طاهر جبريل دكو
_11 _December _2014هـ الموافق 11-12-2014م, 01:26 AM
MADINA BIRNIN MANZO
Godiya ta tabbata ga Allah, salati da sallama su tabbata ga Manzon Allah da alayensa da sahabbansa da wanda ya jibince shi ya bi tafarkinsu har zuwa ranan sakamako, bayan haka:
Lallai (garin) Madina na da falaloli da abubuwan da ta kebanta da su wadanda ba a samun su a wasu garuruwa da biranen musulunci, ita ce hasumiyar Musulunci, kuma ma farin da'awa da kira zuwa ga Allah bayan Makka, kuma inda Allah Ya zaba wa Annabi (صلى الله عليه وسلم) da sahabbansa don hijira.
A cikin ta Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya karasa rayuwarsa a shekarunsa na karshe – karshe, a cikin ta Allah Ya karbi raywarsa, kuma a cikinta kabarinsa mai daraja ya ke tare da abokansa biyu a rayuwar duniya da kabari da ma lahira sayyidina Abubakar da sayyidina Umar (رضي الله عنهما) bugu da kari masallacinsa mai alfarma ma a cikin Madina ya ke daya daga cikin masallatan da Annabawa suka gina kai! wannan kam ma shi ne wanda fiyayyen manzanni ya gina.
Lallai Madina ita ce Daibatu ddaibah (watau gari mai dadin zama) zuciyar Musulunci, kuma matattarar karfin sa, daga cikinta ne rundunonin tauhidi suka fita domin yada Musulunci da kuma yakar makiya Allah.
Idan mai ziyara ya taho Madina A munasaba ta ziyara ko aikin hajji ko umara niyyarsa ita ce ziyartan masallacin Annabi (صلى الله عليه وسلم) don ya yi sallah a ciki saboda Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya hana shirin tafiya ta musamman zuwa wani bigire da nufin aiwatar da ibada saboda falalar wurin sai dai dayan masallatai uku a inda ya ce:
" لا تشد الرحال إلا إلى ثلاثة مساجد: مسجدي هذا، ومسجد الحرام، ومسجد الأقصى "
Ma'ana: " Ba a nikar gari don tafiya ta musamman a nufi wani bigire don yin ibada a cikinsa sai dai dayan masallatai Uku; masallacin nan nawa da masallacin harami na Makka da masallacin Kudus" Bukhari da Muslim ne suka ruwaito shi.
Saboda haka idan za ka taho Madina, niyyarka ta kasance ta ziyartan masallacin Annabi (صلى الله عليه وسلم). Idan ka zo da wannan niyyar to ya halitta kuma ka ziyarci wuraren ziyara na garin Madina kari a kan masallaci na Annabi (صلى الله عليه وسلم).
Muna iya kasa ziyara a garin Madina gida biyu:
Ziyara ta ibada, da ziyara ta bude ido. Ta farko watau ziyara ta ibada wurarenta a garin Madina guda biyar ne, biyu daga cikin su masallatai ne uku kuma makabartu ne. Masallatan biyu kuwa su ne Masallacin Annabi (صلى الله عليه وسلم) mai falala, wanda nan gaba kadan bayani zai zo na falalolinsa. Masallaci na biyu shi ne masallacin kuba wanda shi ne Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya fara ginawa a yayin da ya yi hijira zuwa garin Madina masallacinda Allah Ya yabe shi a cikin Alkur'ani da cewa tun tubalin gininsa na farko an daura shi ne akan takawa da tsoron Allah, sannan Annabi ya ce:
«من تطهر في بيته ثم أتى مسجد قباء، فصلى فيه صلاة، كان له كأجر عمرة» سنن ابن ماجه (1412) :
Ma'ana:"Duk wanda ya yi alwala daga gidansa sannan ya tafi masallacin kuba ya yi salla a cikinsa, ya na da lada kamar na umara" Ibnu Majah ne ya ruwaito shi 1412. Albani ya inganta shi.
Saboda falalar masallacin Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya kasance ya kan je ko wane asabar akan abin hawa ko a kafa don ya yi sallah kamar yadda imamul Bukhari a cikin sahihinsa (1193) ya ruwaito da isnadinsa zuwa ga Abdullahi dan Umar (رضي الله عنهما) ya na cewa:
«كان النبي صلى الله عليه وسلم يأتي مسجد قباء كل سبت، ماشيا وراكبا» وكان عبد الله بن عمر رضي الله عنهما «يفعله»
Ladubban shiga masallacin kuba daya ne da na sauran masallatai kamar yadda zai zo cikin bayani game da masallacin Annabi (صلى الله عليه وسلم) nan gaba in sha Allahu.
Wuri na uku: Kabarin Annabi (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi)da sahabbansa biyu mafiya daraja (Abubakar da Umar) Allah ya kara musu yarda, zai fara da kabarin Annabi (sallallahu alaihi wasallam) yanamai cewa:
السلام عليك يا رسول الله ورحمة الله وبركاته جزاك الله عن أمتك خير ما جازا نبيا عن أمته
ASSALAMU ALAIKA YA RASULA LLAHI WARAHMATU LLAHI WABARAKATUHU JAZAKA LLAHU AN UMMATIKA KHAIRAMA JAZA NABIYYAN AN UMMATIHI
sannan ya matsa dama kadan gwargwdon zira'i daya ko makamancin haka sai ya ce:
السلام عليك يا أبابكر الصديق جزاك الله عن الإسلام والمسلمين خيرا
ASSALAMU ALAIKA YA ABABAKRIN ASSIDDIK JAZAKA LLAHU ANIL ISLAMI WAL MUSLIMINA KHAIRAN
sannan ya kara gaba kadan sai ya ce:
السلام عليك يا عمر الفاروق جزاك الله عن الإسلام والمسلمين خيرا
ASSALAMU ALAIKA YA UMARAL FARUK JAZAKA LLAHU ANIL ISLAMI WAL MUSLIMINA KHAIRAN.
Daga nan kuma sai ya fice ta babul baqi’i, wannan shi ne iyakacin abin da aka shar'anta masa ya yi a yayin ziyarar kabarin Annabi (sallallahu alaihi wasallam).
Wuri na hudu: Makabartan Baki'a:
Wannan makabartar ta na nan kusa da masallacin Annabi (sallallahu alaihi wa sallam) a bangaren kudu maso gabashin masallacin, wannan makabartan an binne sama da dubu goma daga sahabban Annabi (sallallahu alaihi wa sallam) da Iyalan gidansa wato wasu daga cikin matansa da yayansa da manya manyan malamai daga cikin tabi'ai da wxanda suka biyo baynsu, kuma ba a gushe ba har yau ana binne muminai bayin Allah a cikin wannan wuri. Annabi (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya kasance yakan ziyarce su a zamaninsa ya roqa musu rahamar Allah (Subahanahu wa ta'ala)
Wuri na biyar: Maqabartan shahidai na Uhudu.
Awannan wurin ne aka gwabza yakin nan da aka fi sani da yakin Uhudu a shekara ta uku bayan hijirar Annabi (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) daga Makka zuwa Madina, tsakanin rundunar Allah ta musulmai da rundunar shedan ta kafirai, inda kimanin mutum saba'in daga cikin sahabban Annabi (sallallahu alaihi wasallam). suka yi shahada kuma aka binne su awurin. Domin ziyartan wnnan maqabartan ta shahidai ne ake zuwa ziyara awurin ba don dutsen Uhudu ba. Waxannan maqabartu biyu (Baki'a da Uhudu) idan mutum ya je ana son ya yi kamar yadda ake yi a kowce makabarta, wato ya ce:
«السلام عليكم أهل الديار من المؤمنين والمسلمين، وإنا إن شاء الله بكم لاحقون، نسأل الله لنا ولكم العافية»
ASSALAMU ALAIKUM DARA KAWMIN MU'MININA WA INNA INSHA ALLAHU BIKUM LAHIKUNA NAS'ALU LLAHA LANA WA LAKUMUL AFIYAH.
Kuma bai dace mutum ya roqi Allah wani abun duniya ba asa'ad da ya ziyarci maqabarta koda kuwa kabarin Manzon Allah (sallallahu alaihi wasallam) ne saboda an shar'anta ziyartan makabarta ne domin tuna mutuwa.
Bayan wadannan wurare biyar duk wani wuri a garin Madina da ake zuwa don ziyara to ziyara ce kawai ta bude ido, ya halitta mutum ya je wurare na tarihi don gane wa idonsa abinda ya dade ya na ji a bakin malamai ko ya karanta a cikin littattafai, matukar mutum bai kudurce niyyar ibada ba da ziyartarsa wadannan wurare, to ba a cewa ya yi laifi sai dai ya kiyayi rudin shaidan, don wani ya kan ce bari in je in ga masallacin kiblataini (kamar yadda ya shahara dak da cewa tarihin juya alkibla a masallacin bai tabbata ba) ko ya ce zai je ya gano masallacin ijaba ko wurin da aka yi yakin khandak (wanda ya shahara da saba'u masajid) a karon farko mutum zai ce zan je ne kawai don in gani amma da ya isa sai ya ce to ya ya zan taho masallaci ban yi salla ba? To ka sani cewa duk wani aiki na ibada ba ya karbuwa a wurin Allah har sai ya cika sharudda guda biyu; tsarkin niyya (watau ikhlasi) da mutaba'a (watau koyi da Manzon Allah sallallahu alaihi wasallam) saboda haka tunda bai tabbata daga Annabi (sallallahu alaihi wasallam) ya na nufatan wani masallaci ba a garin Madina da nufin yin salla don falalar masallaci koma bayan masallacinsa da na kuba, to kai ma ka nisanci aikata hakan, sai dai idan ka samu kanka a wani masallaci dai dai da lokacin salla, to sai ka yi salla kamar ko ina, Allah Shi ne mafi sani.
KADAN DAGA CIKIN KEBANTATTUN FALALOLIN MADINA
· Lallai ita ma harami ce amintacciya kamar Makka, ya haramta a kashe abin farauta a cikinta, ko korar sa, kuma ba a cire bishiyarta ko haka ma tsiron da ya fito da kansa a cikinta, kuma ba a daukar abin tsuntuwa a cikinta saboda fadin Annabi (صلى الله عليه وسلم) :
" المدينة حرام ما بين عير إلى ثور لا يختلى خلاها، ولا ينفر صيدها، ولا تلتقط لقطتها إلا لمن أشاد بها، ولا يصلح لرجل أن يحمل فيها السلاح لقتال، ولا يصلح أن يقطع منها شجرة إلا أن يعلف رجل بعيره" رواه أحمد وأبو داوود وصححه الألباني
Ma'ana:" Madina harami ce daga dutsen Airu har zuwa dutsen Sauru, ba a cire tsironta, ba a korar farautarta, ba a daukar tsuntuwar cikinta sai dai ga wanda zai yi cigiyar mai shi, kuma ba ya kyautatuwa ga mutum ya dauki makami a cikinta domin yaki, kuma babu kyau a ciri wata bishiya a cikin ta sai da idan mutum ya na nufin ciyar da rakumarsa ne" Imamu Ahmad da Abu Dawuda ne suka ruwaito shi kuma Albani ya inganta shi.
· Ya na daga cikin falalolin Madina; haramcin kirkiran mummunan aiki a cikinta ko kuma bai wa masu kirkira mafaka saboda fadin Annabi (صلى الله عليه وسلم) :
"المدينة حرم ما بين عير إلى ثور، فمن أحدث فيها حدثا، أو آوى محدثا، فعليه لعنة الله والملائكة والناس أجمعين، لا يقبل منه يوم القيامة صرف ولا عدل".
Ma'ana: "Madina harami ce daga dutsen Airu har zuwa dutsen Sauru, duk wanda ya kirkiri wani mummunan aiki a cikin ta ko kuma ya bai wa mai kirkira mafaka, to tsinuwar Allah ta tabbata a kan sa da ta mala'iku, da ta mutane baki daya, ba za a karbi aikin farilla ko nafila ba daga gare shi" Bukhari da Muslim ne suka ruwaito shi.
Abin nufi da kirkirarren aiki shi ne duk wani sabon aiki mummuna da mutane basu san shi ba kuma basu saba da shi ba.
· Ya na daga cikin falalolin Madina: kasancewar imani na dawowa ya tattaru a cikinta, saboda haka ita ce makomar zukatan muminai, adadi nawa ne na mutane su ke burin zama a cikinta, kuma su ke kuka saboda begen ziyartan ta, da ni'imtuwa da yin salla a cikin masallacinta. Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya ce:
«إن الإيمان ليأرز إلى المدينة كما تأرز الحية إلى جحرها»
Ma'ana: "Lallai imani ya na tattaruwa zuwa Madina kamar yadda macijiya ta ke komawa zuwa ga raminta" Bukhari da Muslim ne suka ruwaito shi.
· Yana daga cikin falalolinta lallai ita ta na kore miyagun cikinta na mutane kamar yadda Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya ce :
أمرت بقرية تأكل القرى يقولون: يثرب، وهي المدينة، تنفي الناس كما ينفي الكير خبث الحديد ""
Ma'ana : " An umurce ni da (yin hijira zuwa) wani gari mai cinye garuruwa suna cewa da ita yathriba ita ce Madina ta na kore (miyagun) mutane kamar yadda zugazugi ke kore daudar bakin karfe". Bukhari da Muslim ne suka ruwaito shi. Wato ta na kore mara imani wanda babu alkhairi a tare da shi.
· Ya na daga cikin falalolin Madina Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya yi mata addu'ar lafiya da albarka inda ya ce:
«اللهم حبب إلينا المدينة كحبنا مكة أو أشد، اللهم بارك لنا في صاعنا وفي مدنا، وصححها لنا، وانقل حماها إلى الجحفة»
Ma'ana: "Ya Allah Ka sanya son Madina a zukatan mu kamar yadda ka sanya mana son Makka ko fiye, ya Allah Ka sanya albarka a cikin sa'inmu da mudunmu, kuma Ka kyautata ta gare mu, kuma Ka kauratar da zazzabin cikin ta zuwa Juhfa" Bukhari da Muslim ne suka ruwaito shi.
· Ya na daga cikin falalolin Madina; kwadaitarwa game da zama cikin ta da mutuwa a cikinta. Saboda fadin Annabi (صلى الله عليه وسلم) :
" من استطاع أن يموت بالمدينة فليمت، فإني أشفع لمن يموت بها "
Ma'ana: " Cikin ku duk wanda ya samu dammar mutuwa a Madina to ya mutu a cikinta, domin ni zan ceci wanda ya mutu a cikinta" Imamu Ahmad da Tirmidhi da wanin su ne su ka ruwaito shi kuma Albani ya inganta shi.
· Ya na daga cikin falalolin Madina; annoba ba ta shiga cikinta haka ma Dujal saboda fadin Annabi (صلى الله عليه وسلم) :
«على أنقاب المدينة ملائكة لا يدخلها الطاعون، ولا الدجال»
Ma'ana: " Daga mashigan Madina akwai mala'iku matsara annoba ba za ta shige ta ba haka nan ma Dujal" Bukhari da Muslim ne suka ruwaito shi.
A cikin sahihul Bukhari Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya ce:
«لا يدخل المدينة رعب المسيح الدجال، لها يومئذ سبعة أبواب، على كل باب ملكان»
Ma'ana :" Firgicin Almasihu Dujjal ba zai shiga Madina ba, a wannan lokacin za ta kasance da kofofi bakwai a ko wane kofa akwai mala'iku biyu"
· Ya na daga cikin falalolinta cewa babu wanda zai nufi mutanenta da sharri face Allah Ya halaka shi. Saboda fadin Annabi (صلى الله عليه وسلم) :
«لا يكيد أهل المدينة أحد، إلا انماع كما ينماع الملح في الماء»
Ma'ana: " Babu wanda zai nufi mutanen Madina da wani kaidi face ya narke kamar yadda gishiri ke narkewa acikin ruwa" Bukhari ne ya ruwaito shi.
· Ya na daga cikin falalolin Madina abinda Allah Ya sanya na amfani da kariya daga guba da sihiri a cikin Ajuwarta. Saboda fadin Annabi (صلى الله عليه وسلم):
«من أكل سبع تمرات مما بين لابتيها حين يصبح، لم يضره سم حتى يمسي»
Ma'ana: " Duk wanda ya ci dabinnai bakwai daga abinda ke tsakanin duwatsu biyu na ta (wato Madina) a yayin da ya wayi gari, to guba ba za ta cutar da shi ba har ya yammaita" Muslim ne ya ruwaito shi.
A wani lafazin ya ce :
«من تصبح سبع تمرات عجوة، لم يضره ذلك اليوم سم ولا سحر»
Ma'ana: " Wanda ya karya kumallo da dabinnai bakwai na ajuwa, a wannan yinin guba ba za ta cutar da shi ba ko sihiri" Bukhari da Muslim ne suka ruwaito shi.
· Ya na daga falalolin Madina kasancewan masallacin Annabi (صلى الله عليه وسلم) mai tarin falalolin nan na cikinta.
KADAN DAGA CIKIN KEBANTATTUN FALOLIN MASALLACIN ANNABI (صلى الله عليه وسلم)
Masallacin Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya kebanta da wasu falaloli wadanda ba a samun su a sauran masallatai da ba shi ba. Daga cikin su:
§ Salla a cikin masallacin Annabi (صلى الله عليه وسلم) ta dara salla a wani masallaci da ba shi ba saw dubu. Ya zo a cikin sahihul Bukhari da Muslim daga hadisin Abuhuraira (رضي الله عنه) Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya ce :
«صلاة في مسجدي هذا خير من ألف صلاة فيما سواه، إلا المسجد الحرام»
Ma'ana: " Salla daya a wannan masallacin nawa ta fi salla dubu a wani masallacin da ba shi ba sai dai masallacin Makka" Imam Annawawi ya ce :"Kuma wannan fifikon ya game sallolin farilla da nafila kamar Makka.
§ Yana daga cikin falalolinsa kasancewar sa daya daga cikin masallatai Uku da ake shirin tafiya ta musamman domin yin ibada a cikin su saboda fadin Annabi (صلى الله عليه وسلم) :

Ma'ana: " Ba a nikar gari don tafiya ta musamman a nufi wani bigire don yin ibada a cikinsa sai dai dayan masallatai Uku; masallacin nan nawa da masallacin Harami na Makka da masallacin Kudus" Bukhari da Muslim ne suka ruwaito shi.
§ Yana daga cikin falalolinsa kasancewa a cikinsa akwai wani bigire wanda dausayi ne daga dausayoyin Aljanna saboda abin da ya inganta a cikin sahihul Bukhari da Muslim na fadin Annabi (صلى الله عليه وسلم) cewa :
«ما بين بيتي ومنبري روضة من رياض الجنة»
Ma'ana : " Abin da ke tsakanin Gidana da Minbarina dausayi ne daga dausayoyin Aljanna"
§ Yana daga cikin falalolinsa duk wanda ya zo masallacin da nufin karatu ko karantarwa ya na matsayin wanda ya fita jihadi ne fi sabilillahi. Saboda fadin Annabi (صلى الله عليه وسلم) :
«من جاء مسجدي هذا، لم يأته إلا لخير يتعلمه أو يعلمه، فهو بمنزلة المجاهد في سبيل الله»
Ma'ana :" Duk wanda ya zo masallacin nan nawa bai zo ba face don wani alheri da zai koya ko ya koyar, to ya na matsayin mai jihadi ne fi sabilillahi" Ibnu Maja ne ya ruwaito shi kuma Albani ya inganta shi.
LADUBBAN SHIGA MASALLACIN ANNABI
(صلى الله عليه وسلم)
v Shiga da kafar dama ya na mai cewa :
((بسم الله، والسلام على رسول الله، اللهم اغفر لي ذنوبي وافتح لي أبواب رحمتك أعوذ بالله العظيم، وبوجهه الكريم، وسلطانه القديم، من الشيطان الرجيم))
Kamar yadda ya zo cikin hadisai ingantattu kamar haka;
عن فاطمة بنت رسول الله صلى الله عليه وسلم، قالت: كان رسول الله صلى الله عليه وسلم، إذا دخل المسجد يقول: «بسم الله، والسلام على رسول الله، اللهم اغفر لي ذنوبي وافتح لي أبواب رحمتك» ، وإذا خرج قال: «بسم الله، والسلام على رسول الله، اللهم اغفر لي ذنوبي، وافتح لي أبواب فضلك» ابن ماجه في السنن كتاب المساجد والجماعات باب الدعاء عند دخول المسجد 771 وصححه الألباني
عن حيوة بن شريح، قال: لقيت عقبة بن مسلم، فقلت له: بلغني أنك حدثت عن عبد الله بن عمرو بن العاص، عن النبي صلى الله عليه وسلم أنه كان إذا دخل المسجد قال: «أعوذ بالله العظيم، وبوجهه الكريم، وسلطانه القديم، من الشيطان الرجيم» ، قال: أقط؟ قلت: نعم، قال: فإذا قال: ذلك قال الشيطان: حفظ مني سائر اليوم أخرجه أبو داوود في السنن كتاب الصلاة باب فيما يقوله الرجل عند دخوله المسجد 466 وصححه الألباني
v Yin salla raka'o'i biyu kafin ya zauna saboda fadin Annabi (صلى الله عليه وسلم) :
«إذا دخل أحدكم المسجد، فلا يجلس حتى يصلي ركعتين»
Ma'ana :" Idan dayan ku ya shiga masallaci ka da ya zauna har sai ya sallaci raka'o'i biyu" Bukhari da Muslim ne suka ruwaito shi.
v An so ya yi sallah a cikin Rauda in dama ta samu saboda falalar wurin, in ko dama bata samu ba to sai ya yi sallar sa a duk inda ya samu dama a cikin masallaci. Amma idan sallar farilla ce to sahun gaba shi ya fi falala saboda fadin Annabi (صلى الله عليه وسلم)
«خير صفوف الرجال أولها»
Ma'ana :" Mafi alherin sahu ga maza shi ne farkonsa" Imamu Muslim ne ya ruwaito shi.
Da fadin Annabi (صلى الله عليه وسلم):
«لو يعلم الناس ما في النداء والصف الأول، ثم لم يجدوا إلا أن يستهموا عليه لاستهموا»
Ma'ana :" Da mutane sun san abinda ke cikin kiran salla da sahun farko na lada, sa'annan ya zama ba za su same shi ba sai sun yi kuri'a, to da za su yi kuri'ar" Bukhari da Muslim ne suka ruwaito shi.
v Ya kamata mutum ya kiyaye bakinsa a cikin masallacin Annabi (صلى الله عليه وسلم) saboda tare da kasancewar wurin masallaci wurin ibada, kuma nan ne makwancin Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) saboda haka kamar yadda zai zama rashin ladabi ga mutum ya daga muryarsa da surutu a gaban Annabi(صلى الله عليه وسلم) a lokacin da ya ke da rai, to haka nan ma baya ya rasu domin darajarsa bata ragu da komai ba bayan ya rasu. Kuma Allah na cewa a cikin suratul hujurat aya ta 2 da ta 3.
{يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا لَا تَرْفَعُوا أَصْوَاتَكُمْ فَوْقَ صَوْتِ النَّبِيِّ وَلَا تَجْهَرُوا لَهُ بِالْقَوْلِ كَجَهْرِ بَعْضِكُمْ لِبَعْضٍ أَنْ تَحْبَطَ أَعْمَالُكُمْ وَأَنْتُمْ لَا تَشْعُرُونَ (2) إِنَّ الَّذِينَ يَغُضُّونَ أَصْوَاتَهُمْ عِنْدَ رَسُولِ اللَّهِ أُولَئِكَ الَّذِينَ امْتَحَنَ اللَّهُ قُلُوبَهُمْ لِلتَّقْوَى لَهُمْ مَغْفِرَةٌ وَأَجْرٌ عَظِيمٌ (3)} [الحجرات: 2، 3]
Ma'ana:" Ya ku wadanda suka yi imani, ka da ku daukaka muryoyinku sama da muryar Annabi kuma ka da ku daga murya gare shi a yayin magana da shi kamar yadda sashenku ke magana da sashe, ka da ku bata ayyukanku alhali ba ku sakankancewa (2) Lallai ne wadanda su ke sassauta muryoyinsu a wurin Manzon Allah, wadannan su ne Allah Ya jarrabi zukatansu da takawa, suna da wata gafara da sakamako mai girma (3)
Imamul Bukhari ya ruwaito da isnadinsa zuwa ga Assa'ib ibn Yazid ya na cewa wata rana na kasance ina tsaye a cikin masallaci sai wani mutum ya wurge ni da tsakwanya, da na daga kai na duba sai na ga ashe Umar, sai ya ce da ni tafi ka zo min da wadncan mutanen guda biyu, da suka zo sai ya ce musu; ku su waye? Ko kuma ku daga ina ku ke? Sai su ka ce mu daga Da'ifa mu ke, sai ya ce da a ce ku 'yan gari ne da na lallasa muku jikinku da duka ba ku san cewa a masallacin Annabi (صلى الله عليه وسلم) ku ke ba ne? duba sahihul Bukhari 470.
Saboda haka ya kai da Allah Ya yi wa ni'imar ziyartan masallacin Annabi (صلى الله عليه وسلم), ka da ka manta cewa ka na wani wuri ne da babu kamar shi don haka kada ka shagala da yawo a garin Madina zuwa kasuwanni ko wasu masallatai da dalili bai inganta daga Annabi (صلى الله عليه وسلم) ba game da wani abu na falalarsu ka bar masallacin Annabi (صلى الله عليه وسلم).
Dahiru Jibril Dukku
dukku111@yahoo.com