المساعد الشخصي الرقمي

مشاهدة النسخة كاملة : Muhimman fatawowi na malam jamilu zarewa


طاهر جبريل دكو
_18 _November _2014هـ الموافق 18-11-2014م, 09:54 PM
MUHIMMAN FATAWOWI NA MALAM JAMILU ZAREWA

1- HUKUNCIN MATAR DA TA AURI SAMA DA NAMIJI DAYA A LAHIRA
Tambaya :
Malam matar da mijinta ya mutu, sai ta yi wani auren, shin za ta sake haduwa da na farkon a lahira, in dukkansu sun shiga aljanna, ko kuma na karshen shi ne zai zama mijinta a can ?

Amsa :
To dan'uwa malamai sun yi sabani akan wannan mas'alar zuwa zantuttuka guda uku :
1. Za ta zauna da wanda ya fi kyawawan dabi'u a duniya.
2. Za'a ba ta zabi.
3. Za ta zauna da na karshensu.
Wannan maganar ta karshe ita ce mafi inganci saboda fadin Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi cewa : "Duk matar da mijinta ya mutu, ta yi aure a bayansa, to ranar lahira za ta kasance ga na karshensu" Albani ya inganta shi a Sahihu-jamiussagir a hadisi mai lamba ta : 2704.

Wannan kuma shi ne dalilin da ya hana Ummuddarda'a aure bayan mijinta ya mutu, lokacin da Mu'awiya ya nemi ya aure ta, ta ki yarda ta aure shi, saboda tana so ta zauna da abudarda'a a lahira . duba silsilasahiha hadisi mai lamba ta : 1281
Munawy yana cewa : "Malamai suna cewa : Wannan shi ne daya daga cikin dalilan da suka sa matayan Annabi s.a.w. ba su yi aure ba bayansa, saboda Allah ya riga ya kaddara cewa : matayansa ne a aljanna" duba Faidhul-kadeer 3\151

Allah ne ma fi sani.

2- SHIN AKWAI ZAKKA A CIKIN ALBASHI ?

Tambaya :
Malam yaya zakkar ma'aikaci ya kamata ta zamo? Domin wasu ma'aikatu sukan bada alawus a dunkule wanda ya isa zakkah to amma wasu sukanyi gini ko sayen filaye ko gonaki da kudin kafin shekara ta zagayo sun kare

Amsa :
To dan'uwa, hukuncin wannan albashi zai fara ne daga lokacin da ya shiga mulkinsa, don haka mutukar ba su shekara ba, to babu zakka a ciki, domin ba kawai samun nisabe ne ya ke wajabta zakka ba, dole sai an samu zagayowar shekara daga lokacin da kudin su ka shiga mulkinsa, don haka duk albashin da ya kai nisabin zakka, kuma aka ajjiye shi ya shekara to ya wajaba a fitar masa da zakka, amma mutukar shekara ba ta zagayo masa ba, to zakka ba ta wajaba ba akan wanda ya mallake shi ba.
saidai yana daga cikin dabarun da sharia ta haramta, mutum ya yi abin da zai sarayar masa da wajibi da gangan, don haka mutukar ya sayi filayan ne da nufin kaucewa fitar da zakka, to tabbas ya sabawa Allah.

Allah ne ma fi sani

3- HUKUNCIN BAWA MATAR AURE ZAKKAR FIDDA KAI

Tambaya :
Assalamu Alaiykum, Malam Shin ya halasta in baiwa matar aure zakkatil- fitr?
Amsa :
To dan'uwa malamai suna cewa ya halatta a baiwa matar aure zakkar fidda kai, mutukar tana cikin bukata, saidai wasu malaman suna cewa mutukar tana da miji wanda zai wadatar da ita, to ba za'a bata ba, domin yana daga cikin hikimomin zakkar fidda-kai wadatar da mutane a wannan ranar, daga barin roko.

Allah ne mafi sani

4- HUKUNCIN DALILIN AURE

TAMBAYA :
Malam menene hukuncin 'yan matan da suke bada hotunansu ga tsofafi don su nema musu mijin aure ?

AMSA
Addinin musulunci ya haramta kallo zuwa ga matar da ba muharrama ba, sai in akwai lalura, amma ya halatta ka kalli mace, idan kana so ka aure ta, kamar yadda ya zo a cikin hadisi, inda Annabi s.a.w. yake cewa : "Idan dayanku yana neman aure, to in ya sami damar kallon abin da zai kira shi zuwa aurenta, to ya aikata hakan" ABU DAWUD
Malamai sun yi sabani akan wurin da ya kamata mutum ya kalla a jikin mace lokacin da ya je neman aure :
1. Akwai wadanda suka ce zai kalli fuska da tafin hannu ne kawai.
2. Wasu malaman sun tafi akan cewa : zai kalleta a kayan da take sawa a cikin gida, ta fuskace shi ya kalle ta, sannan ta juya baya ya kalleta.
Wannan ra'ayin shi ne ya fi dacewa, saboda ta haka mutum zai san yanayin matar da zai aura.
Ta hanyar bayanan da suka gabata, za mu iya fahimtar cewa aikin dalilin aure ya hallata, amma da sharuda, ga wasu daga ciki :
1. Ya zama hoton ya fito da asalin fuskar matar, bai KWARZANTA ta ba, ta yadda za'a iya yaudarar namijin, ko a rude shi.
2. Ya zama wacce za'a bawa hoton mai amana ce, ta yadda ba za ta nunawa wanda ba shi da nufin aure ba, saboda asali ya haramta ayi kallo zuwa ga matar da ba muharrama ba, sai in akwai lalura, sai ga wanda yake nufin aurarta, wannnan yana nuna cewa, bai halatta asa irin wannan hoton na neman aure ba , a face book, ko a jarida.
3. Ka da hoton ya kun shi fito da tsaraici, ya wajaba a tsaya a iya inda shari'a ta bada umarni.
4. Zai fi dacewa ace mace ce za ta yi dalilin aure, saboda in namiji ne, zai iya fitinuwa da hotunan da yake gani, sai barna ta auku, don haka ita ma macen ya wajaba ta ji tsoron Allah a cikin aikinta.

Allah shi ne ma fi sani.
5- WURAREN DA YA HALATTA A SAKI MACE MAI HAILA

Tambaya :
Akaramakallah na ji an ce haramun ne a saki mace mai haila, to amma wani lokacin za ka ga kun samu rashin jituwa da matarka ta yadda ba za ka iya jiran lokacin tsarkinta ba, to malam akwai wasu lokuta ne da aka halattawa mutum ya saki matarsa ko da tana haila ?

Amsa :
To dan'uwa tabbas Allah ya yi umarni da kar a saki mace sai tana da tsarki kamar yadda yake cewa "Idan za ku saki mata to Ku sake su a farkon iddarsu) ma'ana a tsarkin da ba ku take su ba, Addalak aya ta : (1) saidai akwai wurare guda uku da ya halattta a saki mace mai haila :
1.Idan sakin ya kasance kafin ya kadaita da ita ko kafin ya sadu da ita, to anan ya halatta ya sake ta tana haila.
2. Idan ta yi hailar ne tana da ciki .
3. idan ya sake ta ne bayan ta fanshi kanta, to anan ya halatta ko da tana haila, saboda Annabi s.a.w. bai tambayi matar Thabit ba shin tana haila ne ko tana da tsarki, lokacin da zata yiwa mijinta kul'i, kamar yadda Bhukari ya rawaito a hadisi mai lamba ta : 5273.
Duba : Dima'uddaabi'iyya shafi na :33

In ban da wadannan wurare, to bai halatta a saki mai haila ba, kuma in har an sake ta, to sakin bai auku ba a wajen wasu malaman.
Allah ne mafi sani.

6- HUKUNCIN FUSKANTAR ALKIBLA YAYIN BIYAN BUKATA A BANDAKI

Tambaya :
salam ga tambaya yaya hukuncin mutumin da ya kalli alkibila yayin da yake biyan bukatarsa amma kuma yana bandaki ba'a fili yake ba ?

AMSA :
To kanina, malamai sun yi sabani akan mas'alar, Abu-hanifa ya hana hakan , Malik ya tafi akan cewa mutukar a gida ne to babu laifi, saboda hadisin Abdullahi dan Umar wanda yake cewa : "Na hau dakin Hafsa sai na ga Annabi s.a.w. yana biyan bukatarsa, yana fuskantar Sham ya kuma juyawa alkibla baya", kamar yadda Bukari ya rawaito a hadisi mai lamba ta : 145.
Saidai abin da ya fi shi ne : kar mutum ya fuskanci alkibla, ko da a gida ne, saboda hadisin Abu-ayyub wanda Annabi s.a.w. yake cewa : "Idan kuka zo yin bahaya to kada ku fuskanci alqibla kada kuma ku bata baya" Bukhari a hadisi mai lamba ta : 394 da muslim a hadisi lamba ta : 264
Duba bidayatul-mujtahid 1\115.

Tabbas rashin kallon alqibla yayin biyan bukata shi ne ya fi, saboda hadisin da ya gabata da kuma fita daga sabanin malamai, don haka idan mutum zai gina shadda a gidansa zai yi kyau ya kautar da ita daga alkibla .

Allah ne mafi sani .



7- WA YA FI KOWA KARYA A CIKIN HALITTUN ALLAH ?

Tambaya :
Don Allah malam a cikin kungiyoyin gaba daya wadanda ake dangantawa da musulunci wadanne ne suka fi kirkiro abubuwan da ba su da alaka da musulunci, don su kare akidarsu ?

Amsa :
To dan'uwa gaba daya a cikin kungiyoyin musulunci babu wadanda suka fi 'yan shi'a karya, da kirkire-kirkire marasa asali, ga abin da daya daga cikin magabata yake cewa :
Ma'abota ilimi da masu hankali sun cimma daidaito cewa : 'yan shi'a sune kungiyar da suka fi kowa karya, kuma karyarsu dadaddiya ce, wannan ya sa malaman hadisi suke banbance su daga mutane saboda yawan karyar su, ga maganganun wasu daga cikinsu :
Abuhatim Arrazy yana cewa : "An tambayi Malik game da rafidha (Yan shi'a) sai ya ce : "Kar ku yi Magana da su, kar kuma ku yi riwaya daga gare su, saboda suna karya"
Imamush Shafi'i yana cewa " Ban taba ganin wadanda su ka fi iya shaidar zurr ba, kamar Rafidha"
Sharik kuma yana cewa : "Ina daukar ilimi daga duk wanda na hadu da shi amma ban da 'yan shi'a, saboda suna yiwa Annabi s.a.w. karya"

Duk wanda ya jarraba su, zai gane tsananin karyarsu, ta yaya zuciya za ta amince da wanda karyarsa ta yi yawa ?.
Duba Minhaaj 2\467

8- HUKUNCIN MIJIN DA MATARSA TA NEME SHI DA JIMA'I BAI AMSA MATA BA

Tambaya :
malam ina roko a taimaka min da amsar tambayata, malam na san idan miji ya nemi matar sa don saduwa ita kuma ta ki, ta aikata babban zunubi, to idan mace ta nemi mijin ta shi kuma yaki, shi ma ya aikata zunubi ne ko ko?

Amsa :
To dan'uwa hadisi ya tabbata daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi cewa "Idan miji ya kira matarsa zuwa shimfidarsa ba ta amsa masa ba, to mala'iku za su tsine mata har ta wayi gari" kamar yadda Muslim ya rawaito a hadisi mai lamba ta : 1436.
Saidai abin da malamai suke cewa shi ne : namiji ba shi da laifi,idan matarsa ta neme shi bai amsa mata ba mutukar ba da nufin cutar da ita ya yi hakan ba, domin namiji da mace sun bambanta, saboda mace za'a iya saduwa da ita ko da ba ta da sha'awa, namiji kuwa sai yana da sha'awa, zai iya saduwa, don haka akwai bukatar ace yana da nishadi kafin ya iya jima'i, idan haka ne kuwa ba zai yiwu ya sadu da mace ba duk sanda take so ba, Allah kuma ba ya dorawa rai sai abin da za ta iya, sannan sha'awar maza ta fi ta mata karfi, saboda haka yawanci namiji ne yake neman matarsa ba akasin haka ba.

Allah ne ma fi sani.

9- HUKUNCIN AURAN KRISTA

Tambaya :
Malam musulmi zai iya auren ahlul-kitab tana addininta yana musuluncinsa ?

Amsa :
To dan'uwa Allah madaukaki ya halatta auren ahlul-kitabi, wato Yahudu da Nasara, kamar yadda ya yi bayanin hakan a cikin suratul Ma'ida aya mai lamba ta : (5), kuma an samu wasu daga cikin sahabai, sun aure su kamar Usman dan Affan - halifa na uku a musulunci- ya auri Banasariya, haka Dalhatu dan Ubaidillah ya auri Banasariya, sannan Shi ma Huzaifa ya auri Bayahudiya, Allah ya kara musu yarda. duba : Ahkamu-ahlizzimah 2\794

Saidai malaman wannan zamanin suna cewa, abin da ya fi shi ne rashin auren Ahlul-kitab saboda yadda zamani ya canza, domin da yawa idan mijinsu musulmi ya mutu yaran suna zama kirista, kai wani wani lokacin ko da sakinta ya yi zata iya guduwa da yaran, sannan zai yi wuya ka samu kamammu wadanda ba su taba zina ba a cikinsu .
Wasu kasashen kuma idan za ka auri kirista daga cikinsu dole sai ka yarda da dokokin kasarsu, a lokuta da yawa kuma za ka samu dokokin sun sabawa ka'idojin musulunci .

Allah ne mafi sani.

10- HUKUNCIN AURAN BAYAHUDIYA KO BANASARIYA GA MUSULMI

Tambaya :
Malam musulmi zai iya auren ahlul-kitab tana addininta yana musuluncinsa ?

Amsa :
To dan'uwa Allah madaukaki ya halatta auren ahlul-kitabi, wato Yahudu da Nasara, kamar yadda ya yi bayanin hakan a cikin suratul Ma'ida aya mai lamba ta : (5), kuma an samu wasu daga cikin sahabai, sun aure su kamar Usman dan Affan - halifa na uku a musulunci- ya auri Banasariya, haka Dalhatu dan Ubaidillah ya auri Banasariya, sannan Shi ma Huzaifa ya auri Bayahudiya, Allah ya kara musu yarda. duba : Ahkamu-ahlizzimah 2\794

Saidai malaman wannan zamanin suna cewa, abin da ya fi shi ne rashin auren Ahlul-kitab saboda yadda zamani ya canza, domin da yawa idan mijinsu musulmi ya mutu yaran suna zama kirista, kai wani wani lokacin ko da sakinta ya yi zata iya guduwa da yaran, sannan zai yi wuya ka samu kamammu wadanda ba su taba zina ba a cikinsu .
Wasu kasashen kuma idan za ka auri kirista daga cikinsu dole sai ka yarda da dokokin kasarsu, a lokuta da yawa kuma za ka samu dokokin sun sabawa ka'idojin musulunci .

Allah ne mafi sani.







11- BAMBANCI TSAKANIN RIIBA DA RIBA

Tambaya :
Don Allah ina da tambaya: wai ma ye riba a musulunci? kuma idan mutum ya siyi abu nera 5 ya halatta ya saida akan nera 8 ?

Amsa :
To malama riba ta kasu kashi biyu :
1. Akwai ribar jinkiri, kamar ka ba mutum bashin naira hamsin, ka nemi
ya dawo maka da naira sittin, ko kuma idan ka bawa mutum bashi, ya yi jinkirin biya, ka ninninka masa kudin da ka ba shi, irin ribar da ake amsa a banki, za ta shiga cikin wannan bangaren.
2. Ribar fi-fiko, kamar yanzu, ki bada naira 1100 tsofafi, a ba ki naira 1000 sababbi, ko kuma ki bayar da shinkafa 'yar gwamnati kwano uku, a ba ki shinkafa ta gida kwano hudu.
Duka wadannan nau'oin guda biyu Allah ya haramta su, kuma ya kwashe musu albarka.

Amma idan mutum ya sayi abu naira 5, ya sayar naira 8, wannan ba'a kiran shi riba a musulunci, saboda yana daga cikin riibar da Allah ya halatta, saidai ana so idan mutum yana siyar da kaya ya saukaka, Annabi s.aw. yana cewa : "Rahamar Allah ta tabbata ga mutumin da idan zai siyar da kaya yake rangwame", kamar yadda ya zo a hadisin Bhukari mai lamba ta : 2076

Allah shi ne mafi sani.


12- HUKUNCIN CANZA WURI BAYAN SALLAR FARILLA KAFIN SALLAR NAFILA

Tambaya :
Menene asali ko dalili idan mutum ya idar da salla zai yi nafila sai naga ya dan matsa baya ko gaba daga inda yayi sallarsa, akwai hadisi ne akan haka?

AMSA :
To dan'uwa Akwai hadisin da yake nuna haka, saidai wasu malaman hadisin sun raunana shi kamar Bukhari a sahihinsa, a hadisi mai lamba : 848, amma Albani ya inganta shi saboda yawan hanyoyinsa, a cikin littafin Sahihu sunani abi-dawud 3\178
Saidai malamai suna cewa : ana so ayi hakan saboda gurare da yawa su yi ma mutum shaida,
Amma abin da ya fi ga liman shi ne canza wuri, saboda abin da aka rawaito daga Aliyu - Allah ya kara masa yarda- yana cewa : "Yana daga cikin sunna, liman ya canza wuri idan zai yi sallar nafila" wannan yasa Imamu Ahmad ya karhantawa liman ya yi nafila a inda ya yi sallar farilla, don kar a zaci sallar ba ta kare ba . Fathul-bary 2\335

ALLAH NE MAFI SANI



13- HUKUNCIN MIKEWA MALAMI KO SHUGABA SABODA GIRMAMAWA

Mal. Ina tp ne yanzu, kuma idan na je aji yara suna mikewa domin gaishe ni mal. na barsu su cigaba ko na dakatar da su ?

Amsa :
To dan'uwa akwai malaman da suka ta fi akan cewa makaruhi ne a mikewa malami, akwai wadanda kuma suka halatta.
Saidai maganar da ta fi ita ce bai hallata malami ya nemi a mike masa ba, saboda fadin Annabi s.a.w. " Duk wanda ya so mutane su mike masa to ya tanaji wurin zamansa a wuta" kamar yadda tirmizi ya rawaito shi kuma ya kyautata shi a hadisi mai lamba ta : 2755, Albani kuma ya inganta shi a silsilatussahihah, hadisi mai lamba ta : 5957
Amma idan aka mikewa mutum ba tare da ya nema ba, to wannan babu laifi ga wanda ya mike da wanda aka mike saboda shi, domin ya zo a hadisi cewa : Annabi s.a.w. ya mikewa zaid bn haritha lokacin da ya dawo daga tafiya, kamar yadda ya zo a hadisin da Tirmizi ya rawaito shi kuma ya kyautata shi a lamba ta : 2732, saidai wasu malaman sun raunana wannan hadisin kamar albani a dha'ifuttirmizi 1\326

Allah ne mafi sani


14- BAMBANCI TSAKANIN MUNAFUNCIN ZUCIYA DA MUNAFUNCIN AIKI

Tambaya :
Mal. menene bambanci tsakanin nifakul amali da i'itikaadi ?

Amsa :
To malam : Nifaqul i'itikadi (wanda ake kudurcewa a zuciya) shi ne boye kafurci da kuma bayyana musulunci, kamar yadda wasu mutane suka yi a zamanin Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, duk wanda ya siffantu da wannan to ba musulmi ba ne.
Amma nifakul-amali (aiki) kuwa to shi ne wanda ya zo a cikin hadisin abdullahi dan amr inda annabi s.a.w. yake cewa : "Dabi'u guda hudu duk wanda suka kasance tare da shi, to ya zama cikakken munafiki, wanda kuma yake da daya daga cikinsu to yana da dabi'ar munafukai har sai ya barta : idan ya yi zance ya yi karya, idan aka amince masa ya ci amana, idan ya yi alkawari ya yi yaudara, idan ya yi husuma sai ya yi fajirci". Bukhari ya rawaito shi a hadisi mai lamba ta : (34) da Muslim a hadisi mai lamba ta : (106)
Don haka in mutum ya siffantu da daya daga cikin wadannan dabi'u guda hudu, to bai fita daga musulunci ba, saidai yana da tawayar imani.

ALLAH NE MAFI SANI


15- IDDAR MATAR DA BA TA AL'ADAR WATA-WATA

Tambaya :
Malam idan ya zama mace ba ta yin haila sai duk bayan wata uku, yaya idarta za ta kasance ?

Amsa :
To malam dole ne, sai ta yi jini uku kamar yadda Hanafiyya suka fada, ko kuma tsarki uku kamar yadda Malikiyya suka tafi akai, ko da kuwa duk shekara take yin haila sau daya, saboda Allah madaukaki ya rataya idda ne da samuwar jini, kamar yadda yake cewa a cikin suratul Bakara aya ta : 228 "Kuma matan aka saka, to za su jira tsawon jinane uku"
DON HAKA DUK TSAWON LOKACIN DA ZA TA ZAUNA TO DOLE SAI TA JIRA SU, KAMAR YADDA AYAR TAKE NUNAWA.

Allah ne mafi sani.

16- SHIN ANNABI MUHD S.A.W. NE FARKON HALITTA ?

Tambaya :
Malam ina da wata tambaya wacce ta daure mun kai, idan ka san amsa don Allah ka bani tare da gamsassun hujjoji. Tambayata shi ne, shin Allah Annabi Muhammad ne ya fara halitta? Shin wai Allah ya ajiye shine sai lokacin da ya gadama sannan ya zo duniya?

AMSA :
Wa alaikum assalam
Akwai hadishin da ya zo wanda yake nuna cewa Annabi s.aw. shi ne farkon wanda aka fara halitta, saidai hadishin bai inganta ba, wasu malaman hadisin, kamar Ibnu-kathir a tarihinsa da Albani a silsilatussahiha hadisi mai lamba 458, sun ce hadisin karya ne.
Fadin cewa Annabi s.a.w. shi ne farkon wanda aka halitta ya sabawa alqur'ani, ta bangarori da dama ga wasu daga ciki :
1. Allah ya tabbatar da cewa Annabi Muhammad mutum ne kamar yadda hakan ya zo a ayoyi daban-daban, sannan kuma Allah ya tabbatar da cewa gaba daya mutane daga Annabi Adam aka same su, kin ga idan ka ce Annabi MUHD shi ne farkon halitta hakan ya sabawa ayoyin alqur'ani.
2. Tarihi ya zo da bayanin nasabar Annabi Muhammad s.a.w., tun daga mahafinsa har zuwa Annabi Ibrahim, kin ga wannan yana nuna an halicce shi ne daga maniyyin mahaifinsa, kamar yadda aka halicci ragowar mutane daga hakan.
Zance mafi inganci shi ne : farkon abin da Allah ya fara halitta shi ne Al'arshi, kamar yadda ya zo a cikin Sahihi Muslim a hadisi mai lamba 2653, cewa : "Allah ya kaddara abubuwa kafin ya halicci sama da kasa da shekaru dubu hamsin a lokacin Al'arshinsa yana kan ruwa"
Kin ga wannan yana nuna cewa Al'arshi ne farkon abin da aka fara halitta ba Annabi muhd s.a.w.
Allah ne mafi sani.





HUKUNCIN KARBAR HAYAR DA ZA TA KAI GA MALLAKAR ABU
Tambaya :
Menene hukuncin shari'a akan irin yanda mutane suke yi, na sayan abin hawa su bawa direba da sharadin cewa : a kullum zai kawo wani ayyanannen kudi (kamar N500), har na zuwa tsawon kamar shekara, akan cewa idan ya shekara yana kawowa abin hawan ya zamo na sa.
Amsa :
To dan'uwa wannan ciniki daga baya ya shigo cikin kasashe musulmai, amma malamai magabata ba su san shi ba, saboda da can a kasashen turawa aka san shi, don haka malaman wannan zamanin suka yi sabani akan wannan mas'alar, akwai wadanda suka halatta wasu bangarori na wannan mua'amala, saidai fatawar manyan malaman Saudiyya da kuma kwamitin fatawa na din-dai-din ita ce : haramta wannan nau'i na haya kamar yadda suka tabbatar da hakan a zamansu na ranar :29/10/1420 saboda ya kunshi zalunci, domin zai iya yiwuwa, mutum ya sare kafin ya kai lokacin da aka diba masa, ka ga kudin da ya biya a baya, ba zai ci gajiyarsu ba, sannan ciniki biyu ne cikin ciniki, don haka ya haramta, kuma hanya ce da za ta jawo talakawa su dinga cin bashi, ba tare da sun damu ba.
Allah ne ma fi sani
HUKUCIN AMFANI DA MAGANIN DA YAKE HANA HAILA
Tambaya :
Allah ya gafarta malam, azumi ya zo ni kuma ba na son na sha ko azumi daya, to shi ne na sayi maganin da zai hanani yin al'ada na sha, bayan mun hadu da kawata, sai take ce min wai babu kyau, shi ne na ce mata ban yarda ba, zan tambayi malamai, don Allah malam a kara min haske ?
Amsa :
To 'yar'uwa amfani da maganin da yake hana haila ya halatta, amma da sharuda guda biyu :
1. Idan ya zama ba zai cutar ba, amma idan zai cutar, to ya haramta saboda fadin Allah “kar ku jefa kawunanku a cikin halaka” suratu Albakarah aya ta 195
2. Ya zama da iznin miji ne, idan hakan ya shafe shi, kamar idan tana iddar da ciyarwa ta wajaba akanshi, to anan bai halatta ta yi amfani da abin da zai hana haila ba saida izninsa, haka nan idan ya zama maganin zai hana daukar ciki to a nan ma dole saida iznin miji.
Saidai duk da cewa hakan ya halatta da sharudan da suka gabata, amma barinsa shi ya fi, sai idan bukatar hakan ta ta so, saboda mutum ya zauna akan yadda yake ya fi masa kwanciyar hankali akan ya yi abin da zai canza dabi’arsa, musamman ma wasu daga cikin kwayoyin na zamani suna dagula kwanakin haila, kamar yadda ya bayyana gare mu, sai a kiyaye.
Don neman karin bayani, duba : Dima'uddabi'iyya shafi na : 54 .
Allah ne mafi sani.

KA’IDOJIN HADDACE AL-QUR’ANI
Tambaya :
Assalamu alaikum, malam don Allah ni karamin dalibi ne, ban dade da fara hadda ba, shi ne nake so a taimaka min da hanyar da zata kai ni zuwa haddace Alqur'ani.
Amsa :
To dan'uwa, ina fatan Allah ya datar da kai zuwa alkairi, ga wasu daga cikin hanyoyin da za su taimaka maka, wajan hadda, mutukar ka kiyaye su, to za ka samu hadda mai kwari :
1. Ya wajaba ka rinka yin hadda a wajan malami saboda ya dinga gyara maka.
2. Idan za ka fara hadda ka fara daga suratu Annas saboda ta fi sauki.
3. Ka da ka dinga haddace abu mai yawa, musamman farkon fara haddarka, saboda wannan zai jawo ka yi hadda mara karfi, ya kamata ka dinga yi daidai yadda zaka iya yin muraja’a , don ka inganta haddarka .
4. Ka rinka yin hadda da al-qur’ani iri daya, saboda hakan zai taimaka ka dinga tuna gurin da kowacce aya take, da kuma tuna inda kowanne shafi ya ke karewa.
5. Duk lokacin da ka haddace izu daya, to kar ka wuce shi, har sai ka maimaita shi a kalla sau ashirin, kafin ka dora na gaba.
6. Idan haddarka ta yi zurfi, to ka samu wanda za ku dinga yin muraja'a da shi, domin wannan yana taimakawa wajan karfin hadda yadda ya kamata.
Don neman Karin bayani, duba : khuduwatun ilassa’adah 200-201
Allah ne ma fi sani
TSARAICIN MACE GA 'YAR'UWARTA MACE
Tambaya :
Mace taba da jikinta ga mata yan'uwanta don ayi mata wanka saboda kwalliya ko irin dilka da halawa din nan wai haramunne? Ko da ta rufe mamanta da mazaunanta? In haramunne kenan daga ina zuwa ina ne tsiraicin mace da bai kamata yar'uwarta mace ta gani ba? Jazakallahu khairaljazaaa.
Amsa :
To 'yar'uwa malamai sun yi sabani game da tsaraicin mace ga 'yar'uwarta musulma, akwai wadanda suka tafi akan cewa : bai halatta 'yar'uwarta mace ta ga wani abu a jikinta ba, sai abin da ya saba bayyana a tsakanin mata, idan suna zaune isu-isu, kamar kafa da hannu da fuska da wuya da makamacin haka.
Saidai abin da mafi yawan malaman fiqhu suka tafi akai shi ne : al'aurar mace ga 'yar'uwarta musulma tana farawa ne daga cibiya zuwa guiwa, kamar yadda al'aurar maza take a tsakaninsu.
Don haka bai hallata ta bari wata mace ta kalli sama da wannan wurin da aka iyakance ba, amma idan kafira ce matar to malamai sun yi bayani cewa ba za ta kalli wani abu ba, sai abin da ya saba bayyana, don haka sai a kula lokacin da za'a je dilka wajan wacce ba musulma ba, don kada garin neman gira a rasa ido .
Allah ne mafi sani



Top of Form






Bottom of Form