طاهر جبريل دكو
_18 _December _2014هـ الموافق 18-12-2014م, 03:50 AM
شروط "لا إله إلا الله "
SHARUDDAN LA'ILAHA-ILLA-LLAHU
MATASHIYA
Dukkan godiya ta tabbata ga Allah ubangijin talikai, kuma salati da sallama su tabbata ga mafi darajan annabawa kuma shugaban manzanni, annabinmu Muhammadu (صلى الله عليه وسلم) da alayensa da sahabbansa baki daya.
Bayan haka: lallai ba abu bane boyayye ga wanda ya ke da sani acikin littafin Allah da sunnar ManzonSa (صلى الله عليه وسلم) abin da kalmar shahada ta ke da shi na muhimmanci, domin ita ce rukuni na farko kuma mafi girma daga cikin rukunnan musulunci. Saboda haka ba a la'akari da wata ibada har sai an gina ta akan shaidawa babu abin bauta bisa cancanta sai Allah, kuma saboda tabbatar da ita Allah Ya halicci (dukkanin) halittu ya kuma aiko mazanni ya saukar da littattafai, saboda haka ta zama ita ce da'awar manzanni baki dayansu. Allah (تعالى) Ya ce:
{وَمَا أَرْسَلْنَا مِنْ قَبْلِكَ مِنْ رَسُولٍ إِلَّا نُوحِي إِلَيْهِ أَنَّهُ لَا إِلَهَ إِلَّا أَنَا فَاعْبُدُونِ} [الأنبياء: 25]
Ma'ana:"Kuma ba Mu aiko wani manzo ba gabanin ka face Mun yi wahayi gare shi cewa babu abin bautawa da bisa cancanta sai Ni, saboda haka ku bauta mi Ni" Suratul Ambiya'i aya ta 25.
Kuma ita ce mabudin musulunci, da ita ce ake samun kariya game da jini da dukiya, kuma da tabbatar da ita ce ake samun tsira daga wuta, kuma ba za ta amfani wanda ya yi furuci da ita ba har sai ya cika sharuddanta, saboda haka naso in ambaci wadannan sharudda a cikin harshen hausa da bayanin ma'anar ko wane sharadi bisa takaitawa da fatar Allah Ya anfani duk wanda ya karanta ko ya saurari mai karantawa da ni da na rubuta shi daga abin da na fa'idantu da shi na ilimin malamai magabata da ma wadansu da su ke raye duk Allah Ya sa an yi shi bisa tsarkin niyya Ya kuma sa ya zama sanadin tsira gare mu baki daya.
Binciken ya kamala ne daren alhamis 25 ga watan Safar hijira na shekara 1436.
Rubutun nawa zai dauki salo ne kamar haka:
Matashiya: zai kunshi abubuwa kamar haka.
Nafarko:ma'anan la'ilaha-illa-llahu da ma'anan hakikance ta.
Nabiyu:Rukunnanta
Na'uku:Sharuddanta
Sharadi na farko; sani wanda ke kore jahilta
Sharadi na biyu; yakini mai kore shakka.
Sharadi na uku; ikhilsi mai kore shirka.
Sharadi na hudu; gaskiya mai kore karya.
Sharadi na biyar; soyayya mai kore kiyayya.
Sharadi na shida; jawuwa (wato sallamawa mai sa cikakkiyar biyayya) wanda ke kore barin (biyayya da kangara)
Sharadi na bakwai; karba wanda ke kore mayarwa.
SHIMFIDA
Zai yi kyau kafin a kirgo sharuddan wannan kalmar ayi nuni zuwa ga ma'anarta da ma'anar hakikance ta da rukunnanta.
NA FARKO:MA'ANARTA DA MA'ANAR HAKIKANCE TA.
Ma'anarta shi ne; babu abin bawtawa bisa cancanta sai Allah, Shi kadai Yake, ba Shi da abokin tarayya.
Kalmar ta la'ilaha illa llahu ta na bayyana cewa: lallai duk wani abin bauta koma bayan Allah, abin bauta ne na karya baa bin bauta ne da aka bauta wa saboda cancanta ba, kuma lallai abin bauta na gaskiya, shi ne Allah Shi kadai babu abokin tarrayya gare shi.
Allah (سبحانه وتعالى)Ya ce:
{ ذَلِكَ بِأَنَّ اللَّهَ هُوَ الْحَقُّ وَأَنَّ مَا يَدْعُونَ مِنْ دُونِهِ هُوَ الْبَاطِلُ وَأَنَّ اللَّهَ هُوَ الْعَلِيُّ الْكَبِيرُ (62)}
Ma'ana:"Wancan! Saboda lallai ne Allah Shi ne gaskiya kuma lallai ne abin da su ke kira koma bayansa shi ne karya kuma lallai Allah Shi ne madaukaki mai girma" Suratul Hajji aya ta 62.
Shekh Abdulmuhsin –Allah Ya kare shi – a cikin sharhinsa na mukaddimar risala ya ce:" fadin ibnu abi zaidin –Allah Ya yi masa rahama- 'lallai Allah abin bauta ne guda daya, babu abin bauta koma bayansa' shi ne ma'anan kalmar tauhidi (la'ilaha illa llahu) kuma ta na kunshe da gamammiyar korewa da kebantacciyar tabbatarwa, gamammiyar korewan kuwa, korewa ne ga duk wani abin bauta koma bayan Allah, kebantacciyar tabbatarwa kuwa ita ce tabbar da cancantar bauta ga Allah Shi kadai.
Abin nufi shi ne kore samuwar wani abin bauta bisa cancanta koma bayan Allah, saboda ababen bauta na karya suna nan da yawa, shi ya sa Allah ya ambata game da kafirai cewa lallai su suna cewa:
{أجَعَلَ الْآلِهَةَ إِلَهاً وَاحِداً إِنَّ هَذَا لَشَيْءٌ عُجَابٌ}
Ma'ana: "shin ya sanya gumaka duk su zama abin bauta guda daya? Hakika wannan abu ne mai matuar ban mamaki" Suratu Sad aya ta 5.
((Duba sharhin mukaddimar risala ta malam mai suna katful janiddani shafi na 58 da59)).
Wannan ayar ta na nuni izuwa ga yadda kafiran kuraishawa suka fahimta daga wannan kalmar cewa ta na nufin rusa bautan gumaka dukkaninsa kuma ta na iyakance bauta ga Allah Shi kadai don haka su ka ki karbanta, haka nan mutanen (Annabi) Hudu yayin da (Annabi) Hudu (عليه السلام) ya kiraye su zuwa ga furta la'ilaha illa llahu sai suka ce:
{أَجِئْتَنَا لِنَعْبُدَ اللَّهَ وَحْدَهُ وَنَذَرَ مَا كَانَ يَعْبُدُ آبَاؤُنَا} [الأعراف: 70]
Ma'ana: "Shin ka zo gare mu ne domin mu bauta wa Allah Shi kadai mu bar ababen da iyayenmu suka kasance suna bauta wa" Suratu Hud aya ta 70.
Da wannan sai ya bayyana cewa ma'anan la'ilaha illa llahu da abin da ta ke hukuntawa shi ne kadaita Allah da bauta da barin bautan wani abu koma bayansa, da kuma cewa ma'anan (kalmar) ilahu shi ne abin bauta. Saboda haka da zaran bawa ya ce la'ilaha illa llahu, to hakika ya shelanta wajibcin kadaita Allah ne da bauta da barin bautan wani koma bayan Sa, kamar gumaka da kaburbura da waliyyai da sauransu.
Kuma wannan shi ya ke kara tabbatar da kuskuren masu fassara kudurcewa, la'ilaha illa llahu shi ne tabbatar da samuwan Allah, ko kuma imani da cewa Shi ne mahalicci mai ikon kirkira da masu kama da haka. Da cewa ma'anar ta shi ne babu ma hukunci sai Allah kuma suna zaton cewa wanda ya kudurce hakan kuma ya fassara tauhidi da shi ya hakikance tauhidi, ko da kuwa ya aikata abinda ya aikata na bautan wanin Allah, wannan dai ruguzajjiyar fahimta ce a fili.
Wadannan ba su san cewa kafiran larabawa ma sun yi tarayya da su a cikin wannan akidar ba? Kuma suna cewa lallai Allah Shi ne mahalicci mai ikon kirkira. Allah تعالى Ya ce:
{ وَلَئِنْ سَأَلْتَهُمْ مَنْ خَلَقَ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضَ لَيَقُولُنَّ خَلَقَهُنَّ الْعَزِيزُ الْعَلِيمُ } [الزخرف: 9]
Ma'ana: "Kuma tabbas da za ka tambaye su wane ne ya halicci sammai da kasa? Da sannu za su ce mabuwayi masani ne Ya halicce su" Suratu Azzukhruf aya ta 9.
Kuma suna tabbatar da cewa suna bautar wanin Allah, amma suna riya cewa su ba su bauta wa waninSa ba sai don cewa za su kusantar da su zuwa ga Allah. Kamar yadda Allah Ya ce:
{ أَلَا لِلَّهِ الدِّينُ الْخَالِصُ وَالَّذِينَ اتَّخَذُوا مِنْ دُونِهِ أَوْلِيَاءَ مَا نَعْبُدُهُمْ إِلَّا لِيُقَرِّبُونَا إِلَى اللَّهِ زُلْفَى إِنَّ اللَّهَ يَحْكُمُ بَيْنَهُمْ فِي مَا هُمْ فِيهِ يَخْتَلِفُونَ إِنَّ اللَّهَ لَا يَهْدِي مَنْ هُوَ كَاذِبٌ كَفَّارٌ } [الزمر: 3]
Ma'ana: "Ku saurara! Addini tsrkakakke na Allah ne, wadanda suka riki waninSa a matsayin majibinta (suna cewa) mu ba mu bauta musu face don su kusantar da mu zuwa ga Allah kusantarwa, lallai Allah zai yi hukunci a tsakaninsu game da abin da su ka kasance suna sabani a cikinsa, lallai Allah ba Ya shiryar da makaryaci mai yawan kafirci" Suratu Azzumar aya ta 3.
Ka ga su ma ba su ce suna bautansu ba ne don suna iya halitta ko rayarwa ko matarwa, a a! a fadarsu suma sun yarda cewa duk wadannan abubuwa Allah nekadai ke yin su amma yardarsu da hakan bai sa sun zama musulmai ba, kuma bai hana Annabi ya yake su ba kamar yadda ya yaki sauran kafiran zamaninsa.
Da wannan ne zai kara fitowa fili cewa ma'ana ingantacciya ta kalmar shahada kamar yadda ambatonsa ya gabata a can baya shi ne kore cancantar bauta ga komai koma bayan Allah, da tabbatar da ita ga Allah Shi kadai ba tare da sanya masa abokin tarayya ba.
HAKIKANCE KALMAR SHAHADA
hakikance kalmar shahada shi ne, bawa ya tabbatar da cewa a tsawon rayuwarsa ya nisanci dukkan wata hanya da ta ke kai wa zuwa ga shirka babba ko karama, ya bauta wa Allah Shi kadai da zuciyarsa da harcensa da sauran gabbansa ya na mai tsarkake niyya cikin dukkan nau'ukan bauta, bautar da zai yi kuma tilas ne sai ta kasance shar'antacciya ba kirkirarriya ba.
Shekhul Islam ibnu Taimiyya ya na cewa game da wannan: "… a dunkule muna da asali guda biyu masu girma; daya daga cikin su shi ne: kada mu yi bauta sai ga Allah, na biyu kuma: kada mu bauta masa face da abin da Ya shar'anta, kada mu bauta masa da ibadoji kirkirarru na bidi'o'i. Wannan shi ne tahkikin ma'anar La'ilaha illa llahu Muhammadu rrasulu llahi. Duba majmu'ul fatawa ta Shekhul Islam 1\333. Da 1\618.
Kuma bawa ya na amfanuwa ne da fadin La'ilaha illa llahu idan ya hakikance rukunnanta da sharuddanta kamar yadda nan gaba za mu gani da - izinin Allah -, sa'annan kuma ya mutu a kan haka bai aikata wani abu da ke warware ta ba.
RUKUNNAN LA'ILAHA ILLA LLAHU
Rukunnan La'ilaha illa llahu su ne sassanta da ba ta tabbata ga bawa sai da tabbatar su, wadannan rukunnai guda biyu ne, su ne: korewa da tabbatarwa.
Abinda ake nufi da korwa shi ne, kore cancantar bauta ga wani koma bayan Allah Madaukakin sarki, wannan rukuni shi ne ke cikin La'ilaha.
Abin da ake nufi da tabbatarwa kuma shi ne tabbatar da bauta ta bisa cancanta ga Allah Shi kadai ba tare da sanya maSa abokin tarayya ba a cikin bautarSa kamar yadda ba Shi da abokin tarayya a cikin ayyukanSa na halitta da azurtawa da gudanar al'amuran halittu kuma kamar yadda ba Shi da abokin tarayya a cikin sunayenSa kyawawa da sifofinSa madaukaka. Wannan rukunin shi ne a cikin lafazin Illa llahu.
Saboda haka Shi Allah (سبحانه وتعالى) Shi ne kadai abin bauta bisa cancanta, duk wani abin da ake bauta wa koma bayansa na gumaka da duwatsu da mutane salihai da wadanda ma ba salihai ba da mala'iku da aljannu da sauransu duk bautar da ake musu batacciya ce kamar yadda Allah (تعالى)Ya ce:
{ذَلِكَ بِأَنَّ اللَّهَ هُوَ الْحَقُّ وَأَنَّ مَا يَدْعُونَ مِنْ دُونِهِ هُوَ الْبَاطِلُ وَأَنَّ اللَّهَ هُوَ الْعَلِيُّ الْكَبِيرُ (62)} [الحج: 62]
Ma'ana:"Wancan! Saboda lallai Allah Shi ne gaskiya kuma lallai abin da su ke kira koma bayansa shi ne karya kuma lallai Allah Shi ne madaukaki mai girma". Suratul Hajji aya ta 62.
SHARUDDAN LA'ILAHA ILLA LLAHU
Sharuddan la'ilaha illa llahu su ne wadanda da fadin la'ilaha illa llahu ba ya amfanar mutum har sai ya cika su, su ne kamar haka:
Sharadi na farko: Ilimi game da ma'anar kalmar shahada, wannan ya kunshi sanin hakikanin ma'anarta tare da tabbatar da cancantar bauta ga Allah Shi kadai da kore ta daga waninSa, sanin da ke kore jahilci game da hakikaninta. Wannan sanin abin da ke tabbatar da samuwarsa ga bawa shi ne aga ya nisanci shirka baki dayanta karamarta da babbarta ya kuma tsarkake ibadarsa ta zuci da harce da ta gabbai ga Allah Shi kadai.
Dalilai daga Alkur'ani da hadisan Annabi ingantattu sun tabbata game da wannan sharadin daga cikinsu akwai fadin Allah (تعالى):
{فاعلم أنه لا إله إلا الله ... }[محمد 19]
Ma'ana: "Saboda haka ka sani cewa babu abin bautawa bisa cancanta face Allah… Suratu Muhammad aya ta 19.
Da fadinSa Madaukakin Sarki:
{ وَلَا يَمْلِكُ الَّذِينَ يَدْعُونَ مِنْ دُونِهِ الشَّفَاعَةَ إِلَّا مَنْ شَهِدَ بِالْحَقِّ وَهُمْ يَعْلَمُونَ (86)} [الزخرف: 86]
Ma'ana: Kuma wadanda suke bauta wa koma bayanSa ba su mallakar ceton, sai dai wanda ya shaida da gaskiya (watau (لا إله إلا الله alhali suna sani". Suratu Azzukhruf aya ta 86.
Saboda ma'anar shaidawa da gaskiya shi ne fadin la'ilaha illa llahu, kamar yadda ya zo cikin tafsirin dImamu Ddabari juzu'i na 21 shafi na 604. ma'anan ayar ta kasance ke nan: sai dai wanda ya shaida cewa babu abin bauta bisa cancanta sai Allah alhali ya na sane da ma'anar abin da ya ke furuci da shi.
Dalili na uku daga Alkur'ani shi ne fadin Allah تعالى)):
{هَذَا بَلَاغٌ لِلنَّاسِ وَلِيُنْذَرُوا بِهِ وَلِيَعْلَمُوا أَنَّمَا هُوَ إِلَهٌ وَاحِدٌ وَلِيَذَّكَّرَ أُولُو الْأَلْبَابِ (52) } [إبراهيم: 52]
Ma'ana:"Wannan iyarwa ce ga mutane kuma domin a gargade su da shi kuma su sani cewa abin sani kawai abin bauta bisa cancanta guda daya ne, kuma domin masu hankali su rika wa'aztuwa. Suratu Ibrahim aya ta 52.
Dalili daga hadisin Annabi (صلى الله عليه وسلم) kuma shi ne fadin sa:
"من مات وهو يعلم أن لا إله إلا الله دخل الجنة"
Ma'ana: "Wanda ya mutu alhali ya na sanin cewa babu abin bautawa bisa cancanta sai Allah zai shiga Aljanna. Imamu Ahmad ya ruwaito shi a cikin Almusnad a hadisi mai lamba 464, da 499, Shu'aibul Arna'ut ya inganta isnadinsa.
Sharadi na biyu: Yakini, aharshenlarabci yakini na nufin gushewar shakku da samun tabbbacin al'amari, shi ne kishiyan shakka kamar yadda ilimi ya ke kishiyan jahilci.
Abin nufi da yakini a wannan wuri shi ne: ya kasance mutum ya furta kalmar shahada alhali zuciyarsa na cike da yakini game da abin da la'ilaha illa llahu ta ke nuni zuwa gare shi yakinin da ke gusar da shakku tun daga tushensa. Saboda haka duk wanda ya fade ta alhali akwai wani abu na shakku tare da shi a game da ma'anarta, to bai samu tabbatuwar wannan sharadin ba.
Dalilai masu yawa sun zo daga Alkur'ani da hadisan Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ingantattu.
Daga cikin dalilan da suka zo daga Alqur'ani akwai fadin Allah (تعالى)
{إِنَّمَا الْمُؤْمِنُونَ الَّذِينَ آمَنُوا بِاللَّهِ وَرَسُولِهِ ثُمَّ لَمْ يَرْتَابُوا وَجَاهَدُوا بِأَمْوَالِهِمْ وَأَنْفُسِهِمْ فِي سَبِيلِ اللَّهِ أُولَئِكَ هُمُ الصَّادِقُونَ } [الحجرات: 15]
Ma'ana: "Abin sani kawai, muminai su ne wadanda su ka yi imani da Allah da ManzonSa sa'annan kuma ba su yi tantama ba kuma suka yi jihadi da dukiyoyinsu da jikkunansu saboda Allah, wadannan su ne masu gaskiya". Suratul Hujurat aya ta 15.
Daga sunna kuma Imamu Muslim ya ruwaito hadisi daga Abu Huraira (رضي الله عنه) ya na cewa: Manzon Allah صلى الله عليه وسلم) ) ya ce:
«أشهد أن لا إله إلا الله، وأني رسول الله، لا يلقى الله بهما عبد غير شاك فيهما، إلا دخل الجنة»
Ma'ana:"Ash'hadu alla ilaha illlallahu wa anni rasulullahi bawa ba zai sadu da Allah da su ba ya na mara shakka game da su face ya shiga Aljanna". Sahihu Muslim kitabul iman hadisi na 44.
Da fadin Annabi (صلى الله عليه مسلم) ga Abu Hurairah
" اذهب بنعلي هاتين فمن لقيت وراء هذا الحائط يشهد أن لا إله إلا الله مستيقنا بها قلبه فبشره بالجنة ".
Ma'ana:"Ka tafi da takalman nan nawa, duk wanda ka hadu da shi daga bayan wannan shingen ya na shaidawa babu abin bautawa bisa cancanta sai Allah, ya na mai yakini game da hakan har cikin zuciyarsa, to ka yi masa albishir da gidan aljanna". Sahihu Muslim kitabul iman hadisi na 52.
Da hadisin Mu'azu dan jabal (رضي الله عنه) Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya na cewa:
"ما من نفس تموت وهي تشهد أن لا إله إلا الله وأني رسول الله يرجع ذلك إلى قلب موقن إلا غفر الله لها".
Ma'ana:"Babu wata rai da za ta mutu alhali ta na shaida cewa babu abin bauta bisa cancanta sai Allah kuma ni manzon Allah ne wannan shaidawar na komawa ga zuciya mai yakini face Allah Ya gafarta mata". Sunanu Ibni Majah hadisi na 3796.
Wadannan dalilai ken an daga Alkur'ani da hadisan Annabi (صلى الله عليه وسلم) da su ke nuni zuwa ga cewa yakini sharadi ne a cikin shahadar bawa, Allah shi ne mafi sani.
Sharadi na uku:Ikhlasi, hakikanin ma'anar ikhlasi shi ne bawa ya nufi Allah da aikinsa ya kuma barranta daga yin wani aiki na ibada don neman yardar wani mahaluki. Kishiyar ikhlasi ita ce shirka, saboda haka duk wanda bai yi ikhlasi ba a cikin aikinsa na ibada, watau ya yi aikin nasa saboda riya da sum'a da Duniya da makamantan haka to shahadarsa bata cika ba saboda ya rasa sharadi guda daya mai girma wacce ita ce ikhlasi.
Ga wasu daga cikin dalilai da suke tabbatar da wannan sharadin.
Daga Alkur'ani mai girma fadin Allah (سبحانه وتعالى)
{إنا أنزلنا إليك الكتاب بالحق فاعبد الله مخلصا له الدين , ألا لله الدين الخالص …} الآية.
Ma'ana:"Lallai ne Mu Mun saukar maka da littafi da gaskiya, saboda haka ka bauta wa Allah ka na mai tsarkake addini gare shi. Ku saurara! Lallai tsarkakakken addini na Allah ne" Suratu Azzumar aya ta 3.
Da fadin Allah (سبحانه وتعالى):
{قُلِ اللَّهَ أَعْبُدُ مُخْلِصًا لَهُ دِينِي} [الزمر: 14]
Ma'ana:"Ka ce, Allah kadai zan bauta wa, ina mai tsarkake addinina gare shi". Suratu Azzumar aya ta 14.
Da fadin Allah (سبحانه وتعالى):
{وما أمروا إلا ليعبدوا الله مخلصين له الدين حنفاء ... } الآية.
Ma'ana:"Kuma ba'a umurce su ba face da su bauta wa Allah suna ma su tsarkake addini gare Shi ma su karkata zuwa ga tafarkin gaskiya". Suratul Bayyinah aya ta 5.
Daga Abu Hurairata (رضي الله عنه) ya ce na ji Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya na cewa: Allah (تعالى) Ya ce:
" أنا أغنى الشركاء عن الشرك من عمل عملا أشرك فيه معي غيري تركته وشركه "
Ma'ana:"Ni ne mafi wadatuwa daga barin abokin tarayya…." Sahihu muslim hadisi na 7475.
Daga Abu Hurairata (رضي الله عنه) ya ce ; an ce ya ma'aikin Allah wane ne ya fi cancantan ya rabauta da samun cetonka ranar alkiyama? Sai ya ce:
" أسعد الناس بشفاعتي يوم القيامة من قال لا إله إلا الله خالصا من قلبه ". وفي رواية"خالصة من قلبه ".
Ma'ana:"wanda ya fi cancantar ya rabauta da samun cetona ranar alkiyama shi ne wanda ya ce la'ilaha illa llahu ya na mai tsarkake niyyarsa har cikin zuciya (watau ya na mai ikhlasi)" Sahihul Bukhari hadisi na 99.
Daga Itban bin Malik (رضي الله عنه) ya ce Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya ce:
" إن الله حرم على النار من قال لا إله إلا الله يبتغي بذلك وجه الله عز وجل " متفق عليه.
Ma'ana:"Lallai Allah Ya haramta wanda ya ce la'ilaha illa llahu ya na mai nema yardan Allah (عز وجل) da fadin hakan ga wuta" Bukhari da Muslim.
Daga Mu'azu dan Jabal (رضي الله عنه) ya ce lallai Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya ce:
" من شهد أن لا إله إلا الله مخلصا من قلبه دخل الجنة".
Ma'ana:" wanda ya shaida cewa babu abin bautawa bisa cancanta sai Allah ya na mai ikhlasi har cikin zuciyarsa zai shiga Aljanna". Sahihu bni Hibban 200.
Abin nufi da ikhlasi a nan shi ne, tsarkake niyya cikin kudurin da bawa ya yi game da ma'anar la'ilaha illa llahu kuma tasirin hakan ya bayyana a cikin dukkanin ayyukan bauta na zuci da na gabbai.
Ibnu Taimiyya – Allah Ya yi masa rahama - ya na cewa: "shi ko ikhlasi, shi ne hakikanin misulunci, saboda musulunci shi ne sallamawa da mika wuya ga Allah ba ga waninSa ba. Kamar yadda Allah (تعالى) Ya ke cewa:
{ضرب الله مثلا رجلا فيه شركاء متشاكسون ورجلا سلما لرجل هل يستويان ... }
Ma'ana:"Allah Ya buga misali da wani mutum bawa wanda mutane da yawa suka yi tarayya cikin mallakarsa, da wani bawan shi kuma mallakar mutum daya ne, shin za su zama daya a wurin misali?...." Suratu Azzumar aya ta 29.
Saboda haka duk wanda bai sallama ya mika wuya ga Allah ba to shi mai girman kai ne, wanda kuma ya mika wuya ga Allah tare da waninsa shi kuma ya yi shirka, ko wane daya daga cikin biyun: girman kai da shirka ya na kishiyantar musulunci ne, watau musulunci sabanin shirka ce da girman kai" Majmu'ul fatawa 10/14.
Daga haka za mu kara fahimtar cewa wanda ya furta kalmar shahada ko da ya san ma'anarta kuma bisa yakini ba za ta amfane shi ba har sai ya kasance mai ikhlasi cikin bautarsa ga Allah Shi kadai. Ma su ikhlasi kuma su ne wadanda dukkanin ayyukansu na ibada su ka kasance saboda Allah Shi kadai sawa'un ayyukan zuci ne ko na furuci ko aikin gabbai, ba su nifin samun wani sakamako ko yabo game da aikinsu na ibada a wurin mutane ko neman gindin zama ko matsayi a zukatansu ko gudun zargi daga wurinsu.
Saboda haka wanda ya kirayi wanin Allah ya rusa la'ilaha illa llahunsa domin ya rasa sharadin ikhlasi, ko da kuwa wanda ya kira din mai matsayi ne a wurin Allah kamar mala'ika ko annabi ko waliyyi salihi ko waninsu koma bayan Allah (سبحانه وتعالى).
Sharadi na hudu: Gaskiya mai kore karya. Abin nufi da wannan sharadin shi ne, mutum ya furta la'ilaha illa llahu ya na mai gaskiya har cikin zuciyarsa game da abin da ya furta na kalmar shahada da abin da ta kunsa.
Dalilai akan wannan sharadin suna da matukar yawa daga cikin su akwai fadin Allah (سبحانه وتعالى)
{الم (1) أَحَسِبَ النَّاسُ أَنْ يُتْرَكُوا أَنْ يَقُولُوا آمَنَّا وَهُمْ لَا يُفْتَنُونَ (2) وَلَقَدْ فَتَنَّا الَّذِينَ مِنْ قَبْلِهِمْ فَلَيَعْلَمَنَّ اللَّهُ الَّذِينَ صَدَقُوا وَلَيَعْلَمَنَّ الْكَاذِبِينَ (3) } [العنكبوت: 1 - 4]
Ma'ana:"Shin mutane suna zaton ne kawai za a kyale su su ce mun yi imani ba tare da an fitine su ba? (2) Hakika Mun jarrabi wadanda suka gabace su, kuma lallai tabbas Allah Ya san wadanda su ka yi gaskiya kuma lallai Ya san makaryata (3)" Suratul Ankabuti aya ta 2 da ta 3.
Hakan ma Allah Ya ce:
{ وَمِنَ النَّاسِ مَنْ يَقُولُ آمَنَّا بِاللَّهِ وَبِالْيَوْمِ الْآخِرِ وَمَا هُمْ بِمُؤْمِنِينَ (8) يُخَادِعُونَ اللَّهَ وَالَّذِينَ آمَنُوا وَمَا يَخْدَعُونَ إِلَّا أَنْفُسَهُمْ وَمَا يَشْعُرُونَ (9) فِي قُلُوبِهِمْ مَرَضٌ فَزَادَهُمُ اللَّهُ مَرَضًا وَلَهُمْ عَذَابٌ أَلِيمٌ بِمَا كَانُوا يَكْذِبُونَ (10)} [البقرة: 8 - 10]
Ma'ana:" Kuma akwai daga cikin mutane wanda ya ke cewa: mun yi imani da Allah da ranar lahira alhali kuwa su ba muminai bane (8) suna yin yaudara ga Allah da wadanda suka yi imani, alhali ba su sakankancewa (9). Suratul Bakara aya ta 8 da ta 9.
Da fadin Allah (تعالى)
{قَالَ اللَّهُ هَذَا يَوْمُ يَنْفَعُ الصَّادِقِينَ صِدْقُهُمْ لَهُمْ جَنَّاتٌ تَجْرِي مِنْ تَحْتِهَا الْأَنْهَارُ خَالِدِينَ فِيهَا أَبَدًا رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُمْ وَرَضُوا عَنْهُ ذَلِكَ الْفَوْزُ الْعَظِيمُ (119)} [المائدة: 119]
Ma'ana:"Allah Ya ce: wannan shi ne yinin da gaskiya za ta yi amfani ga ma abutanta, suna da aljannoni wadanda koramu ke gudana a karkashinsu, suna masu dawwama a cikinta har abada, Allah ya yarda da su kuma suma sun yarda da shi, wancan shi ne rabo mai girma" Surtul Ma'ida aya ta119.
Haka nan ma fadin Allah (تعالى)
{وَالَّذِي جَاءَ بِالصِّدْقِ وَصَدَّقَ بِهِ أُولَئِكَ هُمُ الْمُتَّقُونَ (33)} [الزمر: 33]
Ma'ana:"Wanda ya zo da gaskiya kuma ya gaskata game da ita, to wadannan sune masu takawa" Suratu Azzumar aya ta 33.
An ruwaito daga Abullahi dan Abbas ya na cewa game da ma'anan ayar:" wanda ya zo da la'ilaha illa llahu" duba zadul masir na ibnul Jauzi 4/18 da ibn Kathir 7/99.
Wadannan kadan ken an daga dalilai na Alkur'ani mai girma.
Daga hadisan Annabi (صلى الله عليه وسلم) ingantattu kuwa akwai fadin Annabi (صلى الله عليه وسلم) ga Abu Musa Al'ash'ari alhali ya na tare da wasu daga cikin jama'arsa:
"ابشروا وبشروا من ورائكم: أنه من شهد أن لا إله إلا الله صادقا بها دخل الجنة".
Ma'ana:"Albishirinku kuma ku yi albishir ga wadanda ku ka baro a bayanku cewa duk wanda ya shaida cewa babu abin bauta bisa cancanta sai Allah alhali ya na mai gaskiya game da ita (shahadar) zai shiga Aljannan" Musnad na Imamu Ahmad 19597. Albani ya inganta shi A cikin silsila sahiha 1314.
Da fadin Annabi (صلى الله عليه وسلم) ga Mu'azu dan Jabal (رضي الله عنه)
" ... ما من أحد يشهد أن لا إله إلا الله وأن محمدا رسول الله صدقا من قلبه إلا حرمه الله على النار ... ".
Ma'ana:"Babu wani da zai shaida cewa babu abin bauta bisa cancanta sai Allah kuma lallai Muhammadu ManzonSa ne ya na mai gaskatawa daga zuciyarshi face Allah Ya haramta shi ga wuta" Sahihul Bukhari 128.
Wadannan kadan ke nan daga cikin dalilai na Alkur'ani da hadisi game da kasancewar gaskiya cikin fadin la'ilaha illa llahu sharadi ne, saboda haka duk wanda ya fade ta da fatar baki kawai bata dace da abin da ke zuciyarsa ba – kamar yadda munafukai suke furta ta bisa karya da yaudara – to furucinsu karya ne ba zai amfane su ba a gaban Allah kamar yadda Allah (سبحانه وتعالى) Ya ce:
{إِذَا جَاءَكَ الْمُنَافِقُونَ قَالُوا نَشْهَدُ إِنَّكَ لَرَسُولُ اللَّهِ وَاللَّهُ يَعْلَمُ إِنَّكَ لَرَسُولُهُ وَاللَّهُ يَشْهَدُ إِنَّ الْمُنَافِقِينَ لَكَاذِبُونَ} [المنافقون: 1]
Ma'ana:" Idan munafukai suka taho wurin ka sai su dora cewa: mun shaida lallai kai manzon Allah ne, Allah Ya san cewa kai manzonSa ne, kuma Allah Ya shaida cewa lallai munafukai karya su ke yi" Suratul Munafikuna aya ta 1.
Sharadina biyar: soyayya: Ma'anar wannan sharadin shi ne kaunar la'ilaha illa llahu, da dukkanin abin ta ke nuni zuwa gare shi na maganganu da ayyuka kaunar da ke kore kiyayya.
Daga cikin haka shi ne Allah da ManzonSa su ka kasance mafiya soyuwa a gare ka sama da wanda ba su ba. Da kaunatar ma'abuta la'ilaha illa llahu wadanda su ke aiki da ita masu lazimtar sharuddanta. Da kuma kin wanda ya saba mata.
Saboda wanda ya furta ta ba zai kai ga saninta da samun karbuwarta a zuciyarsa ba face da kaunarta. Saboda kauna dalili ne na ikhlasi wanda ke kore shirka, duk wanda ya kaunaci Allah (تعالى) to zai kaunaci addininSa.
Allah ((تعالى Ya ce
{ومن الناس من يتخذ من دون الله أندادا يحبونهم كحب الله والذين آمنوا أشد حبا لله ... } الآية. (البقرة 165)
Ma'ana:"Kuma akwai daga cikin mutane wanda ke rikon kinaye baicin Allah suna son su kamar son Allah. Wadanda suka yi imani ne ma fiya tsananin so ga Allah…. Sursatul Bakara aya ta 165.
Kuma Allah ((تعالى Ya ce:
{ يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا مَنْ يَرْتَدَّ مِنْكُمْ عَنْ دِينِهِ فَسَوْفَ يَأْتِي اللَّهُ بِقَوْمٍ يُحِبُّهُمْ وَيُحِبُّونَهُ أَذِلَّةٍ عَلَى الْمُؤْمِنِينَ أَعِزَّةٍ عَلَى الْكَافِرِينَ يُجَاهِدُونَ فِي سَبِيلِ اللَّهِ وَلَا يَخَافُونَ لَوْمَةَ لَائِمٍ} [المائدة: 54]
Ma'ana:" Ya ku wadanda suka yi imani, wanda ya yi ridda ya bar addininsa daga cikinku, to da sannu Allah zai zo da wasu mutane Ya na son su, kuma suma suna sonSa masu tawalu'u ne ga muminai masu izza akan kafirai… Suratul Ma'ida aya ta 54.
Kuma Allah ((تعالى Ya ce:
{قُلْ إِنْ كُنْتُمْ تُحِبُّونَ اللَّهَ فَاتَّبِعُونِي يُحْبِبْكُمُ اللَّهُ وَيَغْفِرْ لَكُمْ ذُنُوبَكُمْ وَاللَّهُ غَفُورٌ رَحِيمٌ} [آل عمران: 31]
Ma'ana:"Ka ce in har kun kasance kuna son Allah to ku bi ni, Allah zai so ku, kuma Ya gafarta mu ku zunubbabanku, kuma Allah mai gafara ne mai jin kai" Suratu Ali Imran aya ta 31.
Kuma Allah Ya ce:
{قُلْ إِنْ كَانَ آبَاؤُكُمْ وَأَبْنَاؤُكُمْ وَإِخْوَانُكُمْ وَأَزْوَاجُكُمْ وَعَشِيرَتُكُمْ وَأَمْوَالٌ اقْتَرَفْتُمُوهَا وَتِجَارَةٌ تَخْشَوْنَ كَسَادَهَا وَمَسَاكِنُ تَرْضَوْنَهَا أَحَبَّ إِلَيْكُمْ مِنَ اللَّهِ وَرَسُولِهِ وَجِهَادٍ فِي سَبِيلِهِ فَتَرَبَّصُوا حَتَّى يَأْتِيَ اللَّهُ بِأَمْرِهِ وَاللَّهُ لَا يَهْدِي الْقَوْمَ الْفَاسِقِينَ (24)} [التوبة: 24]
Ma'ana:" Ka ce idan Ubanninku da 'ya'yanku da 'yan'uwanku da matanku da danginku da dukiyoyinku da kuka tara da fatauci wanda ku ke tsoron tasgaronsa da gidaje wadanda ku ke yarda da su, sun kasance mafiya soyuwa a gare ku daga Allah da ManzonSa da jihadi don daukaka kalmarSa, to ku yi zaman jira har Allah Ya zo da umurninSa, kuma Allah baYa shiryar da mutane fasikai" Suratu Attauba aya ta 24.
Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya ce:
"ثلاث من كن فيه وجد بهن حلاوة الإيمان: من كان الله ورسوله أحب إليه مما سواهما، ومن أحب عبدا لا يحبه إلا لله، ومن يكره أن يعود في الكفر بعد إذ أنقذه الله منه كما يكره أن يلقى في النار". متفق عليه
Ma'ana:"Abubuwa uku duk wanda suka kasance tare da shi, ya samu gardin imani dasu: wanda Allah da ManzonSa suka fi soyuwa a gare shi sama da waninsu, da wanda ya kaunaci bawa ba don komai ba sai domin Allah, da wanda ya ke kyamar komawa ga kafirci bayan Allah Ya tseratar da shi daga gare shi, kamar yadda ya ke kin a jefa shi a cikin wuta" Bukhari da Muslim ne suka ruwaito shi.
Daga Abu Razin Al'ukaili (رضي الله عنه) ya ce: ya ma'aikin Allah, me ne ne imani? Sai ya ce:
"أن تشهد أن لا إله إلا الله وحده لا شريك له وأن محمدا عبده ورسوله وأن يكون الله ورسوله أحب إليك مما سواهما ... " الحديث".
Ma'ana:"Ka shaida cewa ba bu abin bautawa bisa cancanta sai Allah Shi kadai ba shi da abokin tarayya, kuma lallai Muhammadu ManzonSa ne, kuma Allah da ManzonSa su kasance mafiya soyuwa a gare ka sama da waninsu" Imamu Ahmad ne ya ruwaito shi (16194).
Da fadin sa ((صلى الله عليه وسلم:
"لا يؤمن أحدكم حتى أكون أحب إليه من والده وولده والناس أجمعين " متفق عليه.
Ma'ana:"Dayanku ba zai yi imani ba har sai na kasance mafi soyuwa a gare shi bisa ga ma haifinsa da dansa da mutane baki daya" Bukhari da Muslim ne suka ruwaito shi.
Sharadi na shida: Jawuwa
Abin nufi da wannan sharadin shi ne: Makauniyar biyayya cikakkiya ga la'ilaha illa llahu da duk abin da ta ke hukuntawa na zahiri da na badini biyayyar da ta ke kore bari.Wannan kuwa hakikanin sa shi ne sallamawar bawa ga Allah da zuciyarsa da gabbansa bisa kadaitaShi cikin dukkan nau'ukan ibada ta hanyar aikata umurni da barin abin hani. Allah (تعالى) Ya ce:
{وَأَنِيبُوا إِلَى رَبِّكُمْ وَأَسْلِمُوا لَهُ مِنْ قَبْلِ أَنْ يَأْتِيَكُمُ الْعَذَابُ ثُمَّ لَا تُنْصَرُونَ } [الزمر: 54]
Ma'ana:"Ku mai al'amura zuwa ga Ubangijinku kuma ku mika wuya gare Shi gabanin azaba ta zo muku sannan ba za a taimake ku ba" Suratu Azzumar aya ta 54.
Kuma Allah Ya ce:
{وَمَنْ أَحْسَنُ دِينًا مِمَّنْ أَسْلَمَ وَجْهَهُ لِلَّهِ وَهُوَ مُحْسِنٌ} [النساء: 125]
Ma'ana:"Kuma waye ya fi kyawun addini sama da wanda ya sallama fuskarsa ga Allah alhali ya na mai kyutatawa…." Suratu Annisa'i aya ta 125.
Idan muka lura za mu ga cewa duk wadannan ayoyin suna nuni ne zuwa ga wajibcin mika wuya ga Allah Madaukakin Sarki, saboda haka bawa ba zai amfana da furucinsa ga la'ilaha illa llahu ba har sai an samu wannan mika wuyar da sallamawar. Allah (تعالى) Ya ce:
{وَمَنْ يُسْلِمْ وَجْهَهُ إِلَى اللَّهِ وَهُوَ مُحْسِنٌ فَقَدِ اسْتَمْسَكَ بِالْعُرْوَةِ الْوُثْقَى وَإِلَى اللَّهِ عَاقِبَةُ الْأُمُورِ} [لقمان: 22]
Ma'ana:" Wanda ya mika wuya ga Allah alhali ya na mai kyautatawa, hakika ya yi riko da amintacciyar iggiya, kuma karshen al'amura ga Allah su ke" Suratu Lukuman aya ta 22. Wannar amintacciyar iggiya ita ce la'ilaha illa llahu kamar yadda Abdullahi dan Abbas (رضي الله عنهما)ya fassara ta da shi hakama Ibnu Jubair da Dahhak. Duba tafsirin Ibnu Abbas (4/219) da tafisirin Ibnu Kathir (1/684).
Wannan kadan ke nan daga cikin ayoyin Alkur'ani, daga hadisan Annabi ((صلى الله عليه وسلم harwa yau dai akwai hadisin da Imamul Bukhari da Muslim suka ruwaito daga Abdullahi dan Mas'ud (رضي الله عنه) Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya ce:
"لا يحل دم امرئ مسلم يشهد أن لا إله إلا الله وأني رسول الله إلا بإحدى ثلاث: الثيب الزاني والنفس بالنفس، والتارك لدينه المفارق للجماعة".
Ma'ana:"Jinin mutum musulmi wanda ya ke shaida cewa babu abin bautawa bisa cancanta sai Allah kuma ni manzon Allah ne ba ya halitta sai da dayan abubuwa uku; mazinaci katangagge, da rai da ta kashe rai da wanda ya bar addininsa ya ware daga jama'ar musulmi".
Wannan hadisin ya na kara fito da wannan sharadin fili kuma ya na kara tabbatar da cewa ko da bawa ya ce ya shaida babu abin bautawa bisa cancanta sai Allah kuma Annabi Muhammadu ((صلى الله عليه وسلم manzonSa ne ba zai kubutar da jininsa ba har sai ya bi abin da ta ke hukuntawa na lazimtar addini da nisantar abinda ya ke fitar da mutum daga cikinsa, domin barin addini shi ne rashin mika wuya kuma ya na halatta jinnin bawa bayan ya haramta.
Sharadi na bakwai: karba.
Ma'anar wannan sharadin shi ne, bawa ya karbi la'ilaha illa llahu da duk abin da ta ke hukuntawa ba tare da mayar da wani abu ba sakamakon girman kai ko hassada da sauransu, duk wanda ya mai da ita ko abin da take hukuntawa to bai hakiance wannan sharadin ba. Allah (تعال) Ya ce game da kafiran kuraishawa:
{إِنَّهُمْ كَانُوا إِذَا قِيلَ لَهُمْ لَا إِلَهَ إِلَّا اللَّهُ يَسْتَكْبِرُونَ (35) وَيَقُولُونَ أَئِنَّا لَتَارِكُو آلِهَتِنَا لِشَاعِرٍ مَجْنُونٍ (36) بَلْ جَاءَ بِالْحَقِّ وَصَدَّقَ الْمُرْسَلِينَ (37)} [الصافات: 35 - 37]
Ma'ana:"Su sun kasance idan aka ce da su babu abin bautawa bisa cancanta sai Allah, sai su dora yin girman kai (35) kuma su rika cewa; yanzu mu masu barin ababen bauutanmu ne saboda wani mawaki mahaukaci?(36) A'a! ba haka lamarin ya ke ba, ya zo ne da gaskiya, kuma ya gaskata manzanni" Suratu Assafat aya ta 35 zuwa ta 37.
A cikin wannan ayar akwai alkawari na narkon azaba mai radadi a lahira ga wanda duk bai karbi la'ilaha illa llahu ba da abin da ta kunsa na imani da manzancin Annabi ((صلى الله عليه وسلم.
Allah (تعالى) Ya ce:
{وَعَجِبُوا أَنْ جَاءَهُمْ مُنْذِرٌ مِنْهُمْ وَقَالَ الْكَافِرُونَ هَذَا سَاحِرٌ كَذَّابٌ (4) أَجَعَلَ الْآلِهَةَ إِلَهًا وَاحِدًا إِنَّ هَذَا لَشَيْءٌ عُجَابٌ (5)} [ص: 4، 5]
Ma'ana:"Kuma sun yi mamaki don wani mai gargadi ya zo musu daga cikinsu, sai kafirai su ka ce; wannan masihirci ne mai yawan karya(4) Ynazu ya mayar da ababen bauta duk su zama abin bauta guda daya? Lallai wannan abu ne da ya kai makura wurin ban mamaki" Suratu Sad aya ta 4 da ta 5.
A wannan ayar Allah Ya nuna mana yadda kafirai suka ki karban la'ilaha illa llahu saboda ba su yarda da abin da ta ke lazimtawa ba na tsarkake bauta ga Allah Shi kadai, sai Allah Ya kira su kafirai saboda hakan, ibnul Jauzi ya nakalto daga katada ya na cewa - game da wannan ayar- : yayin da Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya kira kuraishawa zuwa ga kadai ta Allah cikin bauta da neman biyan bukatu daga gare Shi Shi kadai, sai suka ce; yanzu abin bauta guda daya shi ne zai iya sauraron dukkanin bukatunmu??? Duba zadul masir na ibnul Jauzi (3/560).
Saboda haka da suka kangare su ka ki karaban la'ilaha illa llahu sai suka tabbata kafirai.
Anan wannan takaitaccen bayani game da sharuddan la'ilaha illa llahu ya kare, muna rokon Allah Ya ba mu ladan abin da muka dace da daidai a ciki Ya kuma gafarta mana abin da ya wakana na kurakurai. Allah Shi ne ma fi sani.
Dahiru Jibril Dukku Aljami'atul Islamiyya Madina
Daren Alhamis 25-2-1436 AH. Wanda ya dace da 17- 12 - 2014.