تسجيل الدخول

مشاهدة النسخة كاملة : Me ya faru a karbala 3


طاهر جبريل دكو
_16 _January _2015هـ الموافق 16-01-2015م, 07:50 AM
ME YA FARU A KARBALA 3
Daga Dr.Mansur [H]
Wane ne YAZIDU?
Sunansa YAZIDU Dan Mu'awiyah Dan Sakhr
(Abu Sufyan) Dan Harb Dan Umayyah Al
Umawy Al Qurashie. Ana yi masa alkunya da
Baban Khalid.
Mahaifiyarsa ita ce Maisun 'yar Bahdal daga
kabilar Kalbu, daya daga cikin kabilun
Kuraishawa masu karfi a wancan lokaci. Ta
rabu da mahaifinsa tana dauke da cikinsa, sai
ta yi mafarkin wata ya fito daga jikinta. Masu
Fassara suka ce mata in har mafarkinki ya
tabbata za ki haifi sarki. Hakan kuwa aka yi.
An haifi YAZIDU a shekara ta 26H a zamanin
halifancin sayyidina Usmanu Dan Affan.
YAZIDU ya tashi a gidan sarauta, domin ko
da aka haife shi mahaifinsa yana gwamnan
Sham. Ya samu tarbiyyar jihadi domin tun
yana matashi dan shekaru 24 ya jagoranci
runduna mafi girma da ta fatattaki Rumawa
kuma ta kwace hedikwatarsu
"Qustantiniyah". Daga nan ne kuma sunan
YAZIDU ya fara fitowa har ya yi tashe a
tsakanin matasa. A nan ne kuma ya samu
tasa daraja daga Hadisin Ummu Haram bint
Malhan Matar sayyidina Ubada bin As Samit
wacce ta ce ta ji Manzon Allah Sallallahu
Alaihi Wa Alihi Wasallam na cewa "Rundunar
farko da zasu yi yaki a teku daga cikin
al'ummata Allah ya gafarta masu". Ta ce,
Manzon Allah ina cikin su? Ya ce, eh. Kina
cikinsu. Sannan ya ce "Rundunar farko da
zasu ci birnin Qaisar daga cikin al'ummata su
ma Allah ya gafarta masu". Ta ce, Manzon
Allah ina cikin su? Ya ce, a'a. (Sahihul
Bukhari, Hadisi na 2924).
Wannan Hadisi ya hada falalar YAZIDU da
babansa gaba daya. Domin kuwa babansa
Mu'awiyah ne ya fara jagorantar Rundunar
farko da ta yi jihadi da Rumawa a teku,
zamanin sarki Usmanu a shekara ta 27H. A
cikin rundunarsa kuwa har da irin su
Miqdadu Dan Amru da Shaddadu Dan Ausu
da Abu Dharril Gifari da Ubada Dan Samit
tare da wannan matar da ta gamu da ajalinta
kai tsaye bayan gama yakin.
Shi kuma YAZIDU shi ne ya ci babban birnin
Qustantiniyah a shekara ta 52H.
Qustantiniyah kuwa ita ce birnin Qaisar a
zamanin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa
Alihi Wasallam. A cikin sojojin wannan
runduna tasa kuwa har da wasu fitattun
sahabbai irin su Ibnu Umar da Ibnuz Zubair
da Ibnu Abbas da Abu Ayyub al Al Ansari,
mai masaukin Manzon Allah Sallallahu Alaihi
Wa Alihi Wasallam, Wanda kuma ya cika kafin
kammala yakin.
(Duba Fathul Bari na Al Hafizh Ibnu Hajar
6/120 da kuma Al Bidayah Wan Nihaya na
Ibnu Kathir 6/249).
Kafin haka YAZIDU ya yi Amirul Hajji na
musulmi baki daya a shekara ta 50H.
Ba zamu yi mamaki ba idan muka ga
mahaifinsa ya zabe shi a matsayin Yarima.
To, amma ko mene ne ya sa aka zabe shi
alhalin akwai wadanda suka fi shi daraja irin
su HUSAINI jikan Manzon Allah Sallallahu
Alaihi Wa Alihi Wasallam da su Ibnu Umar da
makamantansu?
Wannan ita ce tambayar da zamu amsa a
nan gaba Sa'annan mu dawo ma rikicin
mawallafa da takin sakar su a kan wannan
dan taliki YAZIDU kafin mu fantsama a cikin
maganar rikicin da ya hada shi HUSAININ da
YAZIDU wanda a sanadiyyarsa Allah ya ba
HUSAINI shahada.