تسجيل الدخول

مشاهدة النسخة كاملة : Muhimman fatawowi na malam jamilu zarewa kashi na biyu


طاهر جبريل دكو
_18 _November _2014هـ الموافق 18-11-2014م, 10:53 PM
MAHAIFIYATA TA RASU, ANA BIN TA AZUMI !
20 - Tambaya :
Aslm mlm dan Allah ina da tambaya : tun kafin a kama azumi uwata ba ta da lafiya har akayi sallah, rana ta 16 ga watan karamar sallah Allah yayi mata rasuwa, shin za mu ranka mata azumi ko ba sai mun ranka ba ? Allah ya saka da hairi.
Amsa :
To malam mutukar rashin lafiyar ta zarce mata, har zuwa lokacin mutuwarta, to ba za ku rama mata ba, tunda ba sakaci ta yi ba, saboda fadin Allah madaukaki : "Kuma duk wanda yake mara lafiya ko matafiyi to sai ya rama a kwanaki na daban" Bakara aya ta : 185, wato bayan Ramadahana, idan mara lafiya ya samu sauki, ko matafiyi ya dawo , Ka ga wanda bai samu sauki ba har ya mutu, zai zama bai kai lokacin da zai rama ba, don haka sai ya saraya akan shi . .
Amma idan ta samu damar ramawa, ta yi sakaci ba ta rama ba har ta mutu, to sai makusancinta ya rama mata, saboda fadin Annabi s.a.w. : "Duk wanda ya mutu akwai azumi akansa, to sai makusancinsa ya rama masa" . kamar yadda Bukhari ya rawaito shi a hadisi mai lamba ta : 1851. Duba Fataawa nuru aladdarb lamba ta : 247.
Allah ne mafi sani
HUKUNCIN BIN SALLAH DAGA LASIFIKA
21- Tambaya :
Malam gidanmu yana kusa da masallaci, muna jiwo kiran sallah da ikama ta lasipika, ko ya halatta in bi sallar jam'i daga laspika ?
Amsa :
To 'yar'uwa wannan mas'alar ta kasu kashi biyu :
1- Idan ya zama dakinki yana like da masallacin, to tabbas wannan ya halatta, saboda nana A'isha ta bi sallar kisfewa rana daga dakinta, a zamanin Annabi s.a.w. kamar yadda Bukhari ya rawaito hakan a hadisi mai lamba ta : 184, sannan Abdurrazak ya rawaito cewa : takan bi ragowar salloli daga dakinta" kamar yadda ya zo a littafinsa na Musannaf a hadisi mai lamba ta : 4883, saboda dakinta a jikin masallacin yake.
2. Idan ya zama dakin ba ya hade da masallacin, to zance mafi inganci shi ne : bai halatta ki bi ba, saboda a zamanin Annabi s.a.w. sahabbai suna haduwa ne a wuri daya ne idan za su yi sallar jam'i, ba sa rarrabuwa, wannan sai yake nuna cewa, hakan shi ne siffar sallar jama'i, sannan jera sawu a sallah, wani yana bin wani, dole ne .
Allah ne masani .
Don neman karin bayani duba : Fiqhunnawazil na Khalid Al-mushaikih shafi na : 50
MAGANIN CUTAR EBOLA
22- Tambaya :
Malam wani abokina ya yi min waya, yau da safe yace min na samu ruwa na zuba gishiri a ciki, sannan na karanta LAKAD JA'AKUM sai na yi wanka da shi, yana maganin cutar EBOLA, ko zan iya yin hakan ?
Amsa :
To dan'uwa Allah bai halicci wata cuta ba saida ya halicci maganinta, kamar yadda hakan ya tabbata a hadisi, saidai wancan abin da ya fadi maka binciken addini ko na likitanci bai tabbatar da shi a matsayin maganin ebola ba, ka ga kuwa musulunci ba ya gina hukunci akan abin da ba shi da madogara.
Duk da cewa har yanzu, ba'a gano hakikanin maganin cutar Ebola ba, saidai cutar Ebola na daga cikin nau'ukan rashin lafiya, wadanda Allah yake jarrabar bayinsa a lokacin da ya so, ana iya tunkude cututtuka ta hanyoyi masu zuwa :
1. Sadaka : saboda sadaka tana tunkude bala'i.
2. Yawaita istigfari, saboda istigfari yana fitar da mutum daga kuncin da yake ciki.
3. Yawaita salati ga Annabi s.a.w. saboda hakan yana yaye bakin ciki.
4. Biyawa musulmai bukata, saboda duk wanda ya yayewa wani bakin ciki, Allah zai yaye masa wanda yake damunsa .
5. Yawaita Tasbihi, saboda Allah ya tseratar da Annabi Yunus daga cikin kifi, saboda yawan tasbihinsa .
6. Yawaita addu'a, saboda addu'a tana tunkude sharri.
IDAN KA BI WADANNAN ABUBUWA ZA KA SAMU RIGAKAFI DAGA CUTAR EBOLA
Allah ne ma fi sani .
ABUBUWAN DA SUKE KAWO NUTSUWA A CIKIN ZUCIYA
23 - Tambaya :
Don Allah malam ta yaya zan samu nutsuwa a cikin zuciya ta?, saboda wani lokacin sai na ji zuciyata, kamar an kunna min wuta, wasu lokutan kuma bakin ciki ya hana ni bacci
Amsa :
To dan'uwa akwai abubuwan da malamai suka yi bayani cewa : suna kawo nutsuwa a zuciya, ga su kamar haka :
1. Cikakken tauhidi, ta yadda mutum zai bar duk wata shirka da bidi'a da abin da yake kaiwa zuwa gare su .
2. Shiriya da hasken da Allah yake jefawa a zuciyar bawa, wanda duk lokacin da aka rasa shi, sai bawa ya kasance cikin kunci.
3. Ilimi mai amfani, saboda duk lokacin da ilimin mutum ya yalwata, zai samu jindadi a zuciyarsa.
4. Dawwama akan zikirin Allah, saboda fadin Allah "Wadanda suka yi imani zuciyoyinsu suna nutsuwa da zikirin Allah" Suratu Arra'ad aya ta 28
5. Kyautatawa bayin Allah, saboda duk mutumin da yake yin kyauta zai kasance cikin kwanciyar hankali, kamar yadda marowaci yake kasancewa cikin kunci.
6. Fitar da kyashi da hassada daga zuciya.
7. Barin kallo da zancen da ba shi da fa'ida.
8. Barin baccin da ba shi da amfani.
9. Cin abinci gwargwadon bukata, da rashin karawa akan haka.
10. Rashin cakuduwa da mutane sai gwargwadon bukata.
Kishiyoyin wadannan abubuwa su ne suke jawo bakin ciki da damuwa da kuma kunci.
Don neman karin bayani duba zadul-ma'ad 2\22
Allah ne ma fi sani
24 - KA KIYAYE ALLAH ZAI KIYAYE KA
Yahya bn Mu'az yana cewa :
1. "Gwargwadon yadda ka ke jin tsoron Allah, gwargwadon yadda za ka samu kwarjini a wajan bayinsa"
2. "Gwargwadon yadda ka ke son Allah gwargwadon yadda halittu za su soka"
3. "Gwargwadon yadda ka ke shagaltuwa da abin da Allah ya umarce ka da shi, gwargwadon haka bayi za su hidimta maka
HUKUNCIN YIN DILKA
25 - Tambaya :
Mace taba da jikinta ga mata yan'uwanta don ayi mata wanka saboda kwalliya ko irin dilka da halawa din nan wai haramunne? Ko da ta rufe mamanta da mazaunanta? In haramun ne kenan daga ina zuwa ina ne tsiraicin mace da bai kamata yar'uwarta mace ta gani ba? Jazakallahu khairaljazaaa.
Amsa :
To 'yar'uwa malamai sun yi sabani game da tsaraicin mace ga 'yar'uwarta musulma, akwai wadanda suka tafi akan cewa : bai halatta 'yar'uwarta mace ta ga wani abu a jikinta ba, sai abin da ya saba bayyana a tsakanin mata, idan suna zaune isu-isu, kamar kafa da hannu da fuska da wuya da makamacin haka.
Saidai abin da mafi yawan malaman fiqhu suka tafi akai shi ne : al'aurar mace ga 'yar'uwarta musulma tana farawa ne daga cibiya zuwa guiwa, kamar yadda al'aurar maza take a tsakaninsu.
Don haka bai hallata ta bari wata mace ta kalli sama da wannan wurin da aka iyakance ba, amma idan kafira ce matar to malamai sun yi bayani cewa ba za ta kalli wani abu ba, sai abin da ya saba bayyana, don haka sai a kula lokacin da za'a je dilka wajan wacce ba musulma ba, don kada garin neman gira a rasa ido .
Sannan a bisa wannan bayanin da kika yi, dilkar da kika siffanta za ta zama ba ta halatta ba, tun da za'a ga abin da shari'a ba ta hallatata a gani ba.
26 - WASU DAGA CIKIN HUKUNCE-HUKUNCEN DA SUKA SHAFI RANAR IDI (1)
1. Azumtar ranar idi – ya haramta a azumci ranakun idi guda biyu, saboda hadisin Abu-sa'id Al-kudry, -Allah ya yarda da shi - cewa : "Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya hana azumtar ranaku biyu – wato ranar karamar sallah da ranar babbar sallah" Muslim ya rawaito
2. Siffar sallar idi- An karbo daga Abu-sa'id -Allah ya yarda da shi – cewa : "Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance yana fita ranar idin karamar sallah da babbar sallah zuwa filin idi, idan ya fita yana farawa da sallah" Bukari ne ya rawaito
Ana yin ta ne raka'o'i biyu, za'a yi kabbara bakwai a raka'a ta farko, a raka'a ta biyu kuma sai ayi kabbara shida. Abu-dawud
Idan mamu ya riski limaminsa a tsakiyar kabbarori, to zai yi kabbarar harama ne ya bi shi, ba zai rama abin da kubce masa ba na kabbarori, saboda sunnoni ne ba wajibai ba,
27 - MUHIMMANCIN KURUCIYAR YARO
Lokacin kuruciya lokaci ne muhimmi a rayuwar Dan’adam wanda ya kamata mutum ya yi amfani da shi wurin neman ilimi, saboda duk lokacin da mutum ya girma matsaloli su ka yi masa yawa sai ka ga ya kasa neman ilimi yadda ya kamata ko kuma idan ya haddace ya manta da wuri, amma idan yana yaro za ka ga duk abin da aka koya masa ya rike da wuri kuma ya zauna daram.
Magabata sun kasance suna bawa lokacin yarinta mahimmancin gaske, za ka ga tun yaro yana dan karami ya haddace alqur’ani, misali irinsu imamul Bukhari ya haddace kur’ani tun yana shekara bakwai, duk da cewa irin cigaban da mu ka samu a wannan zamanin su ba su same shi ba, kamar kaset da computer da talabijin da sauran abubuwan zamani wadanda suke sawwake karatu, duk da wadannan abubuwa za ka ga wasu daga cikinmu suna sakaci da lokacin kuruciyar yaransu, har za ka ga wasu sun fi damuwa yaro ya je ya yi wasa a mafi yawan lokutansa tare da yara a irin wannan lokaci mai mahimmanci
Ya kai dan’uwana ka yi kokari wurin amfani da kuruciyarka tun kafin matsaloli su yi maka yawa, Imamush Shafi’i yana cewa (da an dora min siyan albasa da ban haddace koda mas’ala daya ba) yana nufin da an dora masa matsalolin yau da kullum da bai iya yin karatu ba.
A KASANCE TARE DA MU A DARUSA NA GABA
28 - TURAKUN KYAWAWAN DABI'U GUDA HUDU NE
Ibnulkayyim yana cewa addini gaba dayansa kyawawan dabi'u ne, don haka duk wanda ya fika kyawawan dabi'u to ya fi ka addini.
Kyawawan dabi'u suna tsayuwa ne akan turaku guda hudu :
1. Hakuri : wanda shi ne yake sanya mutum ya zama mai juriya da hadiye fushi, kamar yadda yake sanya tafiya sannu-a-hankali, da rashin harzuka da kuma rashin gaggawa cikin lamura, kuma yana sanya kamewa daga cutar da wani.
2. Kamewa : wacce ita ce take kai mutum ga barin kaskantattun lamura, da abubuwan da ba su dace ba, ta kuma sanya shi ya zama mai kunya, wanda hakan zai sanya shi ya guji karya da rowa da annamimanci da cin naman mutane, da duk wani abu mara kyau.
3. Gwarzantaka : wacce ita ce take kai mutum zuwa ga kare mutuncin kansa, da aikata abin da zai bashi kima, da yin kyauta ta yadda zai iya rabuwa da abin da yake so, za ka iya cewa gwarzantaka wani abu ne da mutum zai iya rinjayar abokin gabarsa da shi, ta hanyar mallake zuciyarsa yayin fushi, kamar yadda ya zo a hadisi.
4. Adalci : wanda shi ne zai sanya shi ya daidaita dabi'unsa ta yadda za su zama tsaka-tsaki tsakanin ko-in-kula da wuce gona-da-iri.
Duk wasu dabi'u masu kyau da ka gani suna faruwa ne daga wadannan turakun guda hudu .
54196
HUKUNCIN MATAR DA TA YI AURE KAFIN A SAKETA
29 - TAMBAYA :
Mal. Mace ce aka aurar tana 'yar-shekara 14 ga wanda bata so, to sai mijin yayi tafiya har tsawon wata hudu (4) To sai matar tasa aka rubuta mata saki tace ya saketa, bayan ya dawo yace bai saketa ba, amma ba'a yarda ba. Da ta kare idda tayi aure da wani har suka haihu, daga baya kuma suka rabu, kuma yanzu ta ga musifu suna ta samunta, sai take tunanin ko wancan abin ne da tayi. Tana neman fatawa, ina hukuncin ta, da yaran data haifa da miji na biyu?
AMSA:
Malam amsar wannan tambaya yana da mutukar wahala, saidai na nemi taimakon wasu daga cikin malamaina, ga abin da na samo :
1. Abin da ta yi mummuna ne a shari'ar musulunci saboda ta yi aure cikin aure.
2. Zaman da su ka yi da mijinta na biyu, a matsayin mazinaciya take, saboda haka duk kwanciyar da suka yi da wannan mijin na ta zina ne.
3. Yaran da su ka Haifa da mijnta na biyu, 'ya'yansa ne, tun da bai san abin da ya faru ba a baya.
4. Har yanzu igiyar aurenta ba ta warware ba tsakaninta da mijinta na farko, saboda haka har yanzu ita matarsa ce saidai in ya sake ta.
5. Mijinta na farko, zai iya dawowa da ita, ba tare da sake daura aure ba, saidai dole sai bayan ta tuba, domin ita a matsayin mazinaciyya take, kuma Allah ya hana auren mazinaciya.
6. Ya wajaba a gare ta ta yawaita istigfari saboda girman zunubin da ta aikata.
7. Zai yi kyau su je wajan Alkali wanda ya san shari'ar musulunci, domin ya yi musu hukunci.
ALLAH NE MAFI SANI.
30 - ABUBUWAN DA SUKE TAIMAKAWA WAJAN SAMUN ILIMIN ADDINI
Tambaya :
Akaramukallahu Allah ya kara basira, kuma ina neman shawara cewa ni ina son na yi karatun addini, amma da na fara sai na ji kamar raina ba ya so, a bani shawara nagode
Amsa :
To dan'uwa akwai abubuwan da suke taimakawa wajan samun ilimin addini, ga muhimmai daga cikinsu :
1. Tsarkake niyya- duk lokacin da ka tsarkake niyyarka wajan neman ilimi, to Allah zai taimakeka.
2. Yin aiki da abin da mutum ya karanta- domin yin aiki da ilimi yana daga cikin abubuwan da suke taimakawa wurin rike ilimi da kuma kiyaye shi.
3. Neman taimakon Allah – saboda ana so mai neman ilimi ya dinga tunawa cewa Allah shi ne MASANI mai sanar da kowa, don haka ya dinga neman taimako a wurinsa yana rokonsa ya buda masa basira.
4. Nisantar zunubai, saboda ilimin addini haske ne, kuma hasken Allah ba ya bawa mai sabo.
5. Yawan maimaitawa, domin maimaita ilimi na daga cikin abubuwan da suke taimakawa wajan samun ilimi da tabbatarsa a zukata .
6. Jure wahala da kuma hakuri , saboda neman ilimi ba ya yiwuwa sai da wahala kuma duk wanda ba zai iya jure wahala ba, zai yi wuya ya iya neman ilimi yadda ya kamata.
7. . Farawa da abin da ya dace da dalibi, domin ana so dalibi ya fara da littafin da ya dace da shi wurin neman ilimi, saboda idan ya fara da littafin da ya wuce matakin karatunsa, ba zai fahimce ba.
Ina tabbatar maka mutukar ka rike wadannan to Allah zai taimakeka, ka samu ilimi cikin kwanciyar hankali .
ALLAH NE MAFI SANI
31 - SHIN BAIKO AURE NE ?
Tambaya :
Malam an yi min baiko da wani mutum, to shi ne zai yi tafiya sai ya biyo ta gidanmu wai yana so mu sadu, ya yi ta kawo min kauli-da-ba'adi, akan cewa, ai mun riga mun yi aure, ni dai gaskiya malam na ki yarda saboda ina da shakka akai, shi ne nake neman fatawa ?
Amsa;
To 'yar'uwa tabbas akwai malaman da suka yi fatawa a Nigeria cewa : baiko aure ne, saidai zance mafi inganci shi ne baiko ba aure ba ne saboda hujjoji kamar haka :
1. Abin da aka sani shi ne kudin da ake bayarwa yayin baiko ba'a bada su da nufin sadaki, duk da cewa wasu suna dunkulewa su bayar gaba daya, kin ga kuwa in haka ne, to ai dukkan aiyuka ba sa ingatuwa sai da niyya, kamar yadda ya zo a hadisni da dukkan malaman hadisi suka rawaito.
2. Bayan an yi baiko mutum zai iya cewa ya fasa, a dawo masa da kudinsa, kin ga wannan yana nuna ba aure ba ne.
3. Hakan zai iya bude hanyoyin barna, don dukkan wani ashararu zai iya kai kudi a yi masa baiko da wacce yake so ya yi lalata da ita, addinin musulunci kuma ya haramta duk abin da yake kaiwa zuwa barna.
4. Yana daga cikin sharudan auren a wajan wasu malaman samun shaidu, kin ga kuwa wani lokacin wanda zai kai kudin da za'a yi baiko, zai iya zama mutum daya, kin ga akwai nakasu kenan.
5. Abin da muka sani a kasar Hausa, sai bayan an yi baiko, ake sanya ranar daurin aure, kin ga wannann yana nuna cewa, baiko daban, aure daban.
6. Sannan duk mun yarda cewa baiko ba ya wajabta gado tsakanin wadanda aka yiwa, idan daya daga cikinsu ya mutu kin ga wannan yana nuna cewa ba aure ba ne, domin ma'aurata suna gadon junansu .
Allah ne ma fi sani .
HUKUNCIN MATAR DA TA AURI SAMA DA NAMIJI DAYA A LAHIRA
32 - Tambaya :
Malam matar da mijinta ya mutu, sai ta yi wani auren, shin za ta sake haduwa da na farkon a lahira, in dukkansu sun shiga aljanna, ko kuma na karshen shi ne zai zama mijinta a can ?
Amsa :
To dan'uwa malamai sun yi sabani akan wannan mas'alar zuwa zantuttuka guda uku :
1. Za ta zauna da wanda ya fi kyawawan dabi'u a duniya.
2. Za'a ba ta zabi.
3. Za ta zauna da na karshensu.
Wannan maganar ta karshe ita ce mafi inganci saboda fadin Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi cewa : "Duk matar da mijinta ya mutu, ta yi aure a bayansa, to ranar lahira za ta kasance ga na karshensu" Albani ya inganta shi a Sahihu-jamiussagir a hadisi mai lamba ta : 2704.
Wannan kuma shi ne dalilin da ya hana Ummuddarda'a aure bayan mijinta ya mutu, lokacin da Mu'awiya ya nemi ya aure ta, ta ki yarda ta aure shi, saboda tana so ta zauna da abudarda'a a lahira . duba silsilasahiha hadisi mai lamba ta : 1281
Munawy yana cewa : "Malamai suna cewa : Wannan shi ne daya daga cikin dalilan da suka sa matayan Annabi s.a.w. ba su yi aure ba bayansa, saboda Allah ya riga ya kaddara cewa : matayansa ne a aljanna" duba Faidhul-kadeer 3\151
Allah ne ma fi sani.
SHIN ANNABI MUHAMMAD S.A.W. NE FARKON HALITTA ?
33 - Tambaya :
Malam ina da wata tambaya wacce ta daure mun kai, idan ka san amsa don Allah ka bani tare da gamsassun hujjoji. Tambayata shi ne, shin Allah Annabi Muhammad ne ya fara halitta? Shin wai Allah ya ajiye shine sai lokacin da ya gadama sannan ya zo duniya?
AMSA :
Wa alaikum assalam
Akwai hadishin da ya zo wanda yake nuna cewa Annabi s.aw. shi ne farkon wanda aka fara halitta, saidai hadishin bai inganta ba, wasu malaman hadisin, kamar Ibnu-kathir a tarihinsa da Albani a silsilatussahiha hadisi mai lamba 458, sun ce hadisin karya ne.
Fadin cewa Annabi s.a.w. shi ne farkon wanda aka halitta ya sabawa alqur'ani, ta bangarori da dama ga wasu daga ciki :
1. Allah ya tabbatar da cewa Annabi Muhammad mutum ne kamar yadda hakan ya zo a ayoyi daban-daban, sannan kuma Allah ya tabbatar da cewa gaba daya mutane daga Annabi Adam aka same su, kin ga idan ka ce Annabi MUHD shi ne farkon halitta hakan ya sabawa ayoyin alqur'ani.
2. Tarihi ya zo da bayanin nasabar Annabi Muhammad s.a.w., tun daga mahafinsa har zuwa Annabi Ibrahim, kin ga wannan yana nuna an halicce shi ne daga maniyyin mahaifinsa, kamar yadda aka halicci ragowar mutane daga hakan.
Zance mafi inganci shi ne : farkon abin da Allah ya fara halitta shi ne Al'arshi, kamar yadda ya zo a cikin Sahihi Muslim a hadisi mai lamba 2653, cewa : "Allah ya kaddara abubuwa kafin ya halicci sama da kasa da shekaru dubu hamsin a lokacin Al'arshinsa yana kan ruwa"
Kin ga wannan yana nuna cewa Al'arshi ne farkon abin da aka fara halitta ba Annabi muhd s.a.w.
Allah ne mafi sani.
HUKUNCIN SIYAR DA TAKIN MASAI
34 - TAMBAYA :
Akramakallahu, menene hukuncin saye ko sayar da taki na masai? (kashin mutane wanda aka fito da shi daga shadda) don yin amfani da shi a gona?
To malamai suna kasa wannan gida biyu :
1. dan ya zama ya canza daga najasar zuwa wani suna daban, to wannan ya halatta a siyar da shi a zance mafi inganci, kamar takin zamani, bincike ya nuna ana hada shi da kashin mutum lokacin da ake yinsa, saidai tun da siffarsa ta canza daga siffar kashin mutum din ta hanyar magungunan da aka sanya masa, ka ga zai zama ya halatta a siyar da shi.
2. Wanda yake yana nan a sifarsa ta kashin dan'adam, to wannan mafiya yawan malamai suna hana siyar da shi saboda najasa ne, saidai malaman Hanafiyya suna halattawa, idan ya cakudu da kasa mai yawa, saboda bukatuwar mutane i zuwa hakan. Duba Raddul-muktar 5\57 Shafi'iyya kuma suna halatta amfani da shi amma suna hana siyar da shi, duba raudhatu dalibina na Nawawy 3\352
Allah ne mafi sani.
35 - ABUBUWAN DA SUKE TAIMAKAWA WAJAN YIN TSAYUWAR DARE
Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana cewa "Na hore ku da tsayuwar dare domin al'ada ce ta managarta da su ka zo gabaninku, kuma tana kusantarwa zuwa ubangiji, tana kuma kankare zunubai" Tirmizi
An tambayi Hasanul Basary cewa : (Me ya sa masu tsayuwar dare su ka fi kowa kyan fuska, sai ya ce: saboda sun kadaita da Ubangijinsu sai ya tufatar da su daga haskensa)
ٍSaidai akwai abubuwa da suke taimakawa akan haka ga wasu daga ciki :
1. Baccin rana : Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana cewa : " ku yi baccin rana domin shaidanu ba sa baccin rana" Hasanul Basary ya wuce wasu mutane a kasuwa, sai ya ce wadannan ba za su yi bacci ba, sai aka ce masa E, sai ya ce ina ganin darensu ba zai yi kyau ba" ma'ana ba za su iya tsayuwar dare ba.
2. Yin bacci da wuri , Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya karhanta bacci kafin sallar isha da kuma yin hira bayanta, kuma dalilin da ya sa ya karhanta hin hira bayanta saboda hakan zai iya hana mutum tsayuwar dare.
3. Aikata ladubban bacci yayin kwanciya, ta yadda zai karanta abin da ya zo a cikin sunna na ladubban bacci.
4. Umartar wani ya tashe shi kamar matarsa ko wanda suke tare.
5. Rashin cika ciki da abinci.
6. Nisantar yin aiki mai wahala da rana.
7. Nisantar abin da zai kawo maka fargaba a cikin zuciya, ta hanyar rage burirrika da tunanin abin da ya wuce
8. Nisantar zunubai, Fudhail bn Iyadh yana cewa : "idan ka ga ba ka iya tsayuwar dare, to ka tabbatar zunubanka sun yi yawa.
HUKUNCIN RUBUTUN SHA
36 - Tambaya :
DON ALLAH MALAM MENE HUKUNCIN RUBUTA QUR'ANI A SHA DA NUFIN TSARI KO KUMA MAGANI ?
Amsa :
To malam ba'a samu hakan daga annabi tsira da amincin allah su tabbata a gare shi ba, saidai an rawaito halaccin hakan daga wasu daga cikin sahabbai kamar Ibnu Abbas, ya zo a Zadul-ma'ad " Ibnu Abbas ya yi umarni a rubutawa wata mace mai tsananin nakuda wasu ayoyi na Alqur'ani, don ta samu sauki" haka kuma an rawaito halaccin hakan daga wasu tabi'ai kamar Mujahid , wannan kuma shi ne maganar Imamu Ahmad.
Don haka mutum ya karanta ayoyin shi ne ya fi, domin shi ne ya tabbata a ingantattun hadisai, saidai wanda ya rubuta ya sha ba za'a aibanta shi ba, tun da yana da magabata.
Allah ne mafi sani.
Don neman Karin bayani duba : Zadul ma'ad 4\170 da Majmu'ul fataawaa 19\64
37 - TAMBAYA :
MALAM MENENE HUKUNCIN 'YAN MATAN DA SUKE BADA HOTUNANSU GA TSOFAFI DON SU NEMA MUSU MIJIN AURE ?
AMSA
Addinin musulunci ya haramta kallo zuwa ga matar da ba muharrama ba, sai in akwai lalura, amma ya halatta ka kalli mace, idan kana so ka aure ta, kamar yadda ya zo a cikin hadisi, inda Annabi s.a.w. yake cewa : "Idan dayanku yana neman aure, to in ya sami damar kallon abin da zai kira shi zuwa aurenta, to ya aikata hakan" ABU DAWUD
Malamai sun yi sabani akan wurin da ya kamata mutum ya kalla a jikin mace lokacin da ya je neman aure :
1. Akwai wadanda suka ce zai kalli fuska da tafin hannu ne kawai.
2. Wasu malaman sun tafi akan cewa : zai kalleta a kayan da take sawa a cikin gida, ta fuskace shi ya kalle ta, sannan ta juya baya ya kalleta.
Wannan ra'ayin shi ne ya fi dacewa, saboda ta haka mutum zai san yanayin matar da zai aura.
Ta hanyar bayanan da suka gabata, za mu iya fahimtar cewa aikin dalilin aure ya hallata, amma da sharuda, ga wasu daga ciki :
1. Ya zama hoton ya fito da asalin fuskar matar, bai KWARZANTA ta ba, ta yadda za'a iya yaudarar namijin, ko a rude shi.
2. Ya zama wacce za'a bawa hoton mai amana ce, ta yadda ba za ta nunawa wanda ba shi da nufin aure ba, saboda asali ya haramta ayi kallo zuwa ga matar da ba muharrama ba, sai in akwai lalura, sai ga wanda yake nufin aurarta, wannnan yana nuna cewa, bai halatta asa irin wannan hoton na neman aure ba , a face book, ko a jarida.
3. Ka da hoton ya kun shi fito da tsaraici, ya wajaba a tsaya a iya inda shari'a ta bada umarni.
4. Zai fi dacewa ace mace ce za ta yi dalilin aure, saboda in namiji ne, zai iya fitinuwa da hotunan da yake gani, sai barna ta auku, don haka ita ma macen ya wajaba ta ji tsoron Allah a cikin aikinta.
Allah shi ne ma fi sani.
38 - HUKUNCIN YIN MASALLATAN JUMA'A GUDA BIYU A GARI DAYA
MALAM TAMBAYA : YANZU ZA KA GA DAN KARAMIN GARI, AMMA SAI KA GA SAMA DA MASALLACIN JUMA'A DAYA A CIKINSA, SHIN HAKAN YA HALATTA ?
AMSA
To malam babu wani hadisi ingantacce da ya hana hakan, saidai malamai sun yi sabani a cikin mas'alar zuwa maganganu guda uku : wacce ta fi inganci daga ciki, shi ne ya hallata ayi sama da masallacin juma'a guda daya a gari daya, mutukar akwai bukatar hakan, kamar ya zama masallacin farkon ba zai ishi mutane ba, ko kuma za'a samu wata fitina idan aka hadu wuri daya, ko ya zama akwai nisa tsakaninsu, ta yadda mutane za su sha wahala, wajan isowa zuwa gare shi.
idan babu bukata abin da ya fi shi ne yin masallaci guda daya a gari daya, saboda daga cikin hikimomin shar'anta juma'a akwai samun hadinkan musulmai, da kuma nishadantar da juna, da samun lada mai yawa, hakan kuwa zai fi tabbatuwa idan suka yi sallah a masallaci guda daya, wannan ita ce maganar Ibnu Taimimiyya da Ibnu Bazz da kuma Ibnu Uthaimin, da wasu manyan maluma Allah ya yi musu rahama .
ALLAH NE MA FI SANI.
HUKUNCIN MATAR DA TA YI AURE KAFIN A SAKETA
39 - TAMBAYA :
Mal. Mace ce aka aurar tana 'yar-shekara 14 ga wanda bata so, to sai mijin yayi tafiya har tsawon wata hudu (4) To sai matar tasa aka rubuta mata saki tace ya saketa, bayan ya dawo yace bai saketa ba, amma ba'a yarda ba. Da ta kare idda tayi aure da wani har suka haihu, daga baya kuma suka rabu, kuma yanzu ta ga musifu suna ta samunta, sai take tunanin ko wancan abin ne da tayi. Tana neman fatawa, ina hukuncin ta, da yaran data haifa da miji na biyu?
AMSA:
Malam amsar wannan tambaya yana da mutukar wahala, saidai na nemi taimakon wasu daga cikin malamaina, ga abin da na samo :
1. Abin da ta yi mummuna ne a shari'ar musulunci saboda ta yi aure cikin aure.
2. Zaman da su ka yi da mijinta na biyu, a matsayin mazinaciya take, saboda haka duk kwanciyar da suka yi da wannan mijin na ta zina ne.
3. Yaran da su ka Haifa da mijnta na biyu, 'ya'yansa ne, tun da bai san abin da ya faru ba a baya.
4. Har yanzu igiyar aurenta ba ta warware ba tsakaninta da mijinta na farko, saboda haka har yanzu ita matarsa ce saidai in ya sake ta.
5. Mijinta na farko, zai iya dawowa da ita, ba tare da sake daura aure ba, saidai dole sai bayan ta tuba, domin ita a matsayin mazinaciyya take, kuma Allah ya hana auren mazinaciya.
6. Ya wajaba a gare ta ta yawaita istigfari saboda girman zunubin da ta aikata.
7. Zai yi kyau su je wajan Alkali wanda ya san shari'ar musulunci, domin ya yi musu hukunci.
ALLAH NE MAFI SANI.

40 - TAMBAYA :
Malam : Akwai wani hadisi da yake Magana kan cewa kowa ya auri mace kawai dan kyanta Allah zai hana masa jin dadin kyan, ko dan kudinta kawai Allah zai hana masa jin dadin kudin,.... shin kuwa hadisin akwai shi kuma ya inganta?
AMSA :
GA YADDA HADISIN YA KE : DUK WANDA YA AURI MACE SABODA KUDINTA, ALLAH ZAI KARA MASA TALAUCI, DUK WANDA YA AURI MACE SABODA KYAWUNTA ALLAH ZAI KARA MASA MUNI
Saidai a cikin hadisin akwai Abdussalam bn Abdulkuddus wanda yake rawaito hadisan karya, don haka hadisin bai inganta ba.
Allah ne mafi sani