المساعد الشخصي الرقمي

مشاهدة النسخة كاملة : Sabubba goma masu jawo soyayyar allah - maxaukakin sarki- ga bawa


طاهر جبريل دكو
_2 _June _2014هـ الموافق 2-06-2014م, 05:10 PM
SABUBBA GOMA MASU JAWO SOYAYYAR ALLAH - MAXAUKAKIN SARKI- GA BAWA
Ibnul qayyim - acikin Madarijussalikin - yace:
Fasali: cikin sabubba masu jawo soyayya kuma masu wajabta ta.
Su Goma ne.
Na xaya: karatun Qur'ani da tadabburinsa da qoqarin fahimtan ma'anoninsa da abinda ake nufi da shi. Kamar tadabburin littafin da bawa ke haddansa kuma yake sharhinsa domin ya fahimci manufan mawallafinsa game da shi.
Na biyu: Neman kusanci zuwa ga Allah ta hanyar nafilfilu bayan farillai, domin wannan zai isar da shi zuwa ga matakin qauna bayan soyayya.
Na uku: dawwama akan ambaton Sa (wato Allah) acikin ko wane hali, (ambato) da harce da zuci da aiki da hali, saboda kasonsa (wato bawa) a cikin soyayyar (Allah) ya ta'allaqa ne da gwargwadon kasonsaa cikin wannan zikirin.
Na huxu: Fifita abin da Allah ke so bisa abinda ka ke so a yayin da son zuciya ya ke galaba, da xoruwa kan abinda Allah Ya ke so ko da hakan ya yi wuya.
Na biyar: Leqawar zuciya ga sunayenSa da sifofinSa, da sheda (girmansu) da saninsu da jujjuyawansa acikin dawsayin wannan sanin da muhimman (al'amura game da su), saboda duk wanda ya san Allah da sunayenSa da sifofinSa da ayyukanSa, babu makawa zai so shi, shi yasa Almu'axxilatu (wato masu vata sunayen Allah da sifofinSa) da fir'aunawa (wato waxanda suke kan irin kafircin Fir'auna na inkarin cewa akwai Allah) da jahamiyyawa (wato masu bin Jaham akan vatansa, duk masu kangiya ne ga zukata daga isa zuwa ga abin so.
Na shida: Hangen kyawtatawarSa da ni'imominSa na voye da na fili. Domin wannan yana jawo qawnarSa.
Na bakwai: Yana daga cikin mafi ban shi'awa, karayan zuciya gaba xayansa a gaban Allah – Maxaukaki – babu abinda ke iya fito da wannan ma'anan face sunaye da ibarori.
Na takwas: Yin khalwa cikin (bautan Allah) domin ganawa da Shi da karanta magananSa da tsayuwa da zuciya da ladabtuwa da ladubban bauta a gabanSa a lokacin saukan Allah (saman Duniya) sa'annan cikata wannan da istigfari da tuba.
Na tara: Zama da masu son (Allah) so na gaskiya, da tsitstsintan daxaxa daga maganganunsu kamar yadda ake zazzavan daxaxan dabinai. Kuma kada kayi magana har sai idan maslahar yin magana ta fi rinjayi, kuma ka san cewa (yin maganan) qaruwa ne gare ka kuma amfani ne ga waninka.
Na goma: Nisantar da duk wani sababi da zai shiga tsakanin zuciya da Allah mai girma da buwaya.
Da waxannan sabubban guda goma ne masoya (Allah) suka gai ga matakai na soyayya, kuma suka shiga ga masoyi, abinda ke mallake da wannan gaba xaya abubuwa biyu ne, shi ne tanadin Ruhi ga wannan al'amarin, da buxuwar idon basira.
Allah Shine mai datarwa.