المساعد الشخصي الرقمي

مشاهدة النسخة كاملة : HUDUBAR JUMA'A DAGA HARAMIN MAKKA 16 Dhul Hijja 1435


طاهر جبريل دكو
_17 _October _2014هـ الموافق 17-10-2014م, 02:31 PM
HUDUBAR JUM'AH DAGA MASALLACI MAI ALFARMA
A yau jum'ah 16 ga Dhul Hajji 1435H Limamin masallaci mai alfarma Sheikh Saleh bn Muhammad Aal Dalib shi ya jagoranci sallar jum'ah.
Liman ya fara da godiya ga Allah akan kammala wannan babban rukuni daga cikin rukunan musulunci. A cikin gabatarwar hudubarsa ya yi nuni da cewa an gina addinin musulunci dukkansa akan kadaita Allah. Ya yi wasici da jin tsoron Allah. Ya ce da haka ne ake samun aminci da rahamar Allah da jinkayinsa da ni'imominsa da duniya da lahira.
Bayan haka ya bayyana ma alhazai girman ni'imar da Allah ya yi ma su na samun wannan dama. "Ku gode ma Allah. Ku roke shi ya karba ma ku".
Ya yi bushara da cewa alkawarin da Allah ya yi na gafarta ma alhazai ba zai saba ba. Sannan ya shiga bayanin yadda ake godiya ga Allah akan ni'ima.
A cikin hudubar har wayau liman ya jaddada maganar Tauhidi; kadaita Allah. Ya ce duk ayyukan hajji sun ginu ne akan kadaita Allah. Kada mu koma gida mu yi shirka bayan mun zo nan mun ce ma Allah LA SHARIKA LAK.
Liman ya kawo hadisi Sufyan wanda Muslim ya ruwaito a lokacin da ya nemi wasiyya daga manzon Allah (S) ya ce ma sa "Ka ce na yi imani da Allah sannan ka dage".
Ya jaddada kira ga musulmi su aiwatar da darussan aikin hajji idan sun koma gidajensu.
Idan aikin hajji ya kare, idan kwanukan muharram sun wuce, idan wannan ziyara ta zama tarihi.. To bautar Allah ba ta kare ba sai ranar da rayuwa ta kare.
A cikin huduba ta biyu liman ya yi nuni ga halin da al'umma take ciki. Ya gode ma Allah akan samun aminci da zaman lafiya a wannan kasa mai alfarma. Ya rufe hudubar da ayoyin suratul baqara masu nuna ci gaba da ambaton Allah bayan aikin hajji. Ya ce kuma duk alhajin da zai koma gida ya tabbata ya yi dawafin bankwana ba tare da ya maimaita sa'ayi ko ya yi aski ba. Sai fa matar da jinin al'ada ya hana ta yin su, wannan kam sai ta yi su kafin ta wuce.
Ya yi al'umma adduoi masu yawa masu dadi masu albarka. Muna rokon Allah ya karbi adduoinsa.