تسجيل الدخول

مشاهدة النسخة كاملة : Ayoyi uku da su ke rusa addinin shi'a ku sa 'ya'yanku su haddace su


طاهر جبريل دكو
_11 _December _2014هـ الموافق 11-12-2014م, 01:31 AM
ثلاث آيات قرآنية تهدم دين الشيعة حفظو ها لأولادكم
AYOYI UKU DA SU KE RUSA ADDININ SHI'A KU SA 'YA'YANKU SU HADDACE SU
1- 'Yan shi'a suna cewa: Lallai kiran waliyyai ba shirka ba ne.
Allah ya ce:
ذَلِكُمُ اللَّهُ رَبُّكُمْ لَهُ الْمُلْكُ وَالَّذِينَ تَدْعُونَ مِنْ دُونِهِ مَا يَمْلِكُونَ مِنْ قِطْمِيرٍ (13) إِنْ تَدْعُوهُمْ لَا يَسْمَعُوا دُعَاءَكُمْ وَلَوْ سَمِعُوا مَا اسْتَجَابُوا لَكُمْ وَيَوْمَ الْقِيَامَةِ يَكْفُرُونَ بِشِرْكِكُمْ وَلَا يُنَبِّئُكَ مِثْلُ خَبِيرٍ (14)
Ma'ana: Wannan Shi ne Ubangijinku, mulki na shi ne, kuma wadanda ku ke kira koma bayansa ba su mallakar ko da dan hancin dabino (13) in ma kun kiraye su ba su jin kiranku, kuma ko da sun jib a su iya amsa mu ku, kuma a ranar kiyama za su kafirce game da shirkerku, ba bu wanda zai ba ka labari kamar masani mai cikakken sani (14). (Suratu Assaba'i aya ta 13 da ta 14)
Fadin Allah: "ku ke kira koma bayan Sa" ya game Husaini da Abbas da sauran su.
Fadin Allah: "Da shirkarku" Ya na nufin cewa kiran waliyyai shirka ce.
Fadin Allah: " ba bu wanda zai ba ka labari kamar masani mai cikakken sani " Ya na nufin cewa ka da ka nemi wata fatawa bayan maganar Allah.
2- Kuma 'yan shi'a suna cewa "lallai waliyyai suna kusantar da su ga Allah kusanci a yayin da mu ke kiran su. Allah Ya ce:
وَالَّذِينَ اتَّخَذُوا مِنْ دُونِهِ أَوْلِيَاءَ مَا نَعْبُدُهُمْ إِلَّا لِيُقَرِّبُونَا إِلَى اللَّهِ زُلْفَى إِنَّ اللَّهَ يَحْكُمُ بَيْنَهُمْ فِي مَا هُمْ فِيهِ يَخْتَلِفُونَ إِنَّ اللَّهَ لَا يَهْدِي مَنْ هُوَ كَاذِبٌ كَفَّارٌ (3)
Ma'ana: wadanda suka riki majibinta koma bayansa (suna cewa) ba mu bauta musa sai dai don su kusantar da mu zuwa ga Allah kusanci, lallai Allah zai yi hukunci a tsakaninsu cikin abin da suke sabani a cikinsa, lallai Allah ba Ya shiryar da duk wani makaryaci mai yawan kafirci" Suratuz Zumar aya ta 3.
Fadin Allah da Ya ce: suka riki majibinta koma bayansa, watau suna kaunar su kamar yadda su ke kaunar Allah ko ma fiye.
Fadin Allah da Ya ce: sai dai don su kusantar da mu zuwa ga Allah kusanci. Watau da hujjan neman kusanci zuwa ga Allah.
Sannan sai Allah Ya fadi hukuncin mai irin wannan aikin Ya ce: lallai Allah ba Ya shiryar da duk wani makaryaci mai yawan kafirci, watau mai irin wannan aikin kafiri ne kuma makaryaci ne.
3- Yan shi'a su kan ce: ai waliyyai sukan cece mu a yayin da muke kiran su.
Allah Ya ce:
وَيَعْبُدُونَ مِنْ دُونِ اللَّهِ مَا لَا يَضُرُّهُمْ وَلَا يَنْفَعُهُمْ وَيَقُولُونَ هَؤُلَاءِ شُفَعَاؤُنَا عِنْدَ اللَّهِ قُلْ أَتُنَبِّئُونَ اللَّهَ بِمَا لَا يَعْلَمُ فِي السَّمَاوَاتِ وَلَا فِي الْأَرْضِ سُبْحَانَهُ وَتَعَالَى عَمَّا يُشْرِكُونَ (18)
Ma'ana:"Kuma suna bautawa koma bayan Allah abin da ba ya iya cutar da su ko amfanar da su, kuma suna cewa wadannan su ne masu ceton mu a gaban Allah. Ka ce; shin kuna ba wa Allah labari ne game da abin da bai sani ba a cikin sammai da kasa? Tsarki ya tabbata gareShi kuma Ya daukaka daga abin da su ke yi na shirka gare Shi" Suratu Yunus aya ta 18.
Na farko cikin wannan ayar Allah Ya ambaci aikinsu da cewa: suna bautawa koma bayan Allah, watau Allah Ya kira shi bauta.
Sannan Allah Ya ambaci da'awarsu Ya ce: kuma suna cewa wadannan su ne masu ceton mu, watau suna bauta musu ne da da'awar neman ceto.
Sannan sai Allah Ya fadi matsayin aikin na su Ya ce: "daga abin da su ke yi na shirka" watau kiran wanin Allah da hujjar neman ceto shi ma shirka ne.