai wanda ya mutu a lokacinn kwalara sai kuma wanda ya mutu ta hanyar rusowar gini, sai wanda ya nutse a ruwa, Hakanan wanda ya mutum wajan kare dukiyarsa, da wanda kunama ko mijiji ya harba, sai ya yi ajlinsa, haka matar da ta mutu wajan haihuwa, dama wanda namun daji suka cinye shi Haka wanda aka kashe shi saboda kare iyalansa, duk wadannan sun tabbata a cikin hadisai . Saidai wasu malaman suna ganin akwai sharuda kafin mutum ya samu shahada :
Daga ciki kada ya zama : Ba ta hanyar gangaci ya mutu ba, kamar mutumin da bai iya ruwa ba, ya shiga kogi, sai ya mutu, sannan kar ya zama ta hanyar sabo ya isa zuwa shahadar, kamar matar da ta mutu wajan nakudar cikin shege, ko bawan da ya gujewa mai gidansa, sai ya mutu a hanya, wasu kuma suna ganinin hakan ba sharadi ba ne, tun da hadisan ba su kayyade ba. Don neman Karin bayani duba : Fataawal-kubra na Ibnu-taimiyya 3\22 da Mugni A l-muhtaj 3/166
Allah ne mafi sani

(106) SHIN WANDA YA YI SALLAH BABU ALWALA KAFIRI NE ?(Dr. Jamilu Zarewa)
Tambaya Salm dan’uwa kuma malamina ga tambaya naji wata fatawa wacce ba ni da ilimi akanta, wai idan mutun ya yi sallah babu Alwala wai hukuncinsa sai ya sake kalmar shahada ta shiga musulunci, menene ingancin wannan maganar ? Allah ya taimaka Amiin.
Amsa : To malam wannan maganar ta shahara a wajan mutane, saidai a wajan malamai yin sallah babu alwala ya kasu kashi biyu : Idan ya aikata, amma bai halatta hakan ba, ya san ba daidai ba ne, kamar ya aikata saboda kasala, wannan kam bai kafirta ba, saidai ya aikata babban zunubi. idan ya aikata yana mai halatta hakan, ko kuma saboda izgilanci ga addini, sannan ba jahili ba ne, ba shi kuma da wani ta’awili, tabbas wannan aikin kafirci ne, har ma malamai da yawa sun hakaito ijma’i akan kafircin wanda ya yi hakan, saboda akwai karyata shari’a a ciki, da kuma wulakantata . Allah ne mafi sani
Duba : Almajmu’u na Nawawy 2\84 da minhajussunnah 5\204

(107) AN KONA MIN GIDA A RIKICI, KO YA HALLATA NA AMSHI RANCEN BANKI DON NA SAKE GINAWA ?(Dr. Jamilu Zarewa)
Tambaya : Da fatan malam ya tashi lafiya ina da tambaya kamar haka : sakamakon konamun gida da sauran kadarorina da aka yi, a rikicin Boko haram, saboda haka ya sa ba ni da gida, gashi ina da mata uku da ‘ya’ya (11), wannan lalurin ya kai na karbi loan a bank don gina gida ?
Amsa : To dan’uwa ina rokon Allah ya mayar maka da alkairi, ya sa hakan ya zama kaffara ga zunubanka, saidai kamar yadda ka sani yawancin bankuna ba sa bayar da rance dole sai da ruwa wato riba, ita kuma riba tana daga cikin abubuwan da Allah ya kwashewa albarka, kamar yadda hakan ya zo a suratul Bakara aya ta :276, sannan Annabi s.a.w ya kirga ta cikin abubuwa masu hallakarwa, kamar yadda Bukhari ya rawaito hakan a hadisi mai lamba ta : 6465 . Tabbas kana cikin babar matsala, saidai hakan ba zai halatta maka ka ci irin wannan rancen ba, saboda bai kai lalura ba a wajan malaman sharia, kwamitin fatawa na din-din, a kasar Saudiyya, sun tabbatar da cewa : ya haramta ga mutum ya karbi rancen banki mai ruwa saboda gina gida, saboda hakan yana shiga cikin ribar da Allah ya haramta, gashi kuma zai iya warware matsalar da yake ciki ta hanyar amsar gidan haya, wannan yake nuna yana da mafita. Dan’uwana, duk wanda ya ji tsoron Allah, tabbas zai sanya masa mafita, ta inda ba ya zato, duk mutumin da ya bar abu don Allah, to zai musanya masa da wanda ya fi shi alkairi, shiga gidan haya a wajanka ya fi maka karbar ribar da za ta zamar maka alakakai tun a duniya. Don neman Karin bayani duba fataawa Alajna Adda’imah : 13/385 .
Saidai idan duk hanyoyin sun toshe, ya halatta ka amshi rancen gwargwadon lalura, saboda fadin Allah madaukaki, “Kuma tabbas ya bayyana muku abin da ya haramta muku, sai fa idan kun shiga cikin kunci ba yadda za ku yi”, Suratu Al’anam aya ta :119, saidai ya wajaba ka bi duk hanyoyin da kake da su kafin ka yi aiki da wannan ayar.
Allah ne ma fi sani