المساعد الشخصي الرقمي

مشاهدة النسخة كاملة : Manufofin sharia 20


طاهر جبريل دكو
_11 _December _2014هـ الموافق 11-12-2014م, 01:42 AM
MANUFOFIN SHARIA 20


HIKIMOMIN SHAR'ANTA SAKI
Addinin musulunci ya yi umarni da dukkan abubuwan da za su karfafa aure, saidai wani lokacin ma'aurata suna haduwa da wasu mushkiloli wadanda za su sanya rabuwarsu ta zama ita ce ta fi alkairi, Allah yana cewa a cikin haka :"Idan ma'aurata biyu, suka rabu, sai Allah ya wadata kowa daga yalwarsa" Suratu Annis'ai aya ta : 130
Akwai hikomomi da dama, da suka sa Allah ya shar'anta saki, ga wasu daga ciki :
1. Zai iya yiwuwa daya daga cikin ma'aurata ya ga ba zai iya jure dabi'un abokin zamansa ba, ya kuma shiga damuwa saboda haka, sai ya kasance babu wata hanya da za'a iya warware mushkilar sai ta hanyar rabuwa.
2. Idan har ba'a shar'anta saki ba, to daya cikin ma'aurata idan ya gaji da dan'uwansa zai iya neman hanyar da zai huta daga shi, ta hanyar kashe shi, ko kuma illanta shi, kamar yadda hakan ya faru ga wasu daga cikin ma'aurata, ga wasu misalai dana gani da idona wasu kuma na ji labarinsu :
A. Akwai matar dana sani, wacce saboda kiyayyar da take yiwa mijinta ta saka masa garin batiri a cikin abincinsa, saboda kawai tana so ya mutu ta huta da shi.
B. Akwai wanda na sani, saboda da kin da matarsa take masa, ta dauki reza za ta yanki al'aurarsa lokacin da suka zo saduwa.
C. Akwai wacce ta kashe mijinta, saboda ba ta son shi.
DUKA WADANNAN MUSHKILOLIN ZA'A IYA WARWARE SU TA HANYAR SAKI.
3. Idan mace mijinta ba ya birgeta za ta iya rikar kwarto ya rinka biya mata bukatarta, kamar yadda shima namiji zai iya yin hakan, hakan kuma zai haifar da barna a cikin al'umma.
4. Zai yi wahala namiji ya yi adalci ga matar da ba ya sonta, ka ga saki zai zama hanya mafi sauki wajan warware matsalar.
WADANNAN ABUBUWAN DA SUKA GABATA ZA SU NUNA MANA GIRMAN SHARI'AR MUSULUNCI DA KUMA MANUFOFINTA A CIKIN HUKUNCE-HUKUNCENTA, DA FATAN ZA'A KASANCE TARE DA MU A DARUSA NA GABA.

طاهر جبريل دكو
_11 _December _2014هـ الموافق 11-12-2014م, 01:56 AM
MANUFOFIN SHARIA 21


YIN KYAUTA GA MATAR DA AKA SAKA, DA HIKIMAR HAKAN
Addinin musulunci addini ne ta ya yi umarni da kyautatawa, har ga wanda aka samu sabani da shi, Allah yana cewa : "Mummuna da kyakkyawa ba sa taba zama daidai, ka tunkude mummuna da abu ma fi kyau, sai ka ga wanda yake akwai gaba a tsakaninku da shi, ya zama cikakken masoyinka" suratu Fussilat aya ta : 34
Yawanci idan aka yi saki ma'aurata su kan rabu cikin fushi da bacin rai, to amma duk da haka, Allah ya yi umarni da yin kyauta ga matar da aka saka, gwargwadon wadatar miji, ga wasu daga cikin hikimomin da suka sa shari'a ta yi umarni da hakan :
1. Tausasa zuciyar wacce aka saka, saboda za ta zama tana cikin bakin ciki, duk lokacin da miji ya kyautata mata, sai ta zama ta tafi cikin annashuwa tana mai godiya gare shi.
2. Dukiyar da miji zai ba ta lokacin da zai rabu da ita, za ta taimaka ,mata wajen biyan bukatunta, na wannan lokacin, ko wasu matsaloli da za su iya taso mata.
3. Hakan yana daga cikin alamomin rabuwa cikin mutunci.
4. Yin kyauta ga wacce aka saka yana magance rigingimun da suka faru lokacin saki.
5. Zai iya yiwuwa, akwai wasu hakkokinta akansa wadanda bai san su ba, duk lokacin da ya yi hakan sai ya zama ya fita daga kokwanto.
6. Yin kyauta ga wacce aka saki, yana saukake kome, saboda danginta za su rinka kallon miji a matsayin mutumin kirki.

A KASANCE TARE DA MU A DARUSA NA GABA
-