طاهر جبريل دكو
_16 _January _2015هـ الموافق 16-01-2015م, 07:44 AM
ME YA FARU A KARBALA 2
Daga Dr.Mansur [H]
Assalamu alaikum jama'a.
Ina kara jaddada barka da sallah a gare ku
gaba daya. Allah ya karbi ibadarmu.
Zamu ci gaba da darasi na biyu a yau in sha
Allah.
Tun da farko zai yi kyau mu soma da
takaitaccen tarihin mutane biyu wadanda
zancen Karbala yake kewaya a kan su. Su ne:
Sayyidina HUSAINI bin Ali da kuma YAZIDU
dan Sayyidina Mu'awiyah.
Wane ne HUSAINI?
Shi ne jikan Manzon Allah Sallallahu Alaihi
Wasallam HUSAINI Dan Ali Dan Abu Dalib
Dan Abdulmuttalibi Dan Hashimu Al Hashimi.
Mahaifiyarsa ita ce Fatimah Diyar Manzon
Allah Sallallahu Alaihi Wasallam.
An haife shi a cikin watan Sha'aban na
shekara ta hudu bayan hijira.
(watanni 11 ke tsakanin sa da wansa Al
Hasan).
Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam ne
ya sanya masa suna, ya kuma yanka masa
rago.
A Lokacin wafatin Manzon Allah Sallalahu
Alaihi Wasallam HUSAINI na da shekara 6 da
wata 7.
HUSAINI ya fi kowa kama da Manzon Allah
Sallallahu Alaihi Wasallam ta kasan jikinsa.
Amma Al Hasan ya fi shi kama da shi ta
saman jiki.
Sun tashi kamar tagwaye saboda kusancin
shekarunsu kuma Manzon Allah Sallallahu
Alaihi Wasallam ya kasance yana son su da
kaunar su irin so da kaunar da ba sa
boyuwa. Ya kan kuma yi musu addua yana
cewa, "Ya Allah! Hakika ina son su, Ya Allah
kai ma ka so su".
Wannan ya sa masu kwarjini da kauna ba na
wasa ba a wurin Sahabbai wadanda kaunar
da suke ma Manzon Allah Sallallahu Alaihi
Wasallam ta sa suna son duk abinda yake so
kuma yake kauna.
HUSAINI ya yi tarayya da Dan uwansa Al
Hasan a wata falala wadda suka kebanta da
ita, ita ce kasancewar su shugabannin
matasan aljanna.
(Al Jami' na Tirmidhi, Hadisi na 3768 da Al
Musnad na Ahmad (3/3 da 3/62) da Al
Mustadrak na Hakim (3/167). Kuma Tirmidhi
ya inganta shi.