تسجيل الدخول

مشاهدة النسخة كاملة : Ladubba goma daga shekh saleh ibn abullahi ibn hamad al -usaimi


طاهر جبريل دكو
_25 _July _2014هـ الموافق 25-07-2014م, 04:33 PM
بسم الله الرحمن الرحيم
الآداب العشرة للشيخ صالح بن عبد الله بن حمد العصيمي حفظه الله
LADUBBA GOMA
Ka sani- Allah Ya shiryar da ni da kuma kai- na daga manyan ladubba goma;
Na farko; idan ka gamu da musulmi kayi masa sallama kana mai cewa;
Assalamu'alaikum wa rahmatu llahi wa barakatuhu. In wani ya yi maka sallama kuma ka ce;
wa alaikumussalamu wa rahmatullahi barakatuhu.
Na biyu: in ka nufi shiga kan wani, ka nemi izini alhali kana tsaye daga dama ko hagu da kofa, in anyi maka izini sai ka shiga, in ba haka ba ka koma.
Na uku: ka ambaci sunan Allah in za ka ci ko za ka sha kana mai cewa;
Bismillah. Kuma ka ci abin da ke gabanka, kuma ka sude yatsunka in ka kare sannan sai ka ce : Alhamdu lillahi.
Na huxu: in Za kayi zance ka fadi alheri da kyakkyawan lafazi, ka sassawta muryarka, kana mai maga sannu sannu, ka kyawtata sawrare ga wanda ke Magana da kai kana mai fiskantan sa, kada ka katse masa zancensa, kada kuma ka gabaci wanda ya girme ka da Magana.
Na biyar: idan ka zo kwanciya ka yialwala sannan ka kwanta ta gefenka na dama, ka karanta ayatul kursiyyu, sannan ka hada tafukan hannayenka ka karanta kulhuwa da falaqi da nasi sai ka tofa a cikinsu sannan ka shafi dukkan jikinka gwargwadon iko (kana mai farawa da fuska har sau uku).
Na shida: idan za kayi attishawa ka toshe bakinka da hannunka ko da tufarka sannan ka ce Alhamdulillah. In wani ya ce maka Yarhamukallah; to ka ce: yahdikumullahu wa yuslihu balakum.
Na bakwai: ka tunkude hamma gwargwadon iyawarka ko ka toshe da hannunka, kada ka ce: Aah! Aah!
Na takwas: idan ka iso wurin zama ka yi sallama, ka zauna inda zaman mutane ya tuke, kada ka zauna tsakanin rana da inuwa, kada ka rabe tsakanin mutane biyu sai da izininsu, kada ka tada wani don kai ka zauna, ka yalwatawa duk wanda ya shigo, ka ambaci Allah a wurin, mafi karancin sa shi ne,kaffaratul majliis: subhanakallahumma wabi hamdika astagfiruka wa'atubu ilaika.
Na tara: ka bawa hanya hakkinta, ka runtse idonka, kada ka cutar da wani, ka maida sallama, ka yi umurni da kyakkyawa ka kuma yi hani ga mummuna.
Na goma: kasanya tufafi mai kyau, sonsamu fari, kada kuma ya wuce idon sawu, in zaka sa tufa ka fara da dama in zaka cire ka fara da hagu.