المساعد الشخصي الرقمي

مشاهدة النسخة كاملة : Aikin hajji cikin sauki


طاهر جبريل دكو
_10 _September _2014هـ الموافق 10-09-2014م, 02:13 AM
AIKIN HAJJI
KASHE KASHEN AIKIN HAJJI
Aikin hajji ya kasu kashi uku:
IFRADI : Shi ne mutum ya yi niyyar hajji kawai daga mikati banda umara ya na mai cewa (LABBAIKA LLAHUMMA HAJJAN)
QIRANI : Shi ne mutum ya yi niyyar hada aikin hajji da umara tun daga mikati ya na mai cewa (LABBAIKA LLAHUMMA HAJJAN WA UMRATAN)
TAMATTU'I : Shi ne mutum ya yi niyyar umara kawai daga mikati ya na mai cewa (LABBAIKA LLAHUMMA UMRATAN MUTA MATTI’AN BIHA ILAL HAJJI) idan ya isa Makka ya yi umara sai ya sauke iharami har sai ranan takwas ga wata sannan sai ya sake shiga ihrami daga gidansa ko masaukinsa a Makka ya na mai cewa (LABBAIKA LLAHUMMA HAJJAN) akwai hadaya akan mai tamattu,i da kirani amma banda mai ifradi.

BAYANI AKAN AIKIN HAJJI
Aikin hajji ya ginu ne akan rukunnai hudu da wajibai bakwai da mustahabbai masu yawa.
Rukunnan Hajji sun hada da:
1-Daukan harama (wato niyya)
2- Tsayuwar Arfa.
3- Dawaful ifada (wato dawafin da ake yi bayan an yi jifar jamra ta ranar salla)
4- Sa'ayi (wato Safa da Marwa)
wajiban Hajji kuma sun hada da;
1-Daukan ihrami daga Mikati (ga masu tahowa daga wajen Makka, amma yan Makka da wadanda ke garin makka aranar takwas ga watan Zul-hijja zasu dauki niyyarsu ce - wato ihrami - daga gidajensu da masaukansu)
2- Yin aski (sai saye ko kwalkwabo).
3 – Dakatawa a Arfa har zuwa faduwar Rana.
4- Kwanan Muzdalifa.
5- Jifan jamrori (a ranar salla babban jamra ake jifa kuma lokacin wannan jifan ya na farawa ne tun daga lokacin walha wato da hantsi amma jifan jamrori a ranakun sha daya da sha biyu da sha uku -wato ayyamu ttashrik- baya inganta har sai rana ta yi zawali wato farkon lokacin sallar azahar, duk wanda ya yi jifa kafin rana ta yi zawali jifansa bai yi ba sai ya sake)
6 – Kwanan Mina a cikin kwanaki uku ko biyu na bayan salla ayyamu ttashrik. 7 – Dawaful wada'i (wato dawafin bankwana).
Acikin aikin hajji duk abin da ba ya cikin rukunnai da wajibai to mustahabbi ne, shi rukuni barin sa ko bacin sa ya na bata aiki, wajibi kuma barin sa ko bacin sa ya na wajabta fidiya (wato yanka dabbar da ta isa layya ko kuma azumi goma ga wanda ba shi ida wadata, mustahabbi kuma barinsa bai wajabta komai sai dai wanda ya yi shi ya fi wanda bai yi shi ba.
FADAKARWA: Mai barin wajibi da gangan ana jiye masa tsoron bacin aikinsa.
TAKAITACCEN BAYANIN AYYUKAN DA ZA'AYI AKOWACE RANA.
RANAN TAKWAS GA WATAN ZULHIJJA (WATO RANAN TARWIYYA)
Duk mutumin da ke wajen garin Makka zai dauki haraminsa ne daga mikatinsa, sai haramar mai ifradi ta kasance haramar hajji wato ya ce LABBAIKA LLAHUMMA HAJJAN shi kuma mai kirani sai ya yi niyyar hajji da umra a dunkule ya na mai cewa LABBAIKA LLAHUMMA HAJJAN WA UMRATAN, da mai ifradi da mai kirani zasu daura niyyarsu ne tun daga mikati, amma shi mai tamattu'i niyyarsa daga mikati za ta kasance niyyar umra ce kawai, idan suka isa Makka sai mai ifradi ko kirani ya yi dawaful kudum sannan sai ya yi sa'ayinsa (safa da marwa) tun alokacin ko kuma ya jinkirta shi sai bayan ya yi xawaful ifada ranar salla ko bayan shi, kuma su zasu tabbata cikin tufafinsu na ihrami har sai sun aikata biyu daga cikin ayyukan ranar salla, shi ko mai tamattu'i dawafinsa dawafin umra ne bayan shi sai ya yi sa'ayin umra ya yi aski, da haka ya idar da Umara ke nan, sannan sai ya yi haramar hajji ranan takwas ga wata daga Makka amasaukinsa ya na mai cewa LABBAIKA LLAHUMMA HAJJAN ya kuma ci gaba da talbiyya sannan sai kowa da kowa ya kama hanyar tafiya Mina, ya wuni a can, sallolinsa a wannan yinin za su kasance kamar haka; Azahar kasaru wato raka'a biyu La'asar ma haka Magariba kam kamar yadda take raka'a uku Isha'i ma kasaru wato raka'a biyu irin sallar matafiyi dukkanin sallolin nan zai yi su tare da jama'a acikin jam'i kuma kowacce za a yi ta ne a lokacinta, a ranar zai kwana a Mina har ya wayi gari ranan tara gawata.
2- RANAN TARA GAWATA (WATO RANAR ARFA). Idan ya wayi gari ranan tara ga wata ya yi sallan asuba a Mina sai ya nufi Arfa don tsayuwa, aranar zai sallaci Azahar da La'asar alokaci daya wato lokacin sallar Azahar, zai yi su raka'o'i bibbiyu wato kasaru, in ya samu dama ya yi su a masallacin Namira sannan sai ya isa filin Arfa, ya tabbatar da cewa ya shiga cikin filin arfa, zai iya gane shigan sa Arfa ne ta hanyar lura da alluna da aka sanya akan iyakokin arfa, zai gani arubuce ajiki an ce ( Arfa ta fara daga nan da harshen larabci ko turanci) saboda haka ka da Alhaji ya kuskura ya tsaya a wani wuri da baya cikin Arfa domin in ya rasa tsayuwar arfa har lokaci ya kure to hajjin wannan shekarar ya kubuce masa kenan. Annabi (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya ce:"Arfa ita ce hajji
Mutum zai tabbata a cikin Arfa ya na mai tsayuwa ko zama an fi son ya fiskanci alkibla ya kuma yawaita anbaton Allah da addu'o'i na bukatun duniya da lahira Annabi (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya ce:"Mafi alkhairin addu'a ita ce addu'ar ranar Arfa kuma mafi alherin abin da na fadi da ni da annabawan da suka gabace ni shi ne; LA'ILAHA ILLA LLAHU WAHDAHU LA SHARIKA LAHU LAHUL MULKU WA LAHUL HAMDU WA HUWA ALA KULLI SHAI'IN QADIR" kuma koda ya yi bacci awurin babu laifi. Zai kasance a filin Arfa har sai ya haqiqance faxuwar rana sannan sai ya kama hanyar tafiya Muzdalifa sai ya isa can ne zai hada sallolin magariba da isha'i ya yi su a lokaci guda, zai yi Isha'i kasaru wato raka'a biyu, za a yi sallolin ne ackin jam'i wato tare da liman, za a yi musu kiran salla daya in hali ya samu amma kowace salla za ayi mata ikamarta ta musamman. Idan mutum ya ji tsoron fitan lokaci kafin ya isa muzdalifa sai ya yi sallolin biyu akan hanya, kuma ba a yin nafila kafin sallolin ko bayansu haka nan ma cikin dare sai dai witiri da raka'o'in Alfijir su kam Annabi (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ba ya barinsu ko acikin halin tafiya.
Idan matum ya iso muzdalifa ya hakikance shigansa cikinta ta hanyar lura da alamu kamar yadda ya ke a Arfa sai ya yi sallolinsa sa'annan ya nemi wuri ya kwanta ya yi bacci har sai Alfijir ya keto, in ya yi sallar asubahi sai ya ci gaba da anbaton Allah ya na mai fiskantar alkibla har sai gari ya washe sarai sa'annan ya kama hanyar Mina kafin hudowar rana.
RANAN GOMA GA WATA: WATO RANAR SALLA KO RANAR SUKA
A wannan yinin ayyukan da ake yi ayyuka ne guda hudu ga mai tamattu'i da kirani ko kuma uku ga mai ifradi;
NA DAYA: JIFAN BABBAN JAMRA) lokacin jifan ya na farawa ne daga hantsi, da zaran mahajjaci ya isa mina sai ya je ya yi jifan babban jamra wanda shi ne na karshe a jerin jamrori uku ga wanda ya fito muzdalifa, zai yi jifan ne da duwatsu bakwai yan kankana kamar girman dan gurjiya ko mai kama da shi, kuma zai jefa su ne daya bayan daya ya na mai yin kabbara tare da kowane dutse yayin jefawa, bai halatta ayi jifan ba sai da dutse, saboda haka baza a yi da kamar kwallon dabino ko gutsuren katako ko karfe ba da makamantansu, kuma a yayin da zai fara wannan jifan ne zai yanke talbiyya.
FAXAKARWA: Anyi rangwame ga mata masu rauni da maza masu uzurori na musamman da su bar muzdalifa bayan dare ya raba, kuma wannan lokacin ya na farawa ne daga sa'ad da wata ta buya. Amma sunna ga wadanda ba masu uzuri ba shi ne kwana a muzdalifa har gari ya waye.
NA BIYU: HADAYA GA WANDA YA YI HAJJIN TAMATTU'I KO QIRANI
ko dai mutum ya yanka da kansa, ko kuma ya wakilta wani amintaccen mutum ko kamfani (amma ba na baka shawarar wakilta wani mutum ko wanene shi kuwa, abin da ya fi shi ne biya a banki duk da cewa yafi tsada amma yafi tabbaci). Sharuddan dabbar hadaya su ne; ta kasance daga cikin dabbobin ni'ima wato dangin rakuma(mai shekara biyar zuwa sama) ko shanu (mai shekara biyu zuwa sama) ko tumaki (mai watanni shida zuwa sama) ko awaki (mai shekara daya zuwa sama) sannan ta zama kubutacciya daga aibubbuka kamar; ido daya ko bayyanannen rashin lafiya ko bayyanannen dingishi ko ramammiya mara maiko. karamar dabba zata iya isan mutum daya ne wato kamar tunkiya ko rago ko taure ko akuya, manyan dabbobi kuma ko wane daya ya na isan mutum bakwai wato kamar bujumi ko saniya ko rakumi ko taguwa, kuma ya halatta mutum ya ci daga cikin naman hadayarsa, ya yi sadaka kuma ya yi kyauta. Idan mutum bai da wadatan da zai yi hadaya sai ya yi azumi goma guda uku ya yi su tun a kwanakin hajji, bakwai kuma sai ya koma garinsa.
NA UKU ASKI
Ya halatta na miji ya yi kwal kwabo, ko saisaye ga maza, ko kuma saisaye wato yanke gwargwadon kan yatsa ga mace idan gashinta na tsefe, idan kuma ya na kitse ne sai ta yanke gwargwadon kan yatsa ko makamancin haka daga ko wane kitso. Daga nan mutum ya yi karamin tahalluli ke nan, wato duk abin da aka haramta masa a sakamakon ihrami to yanzu ya halatta a gare shi sai dai jima'i kawai shi kam bai halatta har sai mutum ya yi ayyuka uku gaba daya.
NA HUDU: DAWAFUL’ IFADA
Idan mutum ya yi jifa ya yanka dabbar hadaya ya yi aski sai ya garzaya Makka don yin dawaful ifada sannan ya yi sa'ayi (wannan ga mai hajjin tamattu'i kenan amma mai kirani ko ifradi ba zai sake sa'ayi ba matukar ya yi shi tare da dawaful dudum) daga nan komai ya halatta gare shi cikin abubuwan da aka hana shi yi sakamakon shiga ihrami har matarsa wato ya yi tahalluli babba kenan, daga nan kuma sai ya yi kokari ya koma Mina kafin faxuwar rana.
FAXAKARWA: Ayyukan ranar salla guda hudun nan (jifa, hadaya, aski da xawafi duk wanda aka fara da shi ya yi babu laifi.
AYYUKAN RANAKUN SHA XAYA, SHA BIYU DA SHA 'UKU GA WATA (AYYAMU TTASHRIK) Alhaji zai zauna a Mina kwana biyu (wato sha xaya da sha biyu ga wata) ga wanda ya gaggauta kenan ko kuma kwanaki uku wato har zuwa sha uku ga wata ga wanda ya yi jinkiri, amma yin jinkirin ya fi falala ga mai takawa. Idan mutum ya na da niyyar ya gaggauta wato ya bar Mina a ranar sha biyu ga wata to ya wajaba a gare shi yabar mina kafin rana ta fadi a ranar sha biyu ga watan. Idan kuma ya bari rana ta fadi masa bai bar Mina ba a wannan ranar to sai ya kara kwana a Mina har zuwa zawalin ranar sha'uku ga wata ya yi jifan wannan ranar. Acikin wadannan kwanaki uku ko biyu da zai yi a Mina kullum zai je ya jefi jamrori uku baki daya kowanne da duwatsu bakwai bakwai yana mai yin kabbara a yayin da zai jefa kowane dutse, kuma dole ne yabi tsarin jamrorin a yayin jifan, wato ya fara da ta farko sannan ta tsakiya sannan ta karshe.
LOKACIN JIFA: Ba a jifa a wadannan kwanakin sai rana ta yi zawali, wato lokacin sallan azahar kenan, idan mutum ya kuskura ya yi jifa kafin zawali a wadannan kwanakin malamai suka ce jifarsa bata inganta ba sai ya sake bayan azahar ko kuma hukuncinsa ya zama hukuncin wanda ya bar wajibi.
Anaso mutum ya tsaya ya yi addu'a idan ya jefi jamra ta farko kafin ya jefi ta biyu hakama idan ya jefi ta biyu kafin ya jefi ta uku, amma in ya jefi ta uku ba zai tsaya ya yi addu'a ba, kai tsaye sai ya wuce ba tsayawa.
XAWAFUL WADA'I (WATO XAWAFIN BANKWANA)
Aikin karshe da ke kan alhaji acikin aikin hajji shi ne dawafin bankwana, wannan dawafi wajibi ne bisa ra'ayi mafi rinjayi, kuma dawafin akan yi shi ne kafin fita daga garin Makka bayan an shige shi da niyyar aikin hajji, ko da kuwa mahajjacin zai je wani gari ne ya dawo ba wai ya tafi kasarsa kenan ba, kamar masu zuwa Jidda don sayayya bayan sun gama aikin hajji, to abinda ya kamata shi ne su yi dawafin kafin su fita, kuma duk wanda ya yi dawafin a lokacin da zai fita wajen Makka don wata bukata to ya sauke wajibinsa, saboda haka ko ya dawo ba zai sake dawafin bankwana ba, don ya riga ya sauke wannan wajibin da wancan da ya yi kafin ya fita sai dai yayi ta yin ta nafila.
Macen da take cikin haila ko biki bata tsarkakaba har tafiyarsu ta tashi an yafe mata dawafin bankwana matukar ta riga ta yi dawaful ifada, idan kuma ba ta yi dawaful ifada ba tafiyarsu ta tashi kuma ba zai yiwu a jirata har ta tsarkaka ba, ko kuma a canza mata jirgi ta yadda tafiyarta zai jinkirta har ta ta tsarkaka ba kuma babu hali taje ta dawo saboda nisa to daga cikin manyan malamai akwai masu ganin cewa zata yi dawafinta acikin wannan halin kuma babu komai a kanta saboda ba ta da zabi sai dai hakan kuma Allah baya dorawa bawa sai abinda zai iya. Allah shine mafi sani.
Don neman karin bayani tuntubi
Dahiru Jibril Dukku ta wannan layin
0530724716) Email muhammadjibril837@yahoo.com)