المساعد الشخصي الرقمي

مشاهدة النسخة كاملة : Fa'idoji akan azumi daga malam uthaimin allah ya ji kan sa(نبذ في الصيام للشيخ العصيمين)


طاهر جبريل دكو
_10 _July _2014هـ الموافق 10-07-2014م, 02:53 PM
بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيمِ

Dukkan godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai, salati da sallama su tabbata ga Annabinmu Muhammadu da Alayensa da Sahabbansa baki xaya. Bayan haka:
Wannan 'yar tunatarwa ce takaitacciya a kan azumi da hukunce hukuncensa da karkasuwan mutane a game da shi da abubuwan da suke bata azumi da wasu fa'idoji ma na dabam.
Na daya: Azumi shi ne, yin bauta ga Allah ta hanyar kame wa daga dukkanin abubuwan da ke karya azumi tun daga ketowar Alfijir har zuwa faduwar Rana.
Na biyu: Azumin watan Ramadana daya ne daga cikin rukunnan Musulunci masu girma, saboda fadin Annabi (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi):
"بني الإسلام على خمس: شهادة أن لا إله إلا الله، وأن محمد رسول الله، وإقام الصلاة، وإيتاء الزكاة، وصوم رمضان، وحج البيت الحرام" [متفق عليه] .
Ma'ana: "An gina Musulunci ne a kan rukunnai guda biyar; shaidawa babu abin bautawa bisa cancanta sai Allah kuma lallai Muhammadu Manzon Allah ne, da tsaida sallah da bada zakka da azumtan watan Ramadana da zuwa dakin Allah mai alfarma domin aikin Hajji. Bukhari da Muslim ne suka ruwaito shi.
(Karkasuwan) Mutane game da azumi.
Na Daya: Azumi wajibi ne a kan dukkanin Musulmi baligi mai hankali wanda ya ke da iko kuma ya na mazaunin gida.
Na biyu: Kafiri ba ya azumi, kuma biyan (azumi) ba ya wajaba a kansa idan ya musulunta.
Na uku: Yaro karami wanda bai balaga ba azumi bai wajaba a kansa ba, sai dai za'a umurce shi da shi saboda ya saba.
Na hudu: Mahaukaci azumi ba ya wajaba a kansa kuma ba za'a ciyar masa ba, koda kuwa babba ne shi, haka nan mai tabin hankali wanda ba ya iya bambancewa tsakanin abubuwa, da tsoho mai sumbatu wanda ba ya iya bambancewa tsakanin abubuwa (saboda tsufa).
Na biyar: Mara lafiya rashin lafiya mai bijirowa wanda ake sauraron warakarsa, idan azumi zai wahalar da shi sai ya sha, amma zai biya bayan waraka.
Na shida: Mai ciki da mai shayarwa, idan azumi ya na basu wahala sakamakon cikin ko shayarwar, ko suka guje wa 'ya'yansu (na ciki da wanda ake shayarwa wahala) zasu ajiye azumi amma zasu rama idan abinda suke tsoron ya gushe.
Na bakwai: Mai haila da mai biki basu azumi yayin da suke cikin hailar da bikin, amma zasu rama abin da ya kubuce musu na azumin (a kwanakin hailar ko bikin).
Na takwas: Wanda ya bukatu zuwa ga karya azumi domin ceto wani ma'asumi (mara laifi) daga nutsewa a ruwa ko gobara zai karya azumi domin kubutar da shi amma zai rama.
Na tara: Matafiyi idan ya ga dama sai ya yi azumi, idan ya ga dama kuma sai ya sha azumi, sai ya rama abinda ya sha, (hakan ya halatta gare shi) sawa'an tafiyar ta bijiro ne kamar tafiya ta umura, ko tafiya ce ta dindindin kamar 'yan tasi matukar dai basu kasance a garinsu ba.





Abubuwan da suke karya azumi.
Idan mai azumi ya ci ko ya sha wani abu bisa mantuwa ko rashin sani ko aka tilasta shi, to babu ramuko akansa saboda fadin Allah (Maxaukaki)
{رَبَّنَا لَا تُؤَاخِذْنَا إِنْ نَسِينَا أَوْ أَخْطَأْنَا} [البقرة: 286] .
Ma'ana: "Ya Ubangijinmu, kada Ka kama mu (da laifi) idan muka yi mantuwa ko kuskure" (Suratul Baqara 286)
Da faxinSa:
{إِلَّا مَنْ أُكْرِهَ وَقَلْبُهُ مُطْمَئِنٌّ} [النحل: 106]
Ma'ana: "Sai dai wanda aka tilasta alhali zuciyarsa ta na nuste da imani" (Suratun Nahli 106)
{وَلَيْسَ عَلَيْكُمْ جُنَاحٌ فِيمَا أَخْطَأْتُمْ بِهِ وَلَكِنْ مَا تَعَمَّدَتْ قُلُوبُكُمْ} [الأحزاب: 5] .
Ma'ana: "Kuma babu laifi a kanku cikin abinda ku ka aikata bisa kuskure, sai dai abin da zukatanku suka aikata bisa ganganci" (Suratul Ahzab 5)
- Saboda haka idan mai azumi ya manta sai ya ci ko ya sha to azuminsa bai baci ba, saboda shi mai mantuwa ne.
- Kuma da zai ci ko ya sha bisa zaton cewa Rana ta fadi ko kuma Alfijr bai keto ba, to azuminsa bai baci ba saboda shi jahili ne.
- Kuma da zai yi kurkuran baki sai ruwa ya zarce cikin makogwaronsa ba tare da nufi ba azuminsa bai baci ba saboda ba da gangan ba ne.
- Kuma da zai yi mafarki, azuminsa bai baci ba saboda ba shi da zabi.
Abubuwa masu karya azumi guda takwas ne, sune kamar haka:
Na daya: Jima'i idan ya faru daga mutumin da azumi ya wajaba a kansa da rana a cikin ramadana, akwai ramuko a kansa tare da kaffara kakkausa, ita ce 'yanta wuya (wato bawa) idan bai samu dama ba, sai ya azumci watanni biyu a jere, idan bai samu dama ba sai ya ciyar da miskinai sittin.
Na biyu: Fitar da maniyyi a farke ta hanyar wasa da gaba don biyan bukata, ko runguma ko sumbata ko wanin haka.
Na uku: Ci ko sha sawa'un abin da (aka ci ko aka sha) mai amfani ne ko mai cutarwa kamar (taba) sigari.
Na hudu: Allura ko ruwa (wato drip) wanda ya ke iya wadatarwa daga abinci saboda kasancewarsa da ma'anar ci da sha. Amma alluran da ba ya zama madadin abinci, to shi ba ya karya (azumi) sawa'un ta gabbai aka yi shi ko ta jijiyoyi.
Na biyar: Sanya jini, kamar mai azumi ya samu zuban jini sai a saka masa jini domin maye jinin da ya zuba daga jikinsa da fitan jinin haila da biki.
Na shida: Fitar da jini daga jiki ta hanyar yin kaho da makamancinsa. Amma zuban jini da kansa kamar habo ko fitan jini sakamakon cire hakori ko makamancin sa, to shi kam baya karya azumi saboda shi ba kaho ba ne, kuma bai daukan ma'anar kaho.
Na bakwai: Amai idan (mai azumi) ya jawo shi da gangan, amma idan amai ya zo masa ba da gangan ba, to azuminsa bai karye ba.

Fa'idoji
Na daya: Ya halatta ga mai azumi ya yi niyyar azumi alhali ya na da janaba sannan ya yi wanka bayan ketowar alfijir.
Na biyu: Ya wajaba ga mace idan ta tsarkaka daga haila ko biki a cikin ramadana kafin ketowar alfijir ta yi azumi koda kuwa bata yi wanka ba har sai bayan ketowar alfijir.
Na uku: Ya halatta ga mai azumi ya cire hakorinsa ko ya sa magani a rauninsa, da diga (magani a idanunsa ko kunnuwansa (idan ya bukaci yin hakan), azuminsa ba zai karye ba don ya yi hakan koda kuwa ya ji dandano a wuyarsa.
Na hudu: Ya halatta ga mai azumi ya yi asuwaki a farkon yini ko karshensa, kuma shi (asuwaki) sunna ne gare shi kamar yadda yake sunna ga mara azumi.
Na biyar: Ya halatta ga mai azumi ya yi wata dabara da zata saukaka masa tsananin zafi da kishin ruwa kamar watsa ruwan sanyi ko ya zauna a karkashin air condition.
Na shida: Ya halatta ga mai azumi ya shaki abin da zai saukake masa kuncin numfashi wanda ya ke faruwa sakamakon toshewar manumfasa ko makamancinsa.
Na bakwai: Ya halatta ga mai azumi ya jika labbansa da ruwa idan sun bushe, kuma ya yi kurkuran baki idan bakinsa ya bushe ba tare da ruwa ya zarce makoshi ba.
Na takwas: An sunnanta wa mai azumi ya jinkirta suhur har zuwa gaf da ketowan alfijir kuma ya gaggauta buxa baki bayan faduwar rana, kuma ya buda baki da danyen dabino, idan bai samu ba sai ya bude da busasshen dabino, idan bai samu ba kuma sai ya bude da bakin ruwa, idan bai samu ba kuma sai ya bude da kowane irin abinci na halal, idan bai samu ba sai ya yi niyyar bude baki a zuciyarsa har zuwa sa'adda zai samu.
Na tara: An sunnanta wa mai azumi da ya yawaita ayyukan da'a kuma ya nisanci dukkunin abubuwan da aka hana.
Na goma: Ya wajaba ga mai azumi ya kula da wajibai da nisantan haramtattu, saboda haka sai ya aiwatar da salloli biyar na farilla a kan lokutansu, kuma ya aiwatar da su a cikin jam'i idan ya kasance daga wadanda saallar jam'i ta wajaba a kansu ne, kuma ya bar karya da giba da cuta da mu'amaloli na riba, da duk wata magana ko aiki haramtacce. Annabi (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya ce:
"من لم يدع قول الزور والعمل به والجهل فليس لله حاجة في أن يدع طعامه وشرابه". [رواه البخاري] .
Ma'ana: "Wanda bai bar karya ba da aiki da ita da jahilci, to Allah ba Shi da bukatar barin cin abincinsa da shan abin shansa" Imamul Bukhari ne ya ruwaito shi.

Alhamdu lillahi Rabbil alamin, salatin Allah da amincinsa su tabbata ga Annabinmu Muhammadu (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) da alayensa da sahabbansa baki daya.

Wanda ya wallafa shi shi ne, mabukaci zuwa ga Allah (Madaukaki)
Muhammad Salihul Uthaimin a ranar 16 ga watan sha'aban, shekara ta 1401 AH.
Wanda ya tarjama: Dahiru Jibril Dukku 27 sha'aban, 1435 AH.