ãÔÇåÏÉ ÇáäÓÎÉ ßÇãáÉ : tarihin Annabi sallallahu alaihiwa sallam daga daliban Ma'ahad gombe
ØÇåÑ ÌÈÑíá Ïßæ
_5 _November _2014åÜ ÇáãæÇÝÞ 5-11-2014ã, 12:16 PM
TARIHIN
Sallallahu alaihi wasallam
daga tushe na ainihi da ingantattun riwayu.
1432H
Daga daliban ma’ahad (IQMIC) Gombe,
Ishra’fin sheik yahya bello
Da taimakon dalibinsa Jaafar saad.
ÞÇá Çááå ÊÚÇáì Ýí ßÊÇÈå ÇáÚÒíÒ:
ãõÍóãøóÏñ ÑóÓõæáõ Çááøóåö æóÇáøóÐöíäó ãóÚóåõ ÃóÔöÏøóÇÁõ Úóáóì ÇáúßõÝøóÇÑö ÑõÍóãóÇÁõ Èóíúäóåõãú ÊóÑóÇåõãú ÑõßøóÚðÇ ÓõÌøóÏðÇ íóÈúÊóÛõæäó ÝóÖúáðÇ ãöäó Çááøóåö æóÑöÖúæóÇäðÇ ÓöíãóÇåõãú Ýöí æõÌõæåöåöãú ãöäú ÃóËóÑö ÇáÓøõÌõæÏö Ðóáößó ãóËóáõåõãú Ýöí ÇáÊøóæúÑóÇÉö æóãóËóáõåõãú Ýöí ÇáúÅöäúÌöíáö ßóÒóÑúÚò ÃóÎúÑóÌó ÔóØúÃóåõ ÝóÂÒóÑóåõ ÝóÇÓúÊóÛúáóÙó ÝóÇÓúÊóæóì Úóáóì ÓõæÞöåö íõÚúÌöÈõ ÇáÒøõÑøóÇÚó áöíóÛöíÙó Èöåöãõ ÇáúßõÝøóÇÑó æóÚóÏó Çááøóåõ ÇáøóÐöíäó ÂãóäõæÇ æóÚóãöáõæÇ ÇáÕøóÇáöÍóÇÊö ãöäúåõãú ãóÛúÝöÑóÉð æóÃóÌúÑðÇ ÚóÙöíãðÇ (29)
Allah ta'ala ya ce: Muhammadu manzon Allah ne, kuma wadannan da ke tare da shi ma su tsanani ne akan kafirai, ma su tausayi (rahma ) ne a tsakaninsu( junansu), za ka gan su suna ma su ruku’i ma su sujada suna neman falala daga ubangijinsu da yardarsa,alamarsu ta na a cikin fuskokinsu daga kufan sujada,............... suratul fath.
{æóãóÇ ÃóÑúÓóáúäóÇßó ÅöáøóÇ ÑóÍúãóÉð áöáúÚóÇáóãöíäó (107)} [ÇáÃäÈíÇÁ: 107]
Kuma bamu aikeka ba face dominwata rahma ga talikai.
TA{DIMIN SHEIKH YAHYA BELLO.
ÈÓã Çááå ÇáÑÍãä ÇáÑÍíã æÕáì Çááå Úáì ÇáäÈí ÇáßÑíã æÚáì Âáå æÕÍÈå ÃÌãÚíä
Lalle wannan muzakkira ko littafi ya samu ne a sakamakon daura (seminar) da muka shirya wa
dalibai ta haddar littafin:
ÇáÃÑÌæÒÉ ÇáãÆíÉ Ýí ÐßÑ ÍÇá ÃÔÑÝ ÇáÈÑíÉ áÇÈä ÃÈí ÇáÚÒ ÇáÍäÝí
wanda shi wannan littafin dan uwa Jaafar saad -dalibi a jami'ar musulunci ta Madinah- shi ya taho ma na dashi-Allah ya saka masa da alkhairi-.
Wannan daura an shirya ta ne a makarantar Ma'ahad –da ke gombe-, a cikin watan sha'aban, shekara ta 1432H, bayan an kare dauran sai muka umurci daliban da su rubuto ma na tarihin a cikin rubutun zube –lura da cewa asalin littafin da akai musu dauran akai cikin wake ya ke. Sannan bayan sun rubuta sai dan uwa mal.
Jaafar saad ya tsaya wajen hada littafin da kuma tsara shi, tare da kare-karen abunda ya dace da kuma bijiro da shubuhohin ma su shubuha da bayar da amsoshi gamsassu akansu, tare da warware su- muna fatan Allah ya saka masa da alkhairi.
Lalle wannan littafin ya kunshi mafi girman wurare na tarihin Annabinmu sallallahu alaihi wasallam, muna fatan Allah ya saka wa duk wanda ya bayar da gudun mawa wajen wannan aikin, Allah ya karba mana baki daya ya sanyashi cikin mizanin mu na kyawawan ayyuka.
YAHYA BELLO
5/SHAWWAL/1432H
3/9/2011.
GABATARWA.
Da sunan Allah mai rahama mai jin kai, dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah mahaliccin bayi kuma wanda ya cancanci a bauta masa shi kadai ba
abokin tarayya, wanda ya wajaba a kadaita da roko da bakance da dukkan nau'oin ibadu, wanda ya turo manzonsa muhammad don ya fitar da mutane daga duhu zuwa haske.
Salati da salamin Allah su tabbata bisa shugaba jagoranmu Annabi Muhammad da iyalan gidansa da kuma sahabbansa baki daya.
Bayan haka.
Bayanai akan wannan daura sun riga sun gabata daga kalaman malamina sheikh Yahya Bello, kuma babu wani karin bayani ko ragi , sai dai dalibai da su ka yi kokarin tara wannan Aiki, zan lissafosune tare da jerantawa (ma'ana na daya a wajen kokari shi sunansa zai fara zuwa sannan mai bi masa), na dora tubalin
wannan bincike akan rubutun dalibin da ya zama zakaran gwajin dafi a wannan rubutu mai suna Aminu Abdullahi bala, duk da cewa da dama daga cikin babuka babu su a cikin rubutunsa ni ne na kara su, na kuma yi canje-canje a inda ya dace, tare da kari akan abubuwan da daliban suka rubuta a wajajen da na ga kamatar hakan, sannan kuma na bi littafin da aka gabatar musu da dauran
akansa wajen jera abubuwan da suka faru da kuma shekarunsu, sai dai inda na ga cewa maganar marubucin ita ce mafi rauni sai na dauki maganar wanin sa, kuma na sanya dogarona a cikin wannan rubutu –bayan littafin urjuza- na sanya shi a bisa littafin Arrahikul maktum na Mubarak Fori, da kuma Assiratul Nabawiyyah
fi dhau'i masadiril Asliyyah na Mahdi Rizkullah Ahmad, da kuma littafin hikbatun minattarikh na Usmanul Khamis, tare da dauko dalilaina kai tsaye daga Alkur'ani mai girma da kuma sauran littattafan hadisi da na kafa hujja da hadisansu, kuma ina rubuta lambar hadisi a cikin asalin littafin da na dauko,
kuma na kasance galibin tarjama ina tsayawa akan irin tarjaman da sheik Abubakar gumi ya yi, sai dai idan na ga hausar ta yi tsauri lura da rauninmu a yaren sai na yi amfani da mafi sauki daga gare ta, kuma babban hadafin rubuta wannan littafi shi ne al'umma ta kasance wayayya a game da tarihin Annabin ta domin kada macizai su jirkita mana tarihi kuma mu doru a kai , sai muka tace
muka tankade abun da malamai su ka yarda da shi muka kuma mikoshi ga al'umma cikin halin tsafta saboda a yi koyi da Annabi sallallahu alaihi wasallam a dukkan rayuwa da dabi'u, da al'adu da kuma wayewa.
Sunakan daliban su ne kamar haka:
1-Aminu Abdullahi Bala
2-Muhammad Muhammad Tukur da kuma dan uwansa Umar Muhammad Tukur.
3-Auwal Adam
4-Sa'adatu Muhammad Auwal
5-Fadimatu Shu'aib kadah
6-Aishatu Ibrahim khalil
7-Jamila Abdulhamid
8-Aishatu Abubakar
9-Aishatu Hashim
10-Aminatu Harun Mahmud
11-Asma'u Ibrahim
Wadannan su ne sunakan daliban gwargwadon kokarin su , kuma mu na tunatar da al'umma cewa wannan littafi darasu ne na tarihin mafi wayewa da daukaka acikin mutane, ba shati fadi bane, ba kuma tatsuniya ba, wanda Allah ya yi umurni da ayi koyi da shi ne, saboda haka 'yan uwa idan an karanta wannan littafi ya dace a dau darasin da ke ciki a kuma yi aiki da shi, ina fatan Allah ya karbi
wannan aiki, ya kuma saka wa wadanda suka tsaya wajen tabbatuwan sa, lalle shi mai iko ne akan komai.
Ga emails domin kawo gyara ko wani taimako:
mtoon.d.i.maahad@live.com
binsaad13@yahoo.com
Jaafar Saad
5/SHAWWAL/1432H.
ØÇåÑ ÌÈÑíá Ïßæ
_5 _November _2014åÜ ÇáãæÇÝÞ 5-11-2014ã, 01:55 PM
BABI NA FARKO LARABAWA KAFUN MUSULUNCI.
LARABAWA A FARKON KARNUKA DA SUKA GABACI MUSULUNCI
(HALINSU NA ADDINI , SIYASA , DA KUMA ZAMANTAKEWA)
A farkon zamani sayyiduna Ibrahim da ke asalinsa dan kasar iraki a gari da ake kira (ur) daga bisani ya yi hijra zuwa garin harran, ya dau matarsa da aka sani da Hajara domin kauratar da ita daga kasar Filasdinu zuwa lardin Hijaz a wani jeji da ya kasance bai da wani tsiro ballentana ruwa ko dadin rayuwa, tare da cewa
Umurni ne na ubangijinsa amma duk da haka sai da wannan baiwar Allah ta tambaya amma da ya bayyana mata sai ta yarda da hukuncin maulanta (wannan babban dalili ne akan kasancewar annabawa ba sa aikata wani aiki face sunsan hukuncin Allah a ciki ) . haka kuwa ya barta da danta cikin wannan kungurmin daji bisa umurni na maulansa.
Hajara na zaune da danta a wannan daji har guzuri da ke tare da su ya kare, suka kuma shiga halin kunci , amma dake sun riki Allah a matsayin maula ba su nemi temakon wani koma bayansa ba, na daga salihai ko annabawa, a a sai dai suka nemi agajin Allah shi kadai ba tare da sun hada shi da wani ba ta hanyar roko
ko neman agaji , Allah ya yi gaskiya da yake cewa (wadanda suka yi imani kuma basu gauraya imanin su da zalunci(shirka) ba to wadannan su ke da amnu (tabbataccen aminci) kuma su ne shiryayyu.( Suratul an’ami aya: 82)
Wannan na nuna mana cewa idan mutum ya shiga halin kunci bai halalta ya kira wani koma bayan Allah ba ko da kuwa annabi ne ballentana shehu ko waliyyi, domin kuwa da ya halalta da hajara ta kirayi Annabi Ibrahim, ko kuma ta roki wannan da nata wato Annabi Isma’il, amma ina! ta san haramcin hakan, sai ta
kyautata tauhidi ga Allah tace YA ALLAH, ta kuma ki ta kirayi annabawa biyu tare da cewa daya mijinta ne daya kuma danta.
Allah ya saurari bayinsa tun daga saman al’arshi ya kuma amshi rokonsu, ya agaza musu da ruwan zamzam, ya kuma azurtasu da aminci sakamakon tauhidi da suka tabbatar.
Wata kabilar larabawa da ake kira jurhum suka riski samun ruwa a wannan daji
suka kuma nemi tarewa da izinin Hajara, hakan kuwa akai, sai suka samar da
alkarya mai suna Makkah, . Annabi Isma’il ya girma a wannan gari na Makkah
tare da mahaifiyarsa da kuma larabawan jurhum, anan ne ya koyi larabci ya kuma auri ‘ya daga cikin jurhum sai dai zamansu bai yi tsawo ba, suka rabu ya kuma auran wata daga cikin jurhum , daga wannan mata ce Allah ya azurta shi da ‘ya’ya goma sha biyu (12), daga cikin su akwai kaidar dan Isma’il wanda daga tsatsonsa ne aka samu Adnan shi kuma Adnan shi ne kakan Annabi na ashirin
da daya (21).
Haka nan Annabi Isma’il ya zauna tare da Jurhum, an ruwaito cewa Annabi Ibrahim ya kasance ya na ziyartar su lokaci bayan lokaci amma wadanda littattafai su ka tace su ne ziyaru hudu:
1- Annabi Ibrahim ya yi mafarki cewa ya na yanka dansa Annabi Isma’il, sai ya je Makkah domin ya gabatar da wannan mafarki, kasancewar mafarkin annabawa wahayi ne , daga bisani Allah ya fanshe shi da abun yanka mai girma.
2- zuwan da ya yi ziyara bayan auren annabi Isma’il na fari, har ya bar sallahu kan cewa annabi Isma’il ya canza matarsa.
3- zuwan da ya yi bayan Annabi Isma'il ya canza mata ya kuma bar sallahu cewa ya rike wannan matar (kada ya sake ta).
4- zuwan da yayi suka gina dakin kaabah suna masu cewa “ya Allah ka karba mana lallai kai mai ji ne mai gani” suratul bakarah 127.
kuma Annabi Ibrahim ya yi kira ga hajji Suratul hajj27.
Annabi Isma’il ya shugabanci makkah bisa addinin musulunci tafarkin Annabi Ibrahim , tsawon rayuwarsa sannan ‘ya’yansa biyu sai kuma sarauta ta koma hanun kakansu wato mahaifin babarsu daga jurhum.
Annabi isma’il ya rasu ya na da shekara 137, kamar yadda ya zo cikin Arrahikul maktum na Mubarak Foriy.
MULKI DA SARAUTA A CIKIN LARABAWAN MAKKAH.
Ya gabata cewa Annabi Isma’il ya mulki Makkah iya rayuwarsa sannan ‘ya’yansa biyu sai kuma mulki ya koma wajen Jurhum, duka wadannan mutane sun kasance suna mulkar Makka ne bisa tafarkin Annabi Ibrahim, suna masu tauhidi na gaskiya, kwatankwacin sa kuwa shi ne irin abun da Ahlussunnah a yau
Su ke tafiya a kai; Yau da gobe bayan shudewar karoni sai Jurhum suka jirkice suka fara cin dukiyar mutane da sunan addini (Misali suke cewa sune shuwagabannin daki ba za ka roki Allah ba sai dai ka basu kudi su roka maka,ko kuma su damfari baki da makamantansu).
Hakan ya sa adnaniyyun (jikokin adnan) suka fara inkarin dukkan abun da Jurhum ke yi , har kabilar Khuza’ah ta zo Makkah ta yaki Jurhum ta kuma fitar su zuwa Yaman daga nan mulkin Makkah ya dawo hanun Khuza’ah, haka suma suka ci gaba da mulki bisa adalci a kuma kan tafarkin Annabi Ibrahim , har sai da Amru bin luhayy yazo ya kirkiro shirka, -labarinsa na tafe a bangaren addinai-, haka mulki yaci gaba a Khuza’a tare da shirka, har sai da Qusayy bin kilab ya zo ya kori Khuza’a; daga nan mulki ya dawo hanun kuraysh , har zuwan Annabi (s.a.w) da kuma bayansa.
HALINSU A CIKIN SIYASA:
Hukumar Makkah mutane sun kasance suna mutunta ta
saboda kasancewar ta hukumar Harami, sun yi hukunci a kan hukumomi saboda kasancewar su hukumar Harami, haka kuma azzaluman cikinsu sun yi zaluncinsu da sunan mulkin Harami; sai dai duk da haka ba su da karfin bai wa kan su kariya da jure faman yaki kamar yadda aka gani a yakin giwaye.
ADDINI A GARIN MAKKAH:
Larabawa sun kasance bisa Addinin Annabi Ibrahim tun daga wanzuwar zurriyyarsa a yankin jazirar larabawa, sun kasance suna bautawa Allah Shi kadai, suna kuma kyautata masa tauhidi tare da kudurtar cewa shi Allah mai ji ne mai gani , kuma Ya daidaita a bisa Al’arshinsa daidai ta da ta dace da shi, kuma Al’arshinsa ya na saman ruwa, ruwan kuma na saman sama ta bakwai,
kuma basa sifata Shi da sifar daya daga cikin bayinsa, ko su sifata wani bawanSa da sifarsa, basa kuma hada Shi da wani cikin bauta, kamar roko, neman ceto, bakance, duk wadannan abubuwa basa gabatar da su ga kowa sai Allah. A
takaice dai kamar yadda sunnar Annabi Muhammad sallallahu alaihi wasallam take bisa tauhidi haka wadancan larabawan suka kasance, har sai da zamani ya tsawaita musu suka manta da dama daga abubuwan da aka tunatar da su a kai, amma duk da haka tauhidi ya na nan a a cikinsu da kuma wasu daga cikin
abubuwan addini, haka nan suka wanzu cikin aminci sakamakon tauhidi da suka tabbatar, har sai da shugaban Khuza’a Amru bin lu’hayy alkhuza’iy ya zo mu su da shirka, shi Amru bin luhayy ya kasance daga cikin shuwagabannin Khuza’ah, kuma ya tashi bisa kyawawan dabi’u, da sadaka da kokari a kan harkokin addini, sai mutane suka kusance shi suka kuma karkata zuwa gare shi domin
zaton su shi ya na daga cikin manyan waliyyai, amma kash! sai dai dan wuta ne Annabi sallallahu alaihi wasallam ya ce :” Naga Amru bin luhayy ya na jan hanjinsa a cikin Jahannama” imamul Bukhari(4356) da Muslim(5204) suka ruwaito ( Misali suke cewa sune shuwagabannin daki ba za ka roki Allah ba sai dai ka basu kudi su roka maka,ko kuma su damfari baki da makamantansu)
Amru ya yi tafiya zuwa Sham sai ya ga suna bautan gumaka, sai ya kyautata hakan ya kuma zaci cewa daidai ne domin kasancewar Sham garin manzanni, saboda haka yazo Makkah da gunki mai suna hubal, ya kuma kirayi mutanen
Makkah zuwa ga shirka sai suka amsa masa, bai jima ba sai gaba daya larabawa suka amsa, suka kuma samu wasu gumakan kamar Lata da Uzza da Manata , da kuma Wud da Suwa’a da Yaguth da Yauq da Nasra, kuma duk wadannan kamar yadda ya zo a hadisin Abdullahi bin Abbas (r.a) ya ce wadannan sunakan salihai ne daga mutanen Nuh, lokacin da suka mutu, sai shedan yai wa mutanen su wahayin cewa su zana hotunansu a wuraren zamansu, sai suka aikata haka , da lokaci ya ja sai suka bauta musu. (Wannan babban dalili ne a kan cewa rikar hotunan waliyyai da kuma manna su ,hanya ce zuwa ga bauta musu, kuma yin hakan koyi ne da mushrikan farko , kuma halaka ne).
A takaice fikrar karban shirka ta samu ne a lokacin da su mushrikan suka ga mala'iku da annabawa da manzanni da salihan bayi na daga waliyyai da takiyyai da ma su ayyukan alkhairi- da suka ga cewa wadannan su ne mafi kusancin bayi zuwa ga Allah, kuma su ne mafi daraja da ja’hi a wajensa, sannan kuma Allah Ya gudanar da wasu abubuwa a hannun su na daga muujizozi da kuma karamomi, sai wadannan mushrikan su ka dauka cewa Allah ya basu wata kudura da kuma sarrafa al’amura cikin wasu abubuwa da suka kebantu ga Allah shi kadai, kuma suka raya cewa da wannan tasarrufin na su da kuma ja’hinsu a wajen Allah sun cancanci su zama ‘yan tsakiya tsakanin Allah da bayansa (Sai kaji suna cewa kai baka da tsarkin da zaka roki Allah, ka roki waliyyi sai ya isar maka).
suna ganin cewa bai halalta ga wani ba ya bijirto da bukatunsa ga Allah ba face ya kama kafar
wadannan, domin su za su ceceshi a wajen Allah, haka kuma ba za a bauta wa Allah ba sai an bi ta kafar wadannan, domin su wadannan da kusancinsu ga Allah za su kusantar da su zuwa ga Allah, a lokacin da wannan zato ya kama zukatansu kuma wannan akida ta tabbata a cikinsu sai suka rike su majibinta suka kuma sanya su tsani tsakaninsu da Allah Taala, suka kuma ta neman kusanci gare su da dukkan abun da su ke gani cewa sababi ne na kusanci, sai suka kirkiri hotunansu da mutum mutuminsu, imma dai ya zama dai dai da hotunansu ko kuma su raya cewa ga yadda suke sai su zana su ce wannan shi ne wane, wadannan hotunan kuma da mutum-mutumin su ake kira Asnam, wasu kuma ba za su yi hotonsu ba sai dai su sanya kaburburansu da kubbobinsu da wajajen hutunsu su sanya su su zama wajajen girmamawa, su gina masallatai a kai, suna kawo musu abubuwan neman kusanci kamar bakance da neman agaji, su kuma zo musu da kaskan da kai da biyayya irin wacce ba ta dace ga wani ba sai Allah, wadannan wurare su ake kira Ausan, duka kuma sun taru a hausance a karkashin sunan gumaka.
Amma bautan su ga wadannan asnam da ausan (gumaka) sun kasance da damansu Amru bin luhayy ne ya kirkirosu, kuma suna cewa wadannan abubuwa da ya kirkiro ba canji ba ne ga tafarkin Annabi Ibrahim (A.S), a a! suka ce bidi’ah hasana ne sunan ta.
Daga cikin irin bauta da suke gabatarwa ga wa]annan asnam da ausan:
1- suna tarewa a wajensu su kuma karkata izuwa gare su, suna kiran sunayensu , suna neman temakonsu yayin tsanani8, suna rokonsu domin biyan bukatunsu, suna kudurtar cewa wadannan kaburbura da hotuna za su cece su a wajen Allah, kuma za su iya biya mu su bukatunsu.
2- suna hajji a wadannan wurare, suna kaskantar da kai gare su, suna kuma sujada a gare su.
3- suna kawo kusanci ga wadannan kamar irin yanka bakance da sauran su da sunan sadaka, kamar kuma yadda suke yanka da sunayen su.
4- Na daga cikin kusanci da suke gabatarwa, suna ware wani daga cikin abincinsu da abun shansu ga wadannan asnam.
5- na daga ciki cewa suna bakance a cikin noman su da makamantan su.
Wannan shi ne sifofi daga cikin sifofin mushrikai da shirkarsu, sai dai abun mamaki a nan shi ne za ka samu wani da ya ke jingina kansa ga musulunci a yau ya sifatu da wadannan abubuwa daya bayan daya, to mu fa sani cewa duk wanda ya sifatu da su a daya daga cikin shirkarsu to hakika shi ma irin su ne, ko da kuwa
yana ganin cewa shi musulmi ne domin Annabi sallallahu alaihi wasallam yace : “duk wanda yai kamanceceniya da wasu mutane to yana tare da su”(musannaf na ibn Abi shaibah 33016). Kuma mun gani cewa wuce gona da iri cikin salihai da waliyyai da kuma annabawa shi ya sa suka zama mushrikai, kuma jininsu ya
halalta, ashe kenan muma idan muka aikata haka za mu zam irin su.Sannan kuma rikar hotunan waliyyai da salihai da tabarruki da shi shi ya kai su ga shirka kamar yadda ya gabata a hadisin Abdullahi dan Abbas (R.A). Saboda haka muyi iya kokarin mu mu guji shirka da son zuciya, Imam malik (R.H) ya ke cewa “ duk wanda ya kirkiri wata bidi’a a musulunci wacce ya ke ganin ta
hasana (mai kyau) to hakika ya raya cewa Annabi Muhammad ya ci amanar sako.
ØÇåÑ ÌÈÑíá Ïßæ
_6 _November _2014åÜ ÇáãæÇÝÞ 6-11-2014ã, 06:46 AM
Zamantakewa: sunan zamanin wato jahiliyya ya isa ya fitar maka da hoton zamantakewar zamanin, sun kasance mutum daya zai iya auran mata bila adadin, haka kuma saki ba shi da haddi idan namiji na so zai iya sakan mata har sai ta kusa gama idda ya dawo da ita kuma ya kara sakan ta , zai ta haka har ta mutu, wani kuma na iya hada ya da kanwa ko ‘ya da goggonta, da makamantan su,. ta bangaren ‘ya’ya kuma, da daman su suna bunne ‘ya’ya mata
da ransu, domin tsoran talauci, ko tsoran abun kunya, su kuma mata abun ga'da ne basa ga'do, idan mahaifin mutum ya mutu sai ya ga'je matar mahaifin.
Zinace-zinace ya yawaita musamman ma a bangaren bayi, su kam bai zama abun aibi ba a gare su. Kasuwanci ne hanya mafi girma daga hanyoyin arzikin mutanen Makkah, haka kuma yake-yaken bangaranci da asabiyya sun bazu a cikin larabawa.
Duk da cewa mutan jahiliyya suna da wadannan munanan halaye wadanda kare ma ba zai ci ba, amma kuma a gefe guda suna da halaye na kwarai wadanda kowa zai ji sha’awa ya kuma sha mamaki daga cikin su akwai:
1-karamci : sun kasance mutane masu karamci, daga misalin karamcinsu cewa mutum zai yi bako a rana mai sanyi bai da abun da zai ciyar shi sai rakuminsa da ya kasance shi ne rayuwarsa da rayuwar iyalansa amma zai kama ya soke wa wannan bako don ya karrama shi.
2- Cika alkawari: su kan iya rasa ‘ya’yansu da gidajensu a kan cika alkawari, kamar yadda ya zo a kissar Hani’i bin Mas’ud Asshaibani.
3- Karfin hali da kuma kin yarda da reni ko kaskanci, na daga cikin wannan cewa ba sa yarda su ji wata kalma da ke dauke da reni face sun nufi takubba.
4-Juriya da dogewa a kan abu komai wahalar sa.
5-Hakuri da tausayi.
6-Jarumta da rashin tsoro.
7-Sifatuwa da sifofin kauye, da kuma rashin cakuduwa da halayyar birni, na daga cikin sakamakon hakan su ka zama ma su gaskiya da amana su ka kuma rabu da yaudara da cin amana.
Wadannan wasu daga sifofinsu ke nan kyawawa, ba wai don sun kare ba. Abun lura a nan shi ne Makkah da halin da ta ke da shi na yanayi amma Allah ya zabeta don ta zama mabubbugar wahayi, ya kuma zabi wadannan mutane a matsayin ma su Isar da wannan sako ashe akwai hikima, kuma idan mu ka lura da wadannan sifofi na su tun ajahiliyya sifofi ne da su ka karanta a wajen da dama
daga musulmai a yau, kuma Allah ya zabe su ya turo Annabi ya tace munana daga halayensu , suka zama mafi alkhairin mutane, lallai wanda ya duka kansa ya zagi sahabban manzon Allah bayan wannan tsarkake wa da Allah ya mu su
tsarkake wa na musamman to hakika wannan ko jakin gidan su bai kai shi bata ba, domin kuwa ya na fada da falalar Allah ta'ala ne da ya yi a gare su.
Wannan kadan ke nan daga halayen jahiliyya kuma da sannu za mu ga yadda Allah ya turo Annabi ya tsaftace munana daga cikin su ya kuma tabbatar da ma su kyau, wanda da hakan ya zama sahabbai su ne ma fi alkhairin mutane, me zagin su kuwa shi ne mafi sharrin mutane.
Annabi muhammad sallallahu alaihi wasallam, da, mahaifi, miji, aboki, dan uwa, shugaba, jagora, annabi, manzo.
Allah ta’ala yayi gaskiya da ya ke cewa: “Lalle abun koyi mai kyau ya kasance gare ku daga manzon Allah...( Suratul Ahzab21) duba arrahi}ul maktum na mubarak fori.
ØÇåÑ ÌÈÑíá Ïßæ
_14 _November _2014åÜ ÇáãæÇÝÞ 14-11-2014ã, 12:40 AM
BABI NA BIYU
ANNABI SALLALLAHU ALAIHI WASALLAM DAGA HAIHUWA ZUWA ANNABTA.
ANNABI SALLALLAHU ALAIHI WA SALLAM KAFIN MUSULUNCI.
Nasabarsa : shi ne Abul Kasim, Muhammad, dan Abdullahi, dan
Abdulmuddalib(sunansa shaibah) (A wannan kakan ya hadu da sayyiduna Aliyu.), dan Hashim (sunansa Amru), dan Abdu manaf (sunansa mugirah)(a wannan kakan ya hadu da sayyiduna usman zun nurayn) , dan kusayy (sunansa zaid), dan Kilab( a wannan kakan mahaifinsa ya hadu da mahaifiyarsa ) dan murrah(a wannan kakan ya hadu da sayyidu na Abubakar assiddiq) , dan ka’ab(a wannan kakan suka hadu da sayyiduna umar alfaruq), dan lu’ayy, dan Galib, dan Fihr (shi ake wa lakabi da kuraysh) dan malik dan Annadhr (sunansa kais), dan kinanah, dan khuzaimah, dan Mudrikah, (sunansa A’mir), dan Ilyas(a wannan kakanne sheik muhammad bin Abdulwahab ya hadu da manzon Allah sallallahu alaihi wasallam), dan Mudhar, dan Nizar, dan Ma’add, dan Adnan. (Bidaya wannihaya na ibn kathir shafi 2/355-357, sirah na mahdi 105. arrahi} 36-37.) Amma nasabarsa daga kan Adnan zuwa Isma’il an yi sabani wajen jero ta , wajen magana talatin, sai dai wacce ta fi kusanci da inganci shi ne a tsakanin Adnan da annabi Ibrahim (A.S) kakanni arba’in (40) ne.
Daga Annabi Ibrahim zuwa annabi Adam kuwa ma fi yawancin riwayun daga isra’iliyyat suke, amma an ce kakanni ashirin (20) ne a tsakanin su. (Manzon Allah sallallahu alaihi wasallam nada sunaye da dama , daga cikin wadanda suka inganta akwai:
muhammad , Ahmad, Almahiy , Al’a}ibu, Alhashiru, Almu}affiy, nabiyyu rrahmati, nabiyyu ttaubati, Alfatihu.Kamar yadda yazo a littafin bidaya wannihaya na hafiz ibn kasir.) Don karin bayani ka duba littafin Arrahikil maktum na sheik mubarak foriy.
Mahaifiyarsa ita ce Aminatu ‘yar wahb, dan Abdumanaf dan zuhrata dan kilab.
Nasabar Manzon Allah sallallahu alaihi wasallam ita ce mafificiyar nasaba, kuma shi ne ya zama mafificin halitta nasaba da alfahari. Kamar yadda ya ke
cewa:
«Åä Çááå ÇÕØÝì ßäÇäÉ ãä æáÏ ÅÓãÇÚíá¡ æÇÕØÝì ÞÑíÔÇ ãä ßäÇäÉ¡ æÇÕØÝì ãä ÞÑíÔ Èäí åÇÔã¡ æÇÕØÝÇäí ãä Èäí åÇÔã»
Ma'ana : Allah ya zabi kinanata daga ‘ya’yan isma’il, ya zabi kuraysh daga ‘ya’yan kinanata, ya zabi hashim daga kuraysh ya zabeni daga cikin ‘ya’yan hashim (ibn hibban ya ruwaitoshi-zai zo a gaba).
Yayin da hiraklu shugaban rum ya tambayi Abu Sufyan (r.a) a kan nasabarsa sai
Ya ce lallai shi a cikin mu ma abocin kyakkyawar nasaba ne, sai hiraklu ya ce haka annabawa su ke, ana aika ma fi nasaba ne. Bukhari (7) da muslim (3409) suka ruwaito daga hadisin dan Abbas.
Haihuwar sa: An haifi manzon Allah sallallahu alaihi wasallam ranar Litinin, takwas ga watan rabi’ul Auwal, dai- dai lokacin ketowar alfijir, kwana hamsin bayan yakin giwaye, wanda ya ke dai- dai da 20 ga april shekarar miladiyya 571.
An tabka sabani akan kwanan watan da aka haifi Annabi , wasu suka ce biyu ga rabi’ul auwal, wasu suka ce takwas ga wata, wasu suka ce goma, wasu suka ce sha biyu wannan na sha biyun shi yafi shahara a wajen mutane , sai dai shahara bata kawo karko, maganar takwas ta fi karfi ta fuskar isnadi, imam ibn kasir yace:
æÇáÕÍíÍ Úä ÇÈä ÍÒã ÇáÃæá Ãäå áËãÇä ãÖíä ãäå ßãÇ äÞáå Úäå ÇáÍãíÏí æåæ ÃËÈÊ.
Maana “mafi inganci daga ibn hazm shi ne na farkon , wato cewa takwas ga watan , kamar yadda humaidi ya nakalto daga gare shi, kuma shi ne ya fi tabbata”.(ibn kasir, albidaya wannihaya).
Shi kuma Imam muhammad nasiruddeen Al’albani ya ce:
æåÐå ÇáÃÞæÇá ãÚáÞÉ ÈÏæä ÃÓÇäíÏ¡ÅáÇ Þæá ãä ÞÇá Åäå æáÏ Ýí ÇáËÇãä ãä ÑÈíÚ ÇáÃæá¡ ÝÅäå ÑæÇå ãÇáß æÛíÑå ÈÇáÓäÏ ÇáÕÍíÍ Úä ãÍãÏ Èä ÌÈíÑ Èä ãØÚã-æåæ ÊÇÈÚí Ìáíá-æáÚáå áÐáß ÕÍÍ åÐÇ ÇáÞæá ÃÕÍÇÈ ÇáÊÇÑíÎ.
Ma'ana : dukkanin maganganun nan mu’allakai ne ba su da isnadi, sai ta wanda ya ce an haife shi a takwas ga watan rabi’ul auwal, domin Malik da wanin sa sun ruwaito shi da isnadi ingantacce daga muhammad dan jubair dan mud’im tabi’iy ne mai daraja-ta yiwu da wannan ne ma abota tarihi suka inganta wannan maganar.
Abin lura anan shi ne kasancewar ranar haihuwar Annabi ba bu wani hukunci na shari’ah da ke rataye da wannan rana shi ya sa sabani ya yawaita akan wannan rana , kuma magabatan al’umma sun yi ijma’i a kan kasancewar ranar haihuwar Annabi babu wani hukunci na addini da ke da alaka da ita, ba a fara samun bidi’a ba sai bayan kafuwar daular fadimiyya a karni na hudu, su suka fara
kirkirar bidi’ar mauludi, suka kuma sanya lada ga wanda ya yi ko laifi akan wanda ya ki yi, ijma’in magabata daliline a kan kasancewar wannan aiki bidi’a, domin kuwa ijma’i daya ne daga cikin tussa da ake gina hukuncin shari’ah akai, ya wajaba a kan musulmi ya ke tsayuwa a inda aka tsayar da shi ka da ya kirkiri
wani abu bayan babu shi a lokacin magabata na kwarai, an tamabayi manzon Allah sallallahu alaihi wasallam a kan azumin da ya ke ranar litinin sai ya ce: "wannan rana ce da aka haife ni, kuma a kai mun wahayi, aka kuma aiko ni a ciki, kaga ko azumin ma bai rataya shi da haihuwar sa ba domin kuwa ya ce ranar da
aka yi mun wahayi kuma aka aiko ni a cikinsa, kuma ba wanda yasan me Annabi ya ke wa azumin , ta yiwu wahayin ne ko manzancin ko kuma duka, amma kebe daya a kudur ta cewa akan sa ne ba dai dai ba ne, idan ma mun dauka cewa haihuwar ya ke wa, to mu ma wajibi a kan mu shi ne mu tsaya a kan azumin ka da
mu yi kari a addinin Allah, shi ya sa Imamul akhdhari ya ke cewa, a cikin littafin ahlari:
æíÞÝ ÚäÏ ÃãÑå æäåíå
Wato mutum ya tsaya a inda Allah da manzonsa suka umurce shi ya tsaya, kuma ka da ya gota haninsu.
SHEKARAR GIWAYE A shekara ta 525 miladiyya ne rundunar mutum dubu saba’in daga habasha su ka sauka a yaman, su ka mamaye ta, da jagorancin aryad, aryad ya mulki yaman lokaci mai tsawo karkashin sarkin habasha har sai da daya daga cikin komandodinsa ya kashe shi wanda ake kira Abrahata bin sabah al’ashram, a shekara ta 549 m, sai ya mayar da kansa sarkin yaman, bayan ya yardar da sarkin habasha, wannan Abrahatan shi ne ya ci gaba da kira zuwa kiristanci a yaman har ta kai shi ga gina ka’abah a yaman domin ya kawar da mahajjata daga zuwa Makkah, sai wani mutum daga cikin banu kinanata ya ji labarin ka’abar Abrahata sai ya je cikin dare ya shafe fuskarta da kashi, yayin da Abrahata ya san da wannan abu sai ya cika da fushi , ya fita daga yaman da rundunar mutum dubu sittin, zuwa makkah domin rushe dakin ka’abah, ya zabawa kansa ma fi girma daga cikin giwayen da ke tare da rundunar, a tare da rundunar kuwa akwai giwaye tara ko sha uku; ya ci gaba da tafiya har sai da ya kai wani waje da ake kira mugammas anan ne ya shirya rundunarsa , da giwayensa, ya kuma shirya shiga Makkah, a yayin da ya iso wadi muhassar da ke tsakanin Mina da
Muzdalifah sai giwayen su ka tirje, suka ki nufan Ka’abah, sai ya zama duk lokacin da suka nufi wani gefe da ba na Ka’abah ba sai su tafi daga kuma sun nufi ka’abah sai su turje, suna cikin haka sai Allah ya aiko musu da tsuntsaye dake dauke da dutsen wuta guda a bakin su da kuma guda a kowace kafa (uku kenan kowane tsuntsu ke dauka), sai su ka ci gaba da jifansu suka kuma koma
kamar wani karmami da wuta ta cinye, kuma ba kowanne daga cikinsu duwatsun suka samu ba , sai suka ta gudu sashensu na faduwa sashe na takewa , da haka suka halaka, shi kuma Abrahata Allah ya aika masa da wata cuta ta zubar masa ‘yan yatsu, sai ya isa yaman fata-fata, sannan zuciyar shi ta halaka
sai ya mutu.
Su kuma kuraish sun hau duwatsu da makamantansu domin tsira, yayin da wannan abu ya sauka a kan ma’abota giwaye sai suka koma gidajensu cikin aminci.
Shekarar da wannan abu ya faru ita ake cewa shekarar giwaye. Duba Arrahik.
ØÇåÑ ÌÈÑíá Ïßæ
_23 _November _2014åÜ ÇáãæÇÝÞ 23-11-2014ã, 12:13 AM
RENON MANZON ALLAH SALLALLAHU ALAIHI WASALLAM.
Daga farko bayan haihuwar manzon Allah sallallahu alaihi wasallam, maularsa Ummu Ayman ta kasance ta na lura da renon sa.
Tare da mahaifiyarsa kuwa Suwaibatul Aslamiyyah ce ta dauki dawainiyar shayar shi, na wasu kwanaki, ita Suwaibah baiwa ce ga Abu lahb sai ya ‘yanta ta ta kuma shayar da manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam, sannan Halimatu bint Abi zu’aib assa’adiyyah ta karbi renon sa, sunan mijinta kuma Alharis bin Abd uzza bin Rifa’ah, ‘yan uwansa kuma wajen reno su ne Abdullahi bin Alharis, Unaisatu bint Alharis, Huzafatu bin Alharis, kisser Halimatu kuwa ga ta kamar haka:
Ibn Ishak ya kawo cewa Abdullahi bin jaafar ya ce, an labarta min cewa Halimatu Assa’adiyyah ta ce: Na zo makkah cikin wasu mata - wakidi ya ce su goma ne- daga bani saad bin bakrin muna neman shayarwa, kuma cikin busassar shekara, sai na zo akan jakata busassa, da ni da dan dana, da kuma rakumin mu, wallahi ba ta da ko digon nono, wannan daren duka ba na bacci haka danmu ma, babu wadataccen nono a jikina da zai iya kosar shi, haka kuma babu a jikin rakumarmu, sai dai kawai muna neman agaji, sai muka iso Makkah, wallahi ban san wata mata ba daga cikinmu face an bijiro mata da Manzon Allah, sai ta ki karba, saboda an ce maraya ne, mu ka ce mai mahaifiyarsa za ta iya mana? Dama ana neman alkhairi ne da ga mahaifi, babu wata daga cikinmu face ta samu wanda za ta shayar sai ni, a lokacin da muka tashi tafiya sai nacewa mijina Alharis bin abd uzza, ni fa zan karbi marayan nan domin ina kin komawa haka, sai ya ce ki karbe shi, da sannu Allah zai sa mana Albarka a ciki, sai na karbe shi,
wallahi na karbe sa ne kawai don ban sami wani ba, ina karbo sa sai nonona ya cika, ya sha ya koshi, dan uwansa (dan Halimatu ssa'diyya) shi ma ya sha ya koshi, mijina ya je ga rakumar mu sai ya ga ta cika da nono, ya tatsa ya sha ni ma na sha mu ka koshi mu ka yi barci mai dadi a wannan dare, sai mijna ya ce lalle ina ga yau kam Halima kin dauko rabo mai albarka, da muka tashi tafiya jakata din nan ta samu lafiya har ta zama tana wuce sauran jakuna, har muka iso bani sa'ad.
Kuma ban san wata kasa da ta kai kasar bani sa'ad fari ba, amma idan dabbobina suka fita sai su dawo a koshe, har ta kai sauran mutane sukan ce wa mai musu kiwo ka je ta inda na Halima su ke kiwo , sai ya je amma nawa su koshi na su kuma su dawo da yunwa, wallahi Allah bai gushe ba ya na nuna mana albarkarsa har sai da yakai shekara biyu, kuma ya kasance ya na wani irin girma da ya sabawa na sauran yara, bai kai shekara biyu ba face ya zama yaro kosasshe lafiyayye, sai muka mayar da shi wajen iyayensa, amma muka nemi komawa da shi, da kyar mahaifiyarsa ta bar mu........ ١٨
TSAGA KIRJINSA DOMIN CIRE RABON SHAIDAN.
A lokacin da manzon Allah sallallahu alaihi wasallam ya kai shekara biyu da wata biyu, sai mala’iku biyu suka zo suka kwantar da shi suka bude kirjinsa suka yanka zuciyarsa suka fitar da wani abu suka kuma ce wannan shi ne rabon shedan daga jikinka, suka kuma wanke zuciyar suka cika ta da imani da hikima suka mayar suka dinke, wasu sun ce wannan ya kasance ne lokacin da ya ke dan shekara hudu , amma daga maganar Halimatu za mu fahimci cewa shekara biyun shi ne dai dai, ta ce:
Sai ta yarda muka koma tare, sai muka zauna da shi wata biyu ko uku, wani lokaci ya na tare da dan uwansa na shayarwa a bayan gidanmu wajen dabbobinmu sai yaron ya zo ya na sauri ya ce ai dan uwana ba kuraishen nan wasu mutane biyu ma su fararen kaya sun zo sun kwantar da shi sun farka cikinsa, sai mu ka fito ni da babansa (ma'ana mijinta) mu na sauri sai ga shi ya taso fuskarsa ta kara haske, sai babansa ya rungume sa ya ce da shi meye labarinka ya dan dana? Sai ya ce “wasu mutane biyu sun zo sun kwantar da ni sun cire wani abu a zuciyata sun yar, sannan suka mayar da ita kamar yadda ta kasance, sai muka dauke shi mu ka koma gida, sai mijina ya ce Halima mu mayar da wannan
yaro wurin iyayensa, saboda haka mu ka koma Makkah da shi wurin mahaifiyarsa, sai mu ka ce da mahaifiyarsa ga shi nan mun sauke nauyin da ke kanmu, sai ta ce a a ku gaya min gaskiya , ba ta gushe ba ta na tambayar mu har sai da mu ka bayyana ma ta abun da ya faru, sai ta ce “shin kun ji masa tsoran shaidan ne, a a wallahi shaidan bai isa ya cutar da shi ba, wallahi sai wani sha'ani
ya faru ga wannan da nawa, shin bazan ba ku labarinsa ba? Sai mu ka ce ki bamu, sai ta ce “na dau cikinsa ban taba daukan wani abun dauka da ya ke ba nauyi ba irin sa, sai na ga ni a mafarki bayan na dau cikinsa haske ya fito daga gare ni ya haskake gidajen Sham, sannan a lokacin da na haife shi sai yai wani irin sauka wadda babu wani yaro da yayi irin wannan sauka, ya sauka ya na mai dogara akan hanunsa, ya na mai daga kansa zuwa sama, saboda haka ku rabu da sha’aninkun nan (Al bidayah 2/409-412). Wannan hadisin an ruwaito shi ta wasu hanyoyi ba wannan da ya gabata ba , kuma na daga cikin hadisai mash’hurai ma su zagayawa tsakanin malaman tarihi da sirah.
Malaman tarihi suka ce wannan tsaga kirji na Annabi ya faru ba sau daya ba, na farko dai shi ne wannan da ya gabata; wanda wasu suka ce ya na da shekara biyu da wata biyu, wasu kuma suka ce ya na da shekara hudu, hikima a nan shi ne an yi masa wannan tsarkaka domin a tsare shi daga sharrin shaidan a halin yarinta, sai kuma na biyu lokacin da ya ke da shekara goma.
An karbo daga Anas ban malik (R.A) ya ce: lallai Manzon Allah sallallahu alaihi wasallam jibril ya zo masa yayin da ya ke wasa da yara sai ya kama shi ya kwantar shi ya fitar da zuciyar sa ya tsaga ta ya cire wani gudan jini, sai ya ce wannan shi ne rabon shaidan daga gare ka, sai ya wanke ta a wani kasko na zinariya da ruwan zamzam, sannan ya mayar shi ya dinke shi...imamu muslim (262) ya ruwaito shi, hikima a nan shi ne a tsare shi lokacin balaga daga sharrin shaidan. sai na uku lokacin da za a annabtar da shi; An karbo daga Abu zarr (R.A) ya ce “ na ce ya manzon Allah yaushe ka san cewa kai annabi ne a lokacin da kasani, sannan ka samu yakini cewa kai annabi ne? Sai ya ce “wasu mala’iku biyu sun zo min a halin ina wani kwararo a garin Makkah sai dayan su ya sauko kasa dayan kuma ya na tsakanin sama da kasa sai dayan su ya ce shi ne? Sai dayan ya ce shi ne, sai ya ce gwada shi
da mutum daya sai na rinjaye shi –a wata riwaya ya ce gwada shi da dubu sai na rinjaye su, sai ya ce da za a gwada shi da al’ummar sa kaf da ya rinjaye su, -sai su ka bude zuciyata suka wanke su ka mayar suka dinke sannan suka sanya khatamin annabta –ya ce “sai su ka juya suka bar ni sai ya zama kamar ina ganin al’amura a fili, ibin asakir ne ya ruwaito shi (cikin tarikh 2/462), hikima a nan shi ne a shiryasa domin iya daukan nauyin annabta, sai kuma na hudu a lokacin isra’i da mi’iraji; An karbo daga Anas (R.A) da kuma malik dan sa’ sa’ata(R.A) cikin hadisin isra’i ya ce Manzon Allah sallallahu alaihi wasallam ya ce “ ina wajen daki tsakanin mai barci da maras barci – a lafazin anas ya ce sai aka ce ku kama shugabansu kuma ma fi alkhairinsu- sai aka zo da wani kasko a cike da hikmah da imani sai aka yanka daga kirji zuwa marabar ciki sai aka wanke cikin da ruwan zamzam sannan aka cika shi da hikma da imani. Imam bukhari(3050) da imam muslim(264) suka ruwaito shi, hikima a nan shi ne a shirya shi domin ganawa da ubangijinsa subhanahu wa ta’ala.
Anas bin malik (R.A) ya ce “na kasance ina ganin alamar wannan dinkin a kirjinsa.
RASUWAR MAHAIFIYARSA:
A lokacin da ya kai shekara shida sai mahaifiyarsa ta tafi da shi zuwa garin Madinah (a lokacin ana kiran ta da suna yasriba, sai da Annabi ya yi hijra zuwa gare ta ya canza mata suna zuwa Madinah, ya kuma hana a kira ta da yasriba) domin ya ziyarci kawunan sa tare da ummu ayman, a yayin da ta ke dawo wa sai
ajali ya zo mata a wani gari da ake kira Abwa’i tsakanin makkah da Madinah, aka kuma binne ta can, sai Ummu aiman ta dawo da shi Makkah.
Abin lura: Mahaifinsa ya rasu tun ya na ciki bisa magana ma fi inganci.
RENONSA BAYAN RASUWAR MAHAIFIYARSA.
Da mahaifiyarsa ta rasu sai renon sa ya koma wajen kakansa Abulmuddalib, ya kuma ci gaba da renonsa bisa kauna da kiyaye wa har ya kai shekara takwas,
Ya yin da ya kai shekara takwas sai Allah ya karbi rayuwar kakan.
KIWON DABBOBINSA DA KUMA TAFIYARSA ZUWA SHAM NA FARKO
Kafun rasuwar kakansa sai ya bawa baffansa Abu dalib wasiyyar kiyaye shi , saboda soyayyar da ya ga ya na nuna masa, sannan kuma shi ne dan uwa shakiki ga mahaifinsa, daga rasuwar sa sai renonsa ya koma hanun baffansa Abu dalib. Hakanan manzon Allah yaci gaba da rayuwa cikin jin dadi da kamala da yalwa
karkashin luran baffansa Abu dalib, kuma ya kasance yana mai kiwo ga mutanen makkah domin su bashi kudi. Yayin da ya kai shekara sha biyu sai baffansa ya tayar da tafiya zuwa Sham, kuma ya himmatu akan tafiya da Annabi, haka kuwa aka yi, a cikin garin Busra da ke Sham ne su ka ci karo da wani fadan kiristoci da ake kira bahira , shi kuma ya ga ayoyi a tattare da manzon mu, kamar ganin girgije da ke masa inuwa , haka kuma da kuraysh su ka zauna sai suka tare inuwa saboda haka Annabin mu ya zauna a rana amma sai bishiyar ta karkata ta bashi inuwa, kuma dubawa da ya yi sai ya ga khatamin nan na annabta, saboda haka ya sauki ayarin kuraysh da abinci mai kyau, ya kuma bai wa Abu dalib shawarin ya mayar da Annabi Makkah domin ka da yahudawa su cutar da shi. Imam Attirmizi ya rawaito wannan kissar a cikin sunan (3620) ya kuma ce wannan hadisi ne Hassan garibi, ba mu san shi ba face ta wannan fuskar. Sheikh Albani ya ce sahihi ne sai dai ambaton bilal a cikin sa munkari ne.
TAFIYARSA TA BIYU ZUWA SHAM.
Yayin da ya kai shekara ashirin da biyar sai Nana Khadija ta ji labarin amincin sa da kuma kyawawan dabi’unsa saboda haka ta bukaci ya zo su yi kasuwanci, ya zama kudi na ta, aiki kuma na shi sai su ke raba riibar da aka samu, sai Manzon Allah ya yarda ya kuma tafi Sham domin wannan kasuwanci , tare da shi kuma akwai yaron Khadija da ake kira Maisarata, haka ya fita da maisarata cikin wannan tafiya Allah kuma ya ci gaba da nuna wa maisarata ayoyi da ke nuna cewa wannan mutumin da sannu zai zama mai babban sha’ani. Manzon Allah sallallahu alaihi wasallam ya dawo tare da maisarata suna masu cin riiba ta gaske, kuma maisarata ya labarta wa Nana Khadija abun da ya gani na falalar
Annabi a wannan tafiya.
ØÇåÑ ÌÈÑíá Ïßæ
_12 _February _2015åÜ ÇáãæÇÝÞ 12-02-2015ã, 12:52 AM
AURENSA DA NANA KHADIJA.
Bayan dawowarsa daga habasha sai nana khadija ta aika masa ta na mai neman ya aure ta, ya kuma amsa ma ta akan zai aure ta, ita ko khadija ta kasance mace mai himma , mai daraja, mai hankali, Imam ibn kasir ya ce “sai ta bijiro da kanta gare shi, kuma ta kasance daga cikin mafi kyan nasaba a cikin matan kuraish,
kuma mafi girman su wajen daraja, mafi yawansu dukiya, kowa daga cikin mutanenta na burin ya same ta da zai samu, a lokacin da ta ambata wa Annabi hakan sai ya fadawa baffaninsa, sai baffansa Hamzah ya fita tare da shi, har sai da ya shiga kan khuwailid bin Asad, sai ya nema masa ita a wajensa, sai Annabi ya aure ta sallallahu alaihi wasallam. (Albidaya wannihayah). Ibin hisham ya ce “sai ya ba ta sadakin saffan rakumi ashirin, kuma bai auri wata mace ba har ta rasu. Annabi sallallahu alaihi wasallam ya auri Khadijatu ya na dan shekara ashirin da biyar, wasu su ka ce bayan dawowarsa daga sham da wata biyu, ita kuma ta na da
shekara arba’in a ra’ayin wasu, wasu kuma su ka ce shekaranta ashirin da biyar, wasu su ka ce talatin da biyar, imamul baihaki ya nakalto daga Imamul hakim cewa shekarunta talatin da biyar ne. Almusili ya ce “abun gaskiya da aka hadu akai shi ne cewa baffanta Amr bin Asad shi ne ya aurar da ita ga Annabi sallallahu alaihi wasallam. Kafin ta auri Annabi ta yi aure da wani mutum da ake kira Atik bin A’iz almakhzumiy ta haifa masa ‘ya, sannan ta auri Abu halata, suka samu da daya da kuma ‘ya shi ma ya rasu a jahiliyyah, kuma ta zauna da Annabi shekara ashirin da biyar, ta rasu ta na da shekara hamsin , wasu kuma sukace sittin da
biyar,. Imam Ibn kasir ya ce “Khadija takai shekara sittin da biyar, wasu kuma su ka ce hamsin kuma shi ne ya fi inganci.(bidayah wannihayah ). Na daga cikin falalarta cewa ita ce farkon matar Annabi sallallahu alaihi wasallam , kuma ita ce uwar ‘ya’yansa, sannan bai auri wata mace ba har sai da ta rasu, kuma ita ce farkon musulunta a cikin mata. An karbo daga Aliyu (r.a) ya ce : Annabi sallallahu alaihi wasallam ya ce “mafi alkhairi daga cikin mata ita ce khadija” bukhari(3265) da muslim(4562). Ankarbo daga Abu hurairata (r.a) ya ce “Jibril ya zo wa Annabi sallallahu alaihi wasallam sai ya ce da shi ga khadija ta na zuwa da kokon abinci, ka isar ma ta
sallama daga ubangijinta da kuma ni, sannan ka ma ta albishir da wani gida na zinariya a aljannah, wanda babu hayaniya a ciki, ko gajiya. Bukhari (3632) da muslim(4564).
ALLAH YA TSARKAKESHI DAGA DATTIN JAHILIYYAH.
Ibn Ishak ya ce “sai manzon Allah ya girma, Allah ya na kiyaye shi ya na tsare shi daga dattin jahiliyya da aibobinta domin abun da ya ke nufi na karrama shi da aika shi, kuma ya na kan addinin mutanensa (maana ya na kan tafarkin Annabi Ibrahim, bai taba shirka ba), har sai da ya kai shi ne mafi mutuncin mutanensa ,
mafi kyan halinsu, mafi karamcin su wajen cudanya, mafi kyan makwabtansu, mafi girmansu ga hali, mafi gaskiyarsu ga zance, mafi girman su ga amana, mafi nisa ga alfasha da abubuwa masu kaskantar da mutum, don tsarkaka da daukaka, har sai da ya zama bai da wani suna a cikin mutanansa face ‘AMINTACCE’ domin abun da Allah ya tara masa na kirki. An samo cewa Annabi ya ce “ na fito ta hanyar aure ba shashanci ba”(musannaf
abdirrazzak 12845). A shekara ta talatin da biyar da haihuwar Annabi sai kuraysh su ka sake ginin ka’aba shi ma Annabi ya halarta, da su ka iso wajen dora hajarul aswad sai su ka samu sabani, ko wace kabila ta ce ita za ta dora, har su ka kusa yaki , sai wani ya ba da shawara cewa a hukunta farkon wanda ya shigo, sai Annabi ya zama farkon wanda ya shigo su ka ko ce ‘ mun yarda da Al’amin’ sai Annabi ya shimfida mayafin sa ya dora dutsen ya kuma umurci ko wace kabila ta kama
gefe guda , da su ka dago shi sai ya dauke shi da hanunsa mai tsarki ya dora shi a mazauninsa.
vBulletin® v3.8.8, Copyright ©2000-2025,