المساعد الشخصي الرقمي

مشاهدة النسخة كاملة : *** takutaha vs mauludi ***


طاهر جبريل دكو
_16 _January _2015هـ الموافق 16-01-2015م, 07:34 AM
*** TAKUTAHA VS MAULUDI ***
IMAMU MALIK BIN ANAS (R) ya ce: duk abinda be zama Addini a lokacin SAHABBAI ba to ba zai taba zama Addini a wannan zamani ba,
Haba 'yan uwa 'yan Dariqa TIJJANIYYA da QADIRIYYA shin akwai inda aka halatta a hade Mata da Maza banda wajen Arfa ???
Amma kuma kuke cakudewa da sunan Bikin TAKUTAHA ko MAULUDI ???
Hadisi ya Tabbata daga ABDULLAHI IBN AMR, (R.A.) ya ce: MANZON ALLAH (S.A.W.) ya ce: " ALLAH bai aiko wani ANNABI ba, face ya kasance haqqi ne a kan wannan Annabin ya nuna wa Al'ummarsa Alkhyrin da ya sani gare su, kuma ya yi musu gargadi daga sharrin da ya sani gare su". MUSLIM ya ruwaito shi a cikin Sahinsa.
Shin ANNABI (S.A.W.) be isar da sako duka bane har kuka Qirqiro da Maulud alhalin shi beyi ba be ma san shi ba ??
Ga shi kuma Allah da kansa yana cewa:
" A YAU, NA KAMMALA MUKU ADDININKU, KUMA NA CIKA NI'IMATA A KANKU, KUMA NA YARDA DA MUSULUNCI YA ZAMA ADDINI A GARE KU" (Al-Ma'idah, aya ta 3).
Kuma Qirqiro irin wadannan taruka na MAULIDI ko TAKUTAHA, yana fahimtar da cewa ALLAH, (S.W.T.) Bai cika Addini ba ga Al'ummar kenan, Kuma MANZON ALLAH (S.A.W) Bai isar wa Al'umma abin da ya kamata su yi aiki da shi ba, har sai da wadannan 'yan bayan suka zo suka Qirqiri wani abu a cikin shari'ar ALLAH wanda ALLAH bai yi umarni da shi ba, suna riyawar cewa wannan yana daga cikin abin da zai kusanta su zuwa ga ALLAH.
To, babu shakka kuwa wannan abu ne mai hatsarin gaske, kuma yiwa ALLAH da MAZONSA (S.A.W) Fito-na-fito ne.
Haqiqa ALLAH ya kammala Addini ga bayinSa, kuma ya cika ni'ima a kansu.
Kuma sananne ne cewa ANNABINMU, (S.A.W) shi ne fiyayyen ANNABAWA, kuma shi ne cikamakinsu, kuma ya fi dukkansu kammala isar da Manzanci, da kuma yin Nasiha.
Da kuwa rayar da bukuwan MAULIDI yana daga cikin Addini, da ALLAH (S.W.T) Ya yarda da shi, kuma da MANZO (S.A.W) ya bayyana shi ga Al'umma, ko kuma da shi ya yi MAULIDIN a cikin rayuwarsa, ko kuma da SAHABANSA, (R.A) sun yi shi.
Tun da kuwa ba'a samu 1 daga cikin wadannan abubuwa ya faru ba, daga nan za a san cewa MAULIDI da Taron TAKUTAHA basa cikin Musulunci ko kadan, kuma su suna daga cikin Qirqirarrun al'amura wadanda MANZO (S.A.W) ya tsoratar da Al'ummarsa daga gare su.
Kamar fadinsa (S.A.W) A cikin khudubar Juma'a: "Bayan haka, lallai fiyayyen Zance shi ne Littafin ALLAH, kuma fiyayyiyar shiriya ita ce Shiriyar MUHAMMAD (S.A.W) Kuma mafi sharrin Al'amura sune wadanda aka QIRQIRO, kuma dukkan BIDI'A bata ce". MUSLIM ya ruwaito shi a cikin Sahihinsa.
ALLAH YA NUNA MANA GASKIYA YA BAMU IKON BINTA, YA NUNA MANA QARYA YA BAMU IKON GUJE MATA.