المساعد الشخصي الرقمي

مشاهدة النسخة كاملة : Matanin Thalathatul Usul na Asshekh Muhammadu binu Abdilwahhab Allah Ya ji kan sa


طاهر جبريل دكو
_29 _May _2014هـ الموافق 29-05-2014م, 01:50 AM
Thalathatul Usul
Asali Guda Uku
Wallafar shehin Musulunci, Muhammad dan Abdulwahhab – Allah Ya tsarkake ransa, wanda ya rasu (a shekara) ta 1206 bayan hijira.

Da sunan Allah Mai rahama Mai jin kai.
Ka sani, Allah Ya yi maka rahama, cewa; lallai ya wajaba a gare mu mu san wasu mas'aloli guda hudu:
Na farko :Ilimi shi ne sanin Allah, da sanin AnnabinSa da sanin addinin Musulunci da dalilai.
Na biyu : Aiki da shi.
Na uku: Kirazuwa gare shi.
Na hudu: Yinhakuri game da cutuwa a cikinsa.
Dalili a kan haka shi ne : Fadin Allah - Madaukaki

بسم الله الرحمن الرحيم
وَالْعَصْرِ (1) إِنَّ الْإِنْسَانَ لَفِي خُسْرٍ (2) إِلَّا الَّذِينَ آَمَنُوا وَعَمِلُوا الصَّالِحَاتِ وَتَوَاصَوْا بِالْحَقِّ وَتَوَاصَوْا بِالصَّبْرِ (3)
Ma'ana: Da sunan Allah Mai rahama Mai jin kai.
Ina rantsuwa da zamani (1) Lallai ne mutum tabbas yana cikin hasara (2) Face wadanda suka yi imani kuma suka aikata ayyukan kwarai kuma suka yi wa juna wasiyya da bin gaskiya, kuma suka yi wa juna wasiyya da yin hakuri (3)
(Al'imam) Asshafi'i – Allah Ya yi masa rahama – ya ce : Da a ce Allah bai saukar da wata hujja ba a kan halitta face wannan surar, da ta wadatar da su.
Bukhari -Allah Ya yi masa rahama – ya ce : Babi; ilimi gabanin magana da aiki.
Dalilin shi ne fadin Allah – Madaukaki
فَاعْلَمْ أَنَّهُ لَا إِلَهَ إِلَّا اللَّهُ وَاسْتَغْفِرْ لِذَنْبِكَ (19)
Ma'ana: Ka sani cewa; lallai babu abin bautawa bisa cancanta sai Allah kuma ka nemi gafarar zunubbanka (Muhammad 19)
Sai ya fara da (ambaton) ilimi kafin magana da aiki.
Ka sani –Allah ya yi maka rahama- cewa ya na wajaba ga dukkanin musulmi da musulma su san wadannan mas'alolin guda uku, da aiki da su.
Ta daya: Cewa lallai Allah Ya halicce mu kuma Ya azurta mu kuma bai bar mu kara zube ba, a'a Ya aiko Manzo zuwa gare mu; wanda ya yi masa da'a, zai shiga Aljanna, wanda kuma ya saba masa, zai shiga wuta.
Dalilin haka shi ne; fadin Allah – Madaukaki

إِنَّا أَرْسَلْنَا إِلَيْكُمْ رَسُولًا شَاهِدًا عَلَيْكُمْ كَمَا أَرْسَلْنَا إِلَى فِرْعَوْنَ رَسُولًا (15) فَعَصَى فِرْعَوْنُ الرَّسُولَ فَأَخَذْنَاهُ أَخْذًا وَبِيلًا (16)
Ma'ana: Lallai Mu Mun aiko muku wani manzo yana mai yin sheda a kan ku kamar yadda Muka aika wa Fir'auna da Manzo (15) Sai Fir'auna ya saba wa Manzon, sai Muka kama shi kamu mai tsanani (16) (Muzzammil 15-16)
Ta biyu : Cewa lallai Allah ba Ya yarda da a yi maSa tarayya da wani cikin bautarSa, ko da (wanda za a bauta wa tare da shi din) mala'iki ne makusanci (ga Allah) ko kuma annabi ne wanda yake manzo.
Dalilin kan haka shi ne ; fadinSa – Madaukaki

وَأَنَّ الْمَسَاجِدَ لِلَّهِ فَلَا تَدْعُوا مَعَ اللَّهِ أَحَدًا (18)
Ma'ana: Kuma lallai masallatai na Allah ne, saboda haka, kada ku kirayi wani tare da Allah (Jinn 18)
Ta uku: Cewa lallai wanda ya yi wa Manzon (Allah) biyayya, ya kuma kadaita Allah, to ba ya halatta gare shi ya jibinci wanda ya saba wa Allah da Manzonsa ko da kuwa ya kasance dan'uwa ne mafi kusanci.
Dalilin haka shi ne ; fadinSa – Madaukaki

لَا تَجِدُ قَوْمًا يُؤْمِنُونَ بِاللَّهِ وَالْيَوْمِ الْآَخِرِ يُوَادُّونَ مَنْ حَادَّ اللَّهَ وَرَسُولَهُ وَلَوْ كَانُوا آَبَاءَهُمْ أَوْ أَبْنَاءَهُمْ أَوْ إِخْوَانَهُمْ أَوْ عَشِيرَتَهُمْ أُولَئِكَ كَتَبَ فِي قُلُوبِهِمُ الْإِيمَانَ وَأَيَّدَهُمْ بِرُوحٍ مِنْهُ وَيُدْخِلُهُمْ جَنَّاتٍ تَجْرِي مِنْ تَحْتِهَا الْأَنْهَارُ خَالِدِينَ فِيهَا رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُمْ وَرَضُوا عَنْهُ أُولَئِكَ حِزْبُ اللَّهِ أَلَا إِنَّ حِزْبَ اللَّهِ هُمُ الْمُفْلِحُونَ (22)
Ma'ana: Ba za ka samu mutane masu yin imani da Allah da ranar lahira suna yin soyayya da wanda ya saba wa Allah da Manzonsa ba, ko da sun kasance ubanninsu ne ko 'ya'yansu ko 'yan'uwansu ko danginsu, wadannan Allah Ya rubuta imani a cikin zukatansu kuma ya karfafe su da wani ruhi daga gare Shi, kuma zai shigar da su gidajen Aljanna wadanda koramu ke gudana a karkashinsu, suna masu dawwama a cikinsu, Allah Ya yarda da su, kuma su ma sun yarda da Shi, wadannan kungiyar Allah kenan, ku saurara! Kungiyar Allah sune masu rabauta. (Mujadala 22)
Ka sani – Allah Ya shiryar da kai zuwa ga yi maSa da'a- cewa lallai hanifiyya addinin (Annabi) Ibrahim shi ne ; ka bauta wa Allah Shi kadai kana mai tsarkake addini gare Shi, da wannan ne Allah Ya umurci dukkan mutane, kuma domin shi Ya halicce su.
Kamar yadda –Madaukaki Ya ce
وَمَا خَلَقْتُ الْجِنَّ وَالْإِنْسَ إِلَّا لِيَعْبُدُونِ (56)
Ma'ana: Kuma ban halicci mutum da aljani ba sai don su bauta miNi. (Dhariyat 56).
Ma'anan su bauta miNi shi ne, su kadaita Ni. Kuma mafi girman abin da Allah Ya yi umurni da shi, shi ne tauhidi, wato kadaita Allah da bauta. Kuma mafi girman abin da Allah Ya hana shi ne shirka, wato kiran waninSa tare da Shi.
Dalili akan haka fadinSa Madaukaki

وَاعْبُدُوا اللَّهَ وَلَا تُشْرِكُوا بِهِ شَيْئًا (36)
Ma'ana: "Kuma ku bauta wa Allah kuma kada ku yi masa tarayya da komai" (Annisa'i36)
Idan aka ce maka: menene asali guda uku da ya wajaba ga mutum ya san su? Sai kace ; sanin bawa ga Ubangijinsa, da addininsa, da Annabinsa Muhammadu – tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi
Idan aka ce maka wanene Ubangijinka? Sai ka ce ; Ubangijina Shi ne Allah wanda Ya rene ni kuma ya reni dukkan talikai da ni'imominsa. Kuma Shi ne abin bautana, bani da wani abin bauta koma bayanSa.
Dalili akan haka shi ne fadinSa – Madaukaki
الْحَمْدُ لِلَّهِ رَبِّ الْعَالَمِينَ (1)
Ma'ana: "Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai" (Fatihah 2)
Kuma duk wani abu koma bayan Allah taliki ne, kuma ni daya ne daga cikin wadannan talikan.
Idan aka ce maka; da me ka san Ubangijinka? Sai ka ce ; da ayoyinSa da halittunSa, kuma daga cikin ayoyinSa akwai; dare da yini da Rana da Wata, kuma yana daga cikin halittunSa; Sammai bakawi da Kassai bakwai da abin da ke cikinsu da abin da ke tsakaninsu.
Dalili akan haka fadinSa – Madaukaki
وَمِنْ آَيَاتِهِ اللَّيْلُ وَالنَّهَارُ وَالشَّمْسُ وَالْقَمَرُ لَا تَسْجُدُوا لِلشَّمْسِ وَلَا لِلْقَمَرِ وَاسْجُدُوا لِلَّهِ الَّذِي خَلَقَهُنَّ إِنْ كُنْتُمْ إِيَّاهُ تَعْبُدُونَ (37)
Ma'ana: Kuma daga cikin ayoyinSa akwai ; dare da yini da rana da wata, kada ku yi sujjada ga Rana kuma kada ku yi ga Wata, ku yi sujjada ga Allah wanda Ya halicce su, in har kun kasance Shi ku ke bauta wa. (Fussilat 37)
Da fadinSa – Madaukaki
إِنَّ رَبَّكُمُ اللَّهُ الَّذِي خَلَقَ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضَ فِي سِتَّةِ أَيَّامٍ ثُمَّ اسْتَوَى عَلَى الْعَرْشِ يُغْشِي اللَّيْلَ النَّهَارَ يَطْلُبُهُ حَثِيثًا وَالشَّمْسَ وَالْقَمَرَ وَالنُّجُومَ مُسَخَّرَاتٍ بِأَمْرِهِ أَلَا لَهُ الْخَلْقُ وَالْأَمْرُ تَبَارَكَ اللَّهُ رَبُّ الْعَالَمِينَ (54)
Ma'ana: Lallai, Ubangijinku Shi ne Allah wanda Ya halicci Sammai da Qasa cikin kwanaki shida, sannan Ya daidaita akan Al'arshi, Ya na sanya dare ya rufe yini, yana neman sa cikin gaggawa, kuma Rana da Wata da Taurari horarru ne da umurninSa, ku saurara! Da halitta da umurni naSa ne, albarkan Allah Ubangijin talikai ta bayyana (A'araf 54)
(Ma'anan Kalmar) Rabbu Shi ne: Abin bauta.
Dalili akan haka shi ne: fadinSa - Madaukaki
يَا أَيُّهَا النَّاسُ اعْبُدُوا رَبَّكُمُ الَّذِي خَلَقَكُمْ وَالَّذِينَ مِنْ قَبْلِكُمْ لَعَلَّكُمْ تَتَّقُونَ (21) الَّذِي جَعَلَ لَكُمُ الْأَرْضَ فِرَاشًا وَالسَّمَاءَ بِنَاءً وَأَنْزَلَ مِنَ السَّمَاءِ مَاءً فَأَخْرَجَ بِهِ مِنَ الثَّمَرَاتِ رِزْقًا لَكُمْ فَلَا تَجْعَلُوا لِلَّهِ أَنْدَادًا وَأَنْتُمْ تَعْلَمُونَ (22)
Ma'ana: Ya ku mutane ! ku bauta wa Ubangijinku wanda Ya halicce ku, da wadanda suka zo gabanin ku saboda ku kasance masu takawa (21) Wanda Ya sanya muku Kasa shimfidaddiya, Sama kuma ginanniya, Ya kuma saukar da Ruwa daga sama, sannan Ya fitar game da shi 'ya'yan itace don ya kasance abinci gare ku. Saboda haka kada ku sanya wa Allah wasu kishiyoyi alhali kuna sani (Baqara 21-22)
Ibnu kathir – Allah Ya yi masa rahama - ya ce: mahaliccin wadannan abubuwan Shi ne ya cancanci a bauta maSa.
Kuma nau'ukan bautan da Allah Ya yi umurni da su misali: Musulunci da Imani da Ihisani (wato kyautatawa). Kuma daga cikin su akwai; addu'a da alkhauf tsoro da arraja'u (wato tsammanin rahamar Allah) da attawakkul (wato dogaro ga Allah) da arraghbatu (wato kwadayin rahamar Allah) da arrahbatu (wato tsoron ukubar Allah) da alkhushu'u (wato tawalu'u) da alkhshiyatu (wato tsoron Allah sakamakon sanin girmanSa, da al'inabtu (wato maida al'amari gare Shi) da al'isti'anatu (wato neman taimako) da al'isti'adhatu (wato neman tsari) da al'istighathatu (wato neman agaji) da yanka da wanin wadannan cikin nau'ukan bautan da Allah Ya yi umurni da su, dukkan su na Allah ne – Madaukaki.
Dalili akan haka shi ne fadinSa – Madaukaki
وَأَنَّ الْمَسَاجِدَ لِلَّهِ فَلَا تَدْعُوا مَعَ اللَّهِ أَحَدًا (18)
Ma'ana: Kuma lallai masallatai na Allah ne, saboda haka, kada ku kirayi wani tare da Allah. (Jinn 18)
Saboda haka duk wanda ya sarrafar da wata daga cikin su ga wanin Allah, to shi mushiriki ne kafiri.
Dalili akan haka shi ne fadinSa – Madaukaki
وَمَنْ يَدْعُ مَعَ اللَّهِ إِلَهًا آَخَرَ لَا بُرْهَانَ لَهُ بِهِ فَإِنَّمَا حِسَابُهُ عِنْدَ رَبِّهِ إِنَّهُ لَا يُفْلِحُ الْكَافِرُونَ (117)
Ma'ana: Kuma wanda ya kira tare da Allah wasu abubuwan bauta na dabam, bashi da hujja game da shi (kiran) to hisabinsa ya na wurin Ubangijinsa ne kawai, lallai (yadda al'amarin yake shi ne) kafirai basu cin nasara. (Mu'minun 117)
Ya zo a cikin hadisi cewa: addu'a ita ce kwakwalwar ibada.
Dalili akan haka shi ne fadinSa – Madaukaki
وَقَالَ رَبُّكُمُ ادْعُونِي أَسْتَجِبْ لَكُمْ إِنَّ الَّذِينَ يَسْتَكْبِرُونَ عَنْ عِبَادَتِي سَيَدْخُلُونَ جَهَنَّمَ دَاخِرِينَ (60)
Ma'ana: Kuma Ubangijinku Ya ce : Ku kiraye Ni, zan amsa muku, lallai wadanda suke girman kai ga barin bauta miNi, da sannu za su shiga Jahannama suna kaskantattu. (Ghafir 60)
Dalilin akan tsoro kuwa shine fadinSa – Madaukaki
فَلَا تَخَافُوهُمْ وَخَافُونِ إِنْ كُنْتُمْ مُؤْمِنِينَ (175)
Ma'ana: Kada ku ji tsoron su, ku ji tsoro Na in har kun kasance Muminai. (Ali imran 175) .
Dalili akan raja'i shi ne faxinSa – Maxaukaki
فَمَنْ كَانَ يَرْجُوا لِقَاءَ رَبِّهِ فَلْيَعْمَلْ عَمَلًا صَالِحًا وَلَا يُشْرِكْ بِعِبَادَةِ رَبِّهِ أَحَدًا (110)
Ma'ana: Saboda haka duk wanda ke fatan haduwa da Allah, sai ya yi aikin kwarai kuma kada ya hada wani da Allah cikin bauta. (Kahfi 110)
Dalilin tawakkali kuma shi ne fadinSa – Madaukaki
وَعَلَى اللَّهِ فَتَوَكَّلُوا إِنْ كُنْتُمْ مُؤْمِنِينَ (23)
Ma'ana : Kuma ga Allah sai ku dogara, in har kun kasance Muminai. (Ma'ida 23)
Kuma Ya ce:
وَمَنْ يَتَوَكَّلْ عَلَى اللَّهِ فَهُوَ حَسْبُهُ إِنَّ اللَّهَ بَالِغُ أَمْرِهِ قَدْ جَعَلَ اللَّهُ لِكُلِّ شَيْءٍ قَدْرًا (3)
Ma'ana: Kuma wanda ya dogara ga Allah, to Shi ne ma'ishinsa. (Dalak 3)
Dalili akan raghaba (wato kwadayin isa ga abin da ke wurin Allah) da rahaba (wato tsoron Allah wanda ke haifar da nisantan sabonSa, shi nau'i ne na tsoro wanda ke hade da aiki) da khushu'i (wato kankan da kai ga Allah domin girmamawa wanda ke sa bawa ya sallama wa hukuncin Allah da kaddararSa) shi ne fadinSa Madaukaki
إِنَّهُمْ كَانُوا يُسَارِعُونَ فِي الْخَيْرَاتِ وَيَدْعُونَنَا رَغَبًا وَرَهَبًا وَكَانُوا لَنَا خَاشِعِينَ (90)
Ma'ana: Lallai ne su sun kasance suna rige rige a cikin aikin alheri kuma suna kiran Mu don kwadayi da fargaba, kuma sun kasance masu gudun sava maNa. (Ambiya'u 90)
Dalilin khashiya (wato tsoron Allah sakamako saninSa) kuwa shine fadinSa – Madaukaki
فَلَا تَخْشَوْهُمْ وَاخْشَوْنِي (150)
Ma'ana: Kada ku ji tsoron su, ku ji tsoro Na. (Bakara 150)
Dalilin Inaba (wato mayar da al'amura ga Allah) shi ne fadinSa – Madaukaki
وَأَنِيبُوا إِلَى رَبِّكُمْ وَأَسْلِمُوا لَهُ (54)
Ma'ana: Kuma ku maida al'amari ga Ubangijinku kuma ku mika wuya gare Shi. (Zumar 54)
Dalilin neman taimako kuma shi ne fadinSa – Madaukaki
إِيَّاكَ نَعْبُدُ وَإِيَّاكَ نَسْتَعِينُ (4)
Ma'ana: Kai kadai mu ke bauta wa kuma Kai kadai mu ke neman taimakonKa. (Fatiha 5).
Ya zo a cikin hadisi cewa: Idan za ka nemi taimako, to ka nema daga Allah.
Dalilin neman tsari kuma shi ne fadinSa – Madaukaki
قُلْ أَعُوذُ بِرَبِّ الْفَلَقِ (1)
Ma'ana: Ka ce ina neman tsari daga Ubangijin safiya. (Falak1)
قُلْ أَعُوذُ بِرَبِّ النَّاسِ (1)
Ma'ana: Ka ce ina neman tsari daga Ubangijin Mutane. (Nas1)
Dalilin neman agaji kuwa shi ne fadinSa - Madaukaki
إِذْ تَسْتَغِيثُونَ رَبَّكُمْ فَاسْتَجَابَ لَكُمْ (9)
Ma'ana: (Ambata musu ya Muhammadu) Lokacin da ku ke neman agaji daga Ubangijinku sai Ya amsa muku. (Amfal 9)
Dalili akan yanka kuwa shi ne fadinSa - Madaukaki
قُلْ إِنَّ صَلَاتِي وَنُسُكِي وَمَحْيَايَ وَمَمَاتِي لِلَّهِ رَبِّ الْعَالَمِينَ (162) لَا شَرِيكَ لَهُ وَبِذَلِكَ أُمِرْتُ وَأَنَا أَوَّلُ الْمُسْلِمِينَ (163)
Ma'ana: Ka ce: Lallai sallata da yankana da rayuwata da mutuwata duk ga Allah suke Ubangijin talikai (162) Babu wani abokin tarayya gare Shi (An'am 162- 163).
Kuma ya zo a cikin hadisi cewa: Allah Ya la'anci wanda ya yi yanka domin wanin Allah.
Dalilin bakance kuwa shi ne fadinSa – Madaukaki
يُوفُونَ بِالنَّذْرِ وَيَخَافُونَ يَوْمًا كَانَ شَرُّهُ مُسْتَطِيرًا (7)
Ma'ana: Suna cika bakance kuma suna tsoron wani yini wanda sharrinsa ya kasance mai hauhawa ne. (Al'insan 7).
Asali na biyu : Sanin addinin Musulunci da dalilai, wanda shi ne mika wuya da sallamawa ga Allah ta hanyar yin tauhidi, da sakankancewa gare Shi ta hanyar yi (masa) da'a, da barrantuwa daga shirka da ma'abutanta.
Kuma shi matakai ne guda uku: Musulunci, Imani da Ihisani. Ko wane mataki daga cikin su yana da rukunnai.
Rukunnan Musulunci guda biyar ne, shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah kuma Annabi Muhammadu Manzon Allah ne, da tsaida salla, da bada zakka, da azumtan watan Ramadana da hajji zuwa dakin Allah mai alfarma.
Dalilin shahada (wato shaidawa babu abin bautawa bisa cancanta sai Allah) fadinSa – Madaukaki
شَهِدَ اللَّهُ أَنَّهُ لَا إِلَهَ إِلَّا هُوَ وَالْمَلَائِكَةُ وَأُولُو الْعِلْمِ قَائِمًا بِالْقِسْطِ لَا إِلَهَ إِلَّا هُوَ الْعَزِيزُ الْحَكِيمُ (18)
Ma'ana: Allah Ya shaida cewa lallai ne babu abin bautawa da gaskiya sai Shi, kuma mala'iku da ma'abuta ilimi (sun shaida) tsayayye da adalci, babu abin bautawa da gaskiya sai Shi, mabuwayi Mai hikima. (Ali Imrana 18)
Ma'ananta shi ne ; babu abin bautawa bisa cancanta sai Allah.
Cewa " babu abin bautawa bisa cancanta " yana kore dukkanin abinda ake bauta wa koma bayan Allah.
Cewa "sai Allah kuma" yana tabbatar da bauta ne ga Allah Shi kadai babu abokin tarayya gare Shi a cikin bautanSa, kamar yadda baShi da abokin tarayya a cikin mulkinSa. Kuma tafsirin ta (wato Kalmar shahada) wanda ya ke fito da ma'ananta fili shi ne fadinSa – Madaukaki - :
وَإِذْ قَالَ إِبْرَاهِيمُ لِأَبِيهِ وَقَوْمِهِ إِنَّنِي بَرَاءٌ مِمَّا تَعْبُدُونَ (26) إِلَّا الَّذِي فَطَرَنِي فَإِنَّهُ سَيَهْدِينِ (27) وَجَعَلَهَا كَلِمَةً بَاقِيَةً فِي عَقِبِهِ لَعَلَّهُمْ يَرْجِعُونَ (28
Ma'ana: Kuma ka ambaci lokacin da Ibrahim ya ce ga mahaifinsa da mutanensa; lallai ni mai barranta ne daga abin da kuke bauta wa (26) Face wannan da Ya kagi halittata, to lallai Shi ne zai shiryar da ni (27) Kuma shi (Ibrahim) ya sanya ta (wato wannan maganar) mai wanzuwa a cikin zurriyyarsa tsammaninsu su komo daga bata (28) (Zukhruf 26-28).
Da fadinSa –Madaukaki
قُلْ يَا أَهْلَ الْكِتَابِ تَعَالَوْا إِلَى كَلِمَةٍ سَوَاءٍ بَيْنَنَا وَبَيْنَكُمْ أَلَّا نَعْبُدَ إِلَّا اللَّهَ وَلَا نُشْرِكَ بِهِ شَيْئًا وَلَا يَتَّخِذَ بَعْضُنَا بَعْضًا أَرْبَابًا مِنْ دُونِ اللَّهِ فَإِنْ تَوَلَّوْا فَقُولُوا اشْهَدُوا بِأَنَّا مُسْلِمُونَ (64)
Ma'ana: Ka ce ; ya ku ma'abuta littafi! Ku taho zuwa ga wata kalma da take daidaita tsakaninmu daku, ka da mu bauta wa komai face Allah, kuma ka da mu yi masa tarayya da komai, kuma ka da sashinmu ya riki sashi iyayen giji koma bayan Allah, to idan suka juya baya, sai ku ce ; ku shaida cewa mu masu sallamawa ne. (Ali Imrana 64).
Dalili kuma akan shaidawa lallai Muhammadu Manzon Allah ne shi ne fadinSa - Madaukaki
لَقَدْ جَاءَكُمْ رَسُولٌ مِنْ أَنْفُسِكُمْ عَزِيزٌ عَلَيْهِ مَا عَنِتُّمْ حَرِيصٌ عَلَيْكُمْ بِالْمُؤْمِنِينَ رَءُوفٌ رَحِيمٌ (128)
Ma'ana: Lallai ne hakika wani manzo daga cikin ku ya zo muku. Abinda ke wahalar da ku ya na da nauyi a gare shi, mai kwadayin (alheri ne) gare ku, ga muminai (shi) mai tausayi ne mai jin kai. (Attauba 128)
Ma'anan shaidawa Muhammadu Manzon Allah ne shi ne ; yi masa da'a cikin abin da ya yi umurni da shi, da gaskata shi cikin abin da ya bada labari, da nisantan abin da ya yi hani da shi kuma ya yi gargadi, kuma ka da a bauta wa Allah face da abin da ya shar'anta.
Dalilin salla da zakka da tafsirin tauhidi kuma shi ne fadinSa – Madaukaki
وَمَا أُمِرُوا إِلَّا لِيَعْبُدُوا اللَّهَ مُخْلِصِينَ لَهُ الدِّينَ حُنَفَاءَ وَيُقِيمُوا الصَّلَاةَ وَيُؤْتُوا الزَّكَاةَ وَذَلِكَ دِينُ الْقَيِّمَةِ (5)
Ma'ana: Kuma ba'a umurce su ba face su bauta wa Allah su na masu tsarkake addini gare Shi, su na masu karkata zuwa ga addinin gaskiya, kuma su tsai da salla su ba da zakka, kuma wannan shi ne addinin managarta. (Albayyina 5).
Dalilin azumi kuma shi ne fadinSa – madaukaki
يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آَمَنُوا كُتِبَ عَلَيْكُمُ الصِّيَامُ كَمَا كُتِبَ عَلَى الَّذِينَ مِنْ قَبْلِكُمْ لَعَلَّكُمْ تَتَّقُونَ (183)
Ma'ana: Ya ku wadanda suka yi Imani! An wajabta azumi a kan ku kamar yadda aka wajabta shi ga wadanda suka gabace ku tsammanin ku ku samu takawa. (Bakara 183)
Dalilin hajji kuma shi ne fadinSa –Madaukaki
وَلِلَّهِ عَلَى النَّاسِ حِجُّ الْبَيْتِ مَنِ اسْتَطَاعَ إِلَيْهِ سَبِيلًا وَمَنْ كَفَرَ فَإِنَّ اللَّهَ غَنِيٌّ عَنِ الْعَالَمِينَ (97)
Ma'ana: Kuma akwai hajji domin Allah akan Mutane, ga wanda ya samu ikon tafarki zuwa gare shi. (Ali Imran 97).
Marataba ta biyu: Imani, shi rassa ne saba'in da wani abu, mafi daukakan su shi ne; fadin la'ilaha illa llahu mafi karantansu kuma shi ne kawar da abu mai cutarwa daga kan hanya, kunya ma reshe ne daga (rassan) Imani.
Rukunnansa guda shida ne : Ka yi Imani da Allah, da Mala'ikunSa, da LittattafanSa, da ManzanninSa, da Ranan karshe, kuma kayi Imani da kaddara ta alheri da ta sharri. Wadannan su ne rukunnan Imani guda shida.
Dalili akan wadannan rukunnan guda shida shi ne fadinSa Madaukaki
لَيْسَ الْبِرَّ أَنْ تُوَلُّوا وُجُوهَكُمْ قِبَلَ الْمَشْرِقِ وَالْمَغْرِبِ وَلَكِنَّ الْبِرَّ مَنْ آَمَنَ بِاللَّهِ وَالْيَوْمِ الْآَخِرِ وَالْمَلَائِكَةِ وَالْكِتَابِ وَالنَّبِيِّينَ (177)
Ma'ana: Bai zama addini ba, kawai don kun juyar da fuskokin ku bangaren Gabas da Yamma, sai dai addini (yana) ga wanda ya yi Imani da Allah da Ranar lahira da Mala'iku da da Littattafai da annabawa. (Bakara 177).
Dalilin kaddara kuma shi ne fadinSa – Madaukaki
إِنَّا كُلَّ شَيْءٍ خَلَقْنَاهُ بِقَدَرٍ (49)
Ma'ana: Lallai Mu ko wane abu Mun halicce shi ne a kan kaddara. (kamar 49)
Martaba ta uku: Ihsani (wato kyautatawa), rukuni ne guda daya, shi ne ; ka bauta wa Allah kamar kana ganin Sa, idan kai baka ganin Sa to fa Shi Yana ganinka.
Dalili akan haka fadinSa – Madaukaki
إِنَّ اللَّهَ مَعَ الَّذِينَ اتَّقَوْا وَالَّذِينَ هُمْ مُحْسِنُونَ (128)
Ma'ana: Lallai Allah Yana tare da wadanda suka yi takawa da wadanda suke masu kyautatawa. (Nahli 128).
Da fadinSa – Madaukaki
وَتَوَكَّلْ عَلَى الْعَزِيزِ الرَّحِيمِ (217) الَّذِي يَرَاكَ حِينَ تَقُومُ (218) وَتَقَلُّبَكَ فِي السَّاجِدِينَ (219)
Ma'ana: Kuma ka dogara ga Mabuwayi Mai jin kai (217) Wanda Ya ke ganin ka yayin da ka ke tashi (218) Da kuma jujjuyawarka a cikin masu sujjada (Shu'ara'u 219).
Da fadinSa – Madaukaki
وَمَا تَكُونُ فِي شَأْنٍ وَمَا تَتْلُو مِنْهُ مِنْ قُرْآَنٍ وَلَا تَعْمَلُونَ مِنْ عَمَلٍ إِلَّا كُنَّا عَلَيْكُمْ شُهُودًا إِذْ تُفِيضُونَ فِيهِ (61)
Ma'ana: Kuma ba ka kasance a cikin wani sha'ani ba, kuma ba ka karanta wani abin karatu daga gare shi ba, kuma ba ku aikata wani aiki ba face Mun kasance halarce a lokacin da (ku ke sakin baki) kuna ta zuba a cikinsa. (Yunus 61)
Dalili daga sunna kuwa shine mashhurin hadisin nan na Jibril daga Umar dan Khaddab (Allah Ya kara masa yarda) ya ce :
"بينما نحن جلوس عند رسول الله صلى الله عليه وسلم إذ طلع علينا رجل، شديد بياض الثياب، شديد سواد الشعر، لا يرى عليه أثر السفر، ولا يعرفه منا أحد، حتى جلس إلى النبي صلى الله عليه وسلم، فأسند ركبتيه إلى ركبتيه، ووضع كفيه على فخذيه، وقال: يا محمد! أخبرني عن الإسلام. قال: أن تشهد أن لا إله إلا الله، وأن محمدا رسول الله، وتقيم الصلاة، وتؤتي الزكاة، وتصوم رمضان، وتحج البيت إن استطعت إليه سبيلا. فقال: صدقت. فعجبنا له يسأله ويصدقه. قال: فأخبرني عن الإيمان. قال: أن تؤمن بالله وملائكته وكتبه ورسله واليوم الآخر، وتؤمن بالقدر خيره وشره. قال: صدقت. قال: فأخبرني عن الإحسان. قال: أن تعبد الله كأنك تراه، فإن لم تكن تراه فإنه يراك. قال: فأخبرني عن الساعة. قال: ما المسؤول عنها بأعلم من السائل. قال: فأخبرني عن أماراتها. قال: أن تلد الأمة ربتها، وأن ترى الحفاة العراة العالة رعاء الشاء يتطاولون في البنيان. قال فمضى، فلبثنا مليا. فقال: يا عمر أتدري من السائل؟ قلت: الله ورسوله أعلم. قال: هذا جبرائيل أتاكم يعلمكم أمر دينكم".
Ma'ana: Yayin da mu ke zaune a wurin manzon Allah – tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi – sai wani mutum ya bullo mana, mai tsananin farin tufafi, mai tsananin bakin gashi, ba'a ganin wata alama ta tafiya a tare da shi, kuma babu wanda ya san shi daga cikin mu, har sai da ya zauna a gaban manzon Allah – tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi – sai ya jingina gwiwoyinsa da gwiwoyinsa (wato gwiwoyin Annabi) kuma ya dora tafukansa a kan cinyoyinsa (wato cinyoyin Annabi) kuma ya ce ; ya Muhammad! Bani labari game da Musulunci, sai ya ce ; shi ne ; ka shaida babu abin bauta wa bisa cancanta sai Allah, kuma Muhammadu ManzonSa ne, kuma ka tsai da salla, kuma ka bada zakka, kuma ka azumci watan Ramadana, kuma ka yi aikin hajji zuwa dakin (ka'aba) in ka samu iko zuwa gare shi. Sai ya ce ; ka yi gaskiya, sai mu ka yi mamakin sa, ya na tambayan sa kuma ya na gaskata shi.
Ya ce ; bani labari game da Imani, sai ya ce ; shi ne ka yi Imani da Allah, da Mala'ikunSa da littattafanSa, da ManzanninSa da Rananr karshe, kuma ka yi Imani da kaddara ta alheri da ta sharri. Ya ce ; ka yi gaskiya, to ba ni labari game da kyautatawa, sai ya ce ; shi ne ka bauta wa Allah kamar ka na ganinSa, duk da cewa kai ba ka ganinSa, to Shi fa Ya na ganin ka. Sai ya ce ; ba ni labari game da tashin Alkiyama, ya ce ; wanda ake tambayan bai fi mai tambayan sani ba. Sai ya ce ; to ba ni labari game da alamominta, ya ce; Kuyanga za ta haifi Uwargijiyarta, kuma za ka ga marasa takalma Huntaye matalauta masu kiwon awaki suna gasan tsawaitawa cikin ginegine. Sai ya wuce, sai muka zauna na tsawon lokaci, sai (Annabi) ya ce ; ya kai Umar ! ka san mai tambayan nan? Ya ce ; sai na ce : Allah da manzonSa ne mafiya sani, ya ce; wannan Jibrilu ne ya zo ne domin ya karantar daku addininku.
Asali na uku: sanin Annabinku Muhammadu –tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ; shi ne Muhammadu dan Abdullahi dan Abdulmuddalib dan Hashim, shi Hashim kuma daga (kabilar) kuraishawa yake, kuraishawa kuma (kabila ce) daga (kabilun) larabawa, larabawa kuma daga zurriyyan (Annabi) Isma'il dan (Annabi) Ibrahim suke - badadin Allah – mafificin salati da sallama su tabbata a gare shi da Annabinmu –.
Ya (rayu) shekaru sittin da uku, arba'in daga ciki kafin Annabta, ashirin da uku kuma ya na Annabi kuma manzo, an maida shi Annabi ne da (saukar) ikra' an kuma maida shi manzo ne da (saukar) Muddahthtir, garinsa shi ne Makka, kuma ya yi hijira zuwa Madina. Allah Ya aiko shi da gargadi game da shirka, kuma yana kira zuwa ga tauhidi.
Dalili shi ne fadinSa – Madaukaki
يَاأَيُّهَا الْمُدَّثِّرُ (1) قُمْ فَأَنْذِرْ (2) وَرَبَّكَ فَكَبِّرْ (3) وَثِيَابَكَ فَطَهِّرْ (4) وَالرُّجْزَ فَاهْجُرْ (5) وَلَا تَمْنُنْ تَسْتَكْثِرُ (6) وَلِرَبِّكَ فَاصْبِرْ (7)
Ma'ana: Ya kai wanda ya lulluba cikin mayafi! (1) Tashi ka yi gargadi (2) Ubangijinka kuma sai ka girmama Shi (3) Tufafinka kuma sai ka tsarkake su (4) Gumaka kuma sai ka kaurace musu (5) Kuma ka da ka yi kyauta kana neman kari (6) Kuma saboda Ubangijinka sai ka yi hakuri (7) Muddahthtir 1-7).
Ma'anan: "Tashi ka yi gargadi" shi ne, ya yi gargadi ga barin shirka kuma ya yi kira zuwa tauhidi.
(Ma'anan): "Ubangijinka kuma sai ka girmama Shi" shi ne; ka girmama Shi da tauhidi.
(Ma'anan): "Tufafinka kuma ka tsarkake su" shi ne; ka tsarkake ayyukanka daga shirka.
(Ma'anan): "Gumaka kuma ka kaurace musu" Arrujzu su ne gumaka, kaurace musu shi ne ; barin su da ma'abutan su, da barrantuwa daga gare su da ma'abutan su, da gaba da su da ma'abutan su, da rabuwa da su da ma'abutan su.
Ya dauki tsawon shekaru goma a kan wannan, ya na kira zuwa ga tauhidi, bayan (shekaru) goman nan kuma sai a ka yi mi'iraji da shi zuwa sama kuma aka farlanta masa salloli biyar. Ya yi salla a Makka shekaru uku, bayan su kuma aka umurce shi da yin hijira zuwa Madina.
Hijira ita ce : kaura daga kasar shirka zuwa kasar Musulunci.
Hijira wajiba ce a kan wannan al'ummar daga kasar shirka zuwa kasar Musulunci, kuma ta na nan har zuwa tashin Alkiyama.
Dalili shi ne fadinSa – Madaukaki
إِنَّ الَّذِينَ تَوَفَّاهُمُ الْمَلَائِكَةُ ظَالِمِي أَنْفُسِهِمْ قَالُوا فِيمَ كُنْتُمْ قَالُوا كُنَّا مُسْتَضْعَفِينَ فِي الْأَرْضِ قَالُوا أَلَمْ تَكُنْ أَرْضُ اللَّهِ وَاسِعَةً فَتُهَاجِرُوا فِيهَا فَأُولَئِكَ مَأْوَاهُمْ جَهَنَّمُ وَسَاءَتْ مَصِيرًا (97) إِلَّا الْمُسْتَضْعَفِينَ مِنَ الرِّجَالِ وَالنِّسَاءِ وَالْوِلْدَانِ لَا يَسْتَطِيعُونَ حِيلَةً وَلَا يَهْتَدُونَ سَبِيلًا (98) فَأُولَئِكَ عَسَى اللَّهُ أَنْ يَعْفُوَ عَنْهُمْ وَكَانَ اللَّهُ عَفُوًّا غَفُورًا (99)
Ma'ana: Lallai ne wadanda Mala'iku su ka karbi rayukansu alhali suna masu zaluntan kansu, suka ce (musu) a cikin me ku ka kasance? Sai su ka ce ; mun kasance wadanda aka raunana a bayan kasa, suka ce ; ashe kasar Allah ba ta kasance mayalwaciya ba domin ku yi hijira a cikinta? To wadannan makomar su ita ce Jahannama, kuma ta munana ta zama makoma (97) Face wadanda aka raunana daga mazaje da mata da yara wadanda ba su iya yin wata dabara kuma ba su shiryuwa ga hanya (98) To wadannan akwai tsammanin Allah Ya yi afuwa gare su, kuma Allah Ya kasance Mai yawan Afuwa ne Mai yawan Gafara. (99) (Nisa'i 97-99)
Da fadinSa – Madaukaki
يَا عِبَادِيَ الَّذِينَ آَمَنُوا إِنَّ أَرْضِي وَاسِعَةٌ فَإِيَّايَ فَاعْبُدُونِ (56)
Ma'ana: Ya ku bayiNa wadanda suka yi Imani! Lallai fa kasaTa mai yalwa ce, saboda haka Ni kadai za ku bauta wa (Ankabut 56).
Albaghwai – Allah Ya yi masa rahama - ya ce ; sababin saukar wannan ayar game da wasu Musulmai ne, da suke Makka basu yi hijira ba, Allah Ya kira su da sunan Imani.
Dalili kuma akan Hijira daga sunna shi ne fadinsa – tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi
«لا تنقطع الهجرة حتى تنقطع التوبة، ولا تنقطع التوبة حتى تطلع الشمس من مغربها»
Ma'ana:Hijira ba za ta yanke ba har sai tuba ta yanke, tuba kuwa ba za ta yanke ba har sai Rana ta fito daga mafadarta.
Yayin da ya samu tabbatuwa a Madina, sai aka umurce shi da sauran shari'a'o'in Musulunci, kamar su zakka da azumi da hajji da jihadi da kiran salla da umurni da kyakkyawa da hani ga mummuna da wanin wadannan daga shari'o'in Musulunci.
Ya dauki (tsawon) shekaru goma a wannan, bayansa kuma sai ya rasu – tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi – amma addininsa na nan, ga addininsa nan babu wani alheri face ya shiryar da al'umma zuwa gare shi, kuma babu wani sharri face ya gargade ta daga gare shi. Alherin da ya shiryar zuwa gare shi shi ne; tauhidi, da dukkanin abin da Allah Ya ke so kuma Ya yarda da shi. Kuma sharrin da ya yi gargadi akan sa shi ne ; shirka da duk abin da Allah baYa so kuma Ya ke kinsa.
Allah Ya aiko shi ga dukkan Mutane , kuma Ya farlanta yi masa xa'a a kan dukkan Aljannu da Mutane.
Dalili akan haka shi ne fadin Allah – Madaukaki
قُلْ يَا أَيُّهَا النَّاسُ إِنِّي رَسُولُ اللَّهِ إِلَيْكُمْ جَمِيعًا (158)
Ma'ana: Ka ce ; ya ku mutane ! lallai ne ni Manzon Allah ne zuwa gare ku gaba daya. (A'raf 158)
Kuma Ya kammala mana addini.
Dalili akan haka shi ne fadinSa – Madaukaki
الْيَوْمَ أَكْمَلْتُ لَكُمْ دِينَكُمْ وَأَتْمَمْتُ عَلَيْكُمْ نِعْمَتِي وَرَضِيتُ لَكُمُ الْإِسْلَامَ دِينًا (3)
Ma'ana: A yau Na kammala muku addininku, kuma Na cika ni'imaTa a kan ku, kuma Na yarda da Musulunci ya zama addini a gare ku. (Ma'ida 3)
Dalili akan mutuwarsa – tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi kuma shi ne fadinSa – Madaukaki
إِنَّكَ مَيِّتٌ وَإِنَّهُمْ مَيِّتُونَ (30) ثُمَّ إِنَّكُمْ يَوْمَ الْقِيَامَةِ عِنْدَ رَبِّكُمْ تَخْتَصِمُونَ (31)
Ma'ana: Lallai kai mai mutuwa ne kuma suma lallai masu mutuwa ne (30) Sa'annan lallai ku a ranar kiyama, a wurin Ubangijinku za ku yi ta yin husuma. (31) (Zumar 30-31)
Kuma mutane idan su ka mutu za'a tashe su, dalili shine fadinSa – Madaukaki
مِنْهَا خَلَقْنَاكُمْ وَفِيهَا نُعِيدُكُمْ وَمِنْهَا نُخْرِجُكُمْ تَارَةً أُخْرَى (55)
Ma'ana: Daga cikinta Mu ka halitta ku, kuma cikinta za Mu maida ku, kuma daga cikinta za Mu sake fidda ku a wani lokacin na dabam. (daha 55)
Da fadinSa – Madaukaki
وَاللَّهُ أَنْبَتَكُمْ مِنَ الْأَرْضِ نَبَاتًا (17) ثُمَّ يُعِيدُكُمْ فِيهَا وَيُخْرِجُكُمْ إِخْرَاجًا (18)
Ma'ana: Kuma Allah ne Ya tsirar da ku daga kasa tsirarwa (17) Sa'annan Ya maida ku cikinta kuma Ya fitar da ku fitarwa (18) (Nuh 17-18)
Bayan an tayar da su kuma, su wadanda za'a yiwa hisabi ne kuma a saka musu game da ayyukansu.
Dalili akan haka shi ne fadinSa – Madaukaki
لِيَجْزِيَ الَّذِينَ أَسَاءُوا بِمَا عَمِلُوا وَيَجْزِيَ الَّذِينَ أَحْسَنُوا بِالْحُسْنَى (31)
Ma'ana : Domin Ya saka wa wadanda suka munana da abin da su ka aikata, kuma Ya saka wa wadanda suka kyautata da sakamako mafi kyau. (Najm 31)
Kuma duk wanda ya karyata tashin kiyama ya kafirta.
Dalili akan haka shi ne fadinSa – Madaukaki
زَعَمَ الَّذِينَ كَفَرُوا أَنْ لَنْ يُبْعَثُوا قُلْ بَلَى وَرَبِّي لَتُبْعَثُنَّ ثُمَّ لَتُنَبَّؤُنَّ بِمَا عَمِلْتُمْ وَذَلِكَ عَلَى اللَّهِ يَسِيرٌ (7)
Ma'ana: Wadanda suka kafirta suna riya cewa; ba za a tayar da su ba (bayan mutuwa), ka ce ; ina rantsuwa da Ubangijina, lallai tabbas za'a tayar da ku, sa'annan kuma za a ba ku labari game da abin da kuka aikata, kuma wannan a wurin Allah, abu ne mai sauki. (Taghabun 7)
Kuma dukkanin manzanni an aiko su ne suna masu albishir kuma masu gargadi.
Dalili shi ne fadinSa – Madaukaki
رُسُلًا مُبَشِّرِينَ وَمُنْذِرِينَ لِئَلَّا يَكُونَ لِلنَّاسِ عَلَى اللَّهِ حُجَّةٌ بَعْدَ الرُّسُلِ وَكَانَ اللَّهُ عَزِيزًا حَكِيمًا (165)
Ma'ana: Manzanni masu bayar da bushara kuma masu gargadi domin kada wata hujja ta kasance ga mutane a kan Allah bayan Manzanni. (Nisa'i 165)
Kuma na farkonsu shi ne Nuhu – amincin Allah ya tabbata a gare shi – na karshensu kuma shi ne (Annabi) Muhammad – tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi
Dalili a kan cewa na farkonsu shi ne Nuhu– amincin Allah ya tabbata a gare shi – fadinSa – Madaukaki
إِنَّا أَوْحَيْنَا إِلَيْكَ كَمَا أَوْحَيْنَا إِلَى نُوحٍ وَالنَّبِيِّينَ مِنْ بَعْدِهِ (163)
Ma'ana: Lallai ne Mu Mun yi wahayi zuwa gare ka kamar yadda Mu ka yi wahayi zuwa ga Nuhu da annbawan da su ka zo bayan sa. (Annisa'i 163)
Kuma ko wace al'umma Allah Ya aika manzo zuwa gare ta tun daga Nuhu har zuwa Muhammad, ya na umuratan su da bautan Allah Shi kadai kuma ya na hana su bautan dagutu.
Dalili akan haka shine fadinSa – Madaukaki
وَلَقَدْ بَعَثْنَا فِي كُلِّ أُمَّةٍ رَسُولًا أَنِ اُعْبُدُوا اللَّهَ وَاجْتَنِبُوا الطَّاغُوتَ (36)
Ma'ana: Kuma lallai ne, hakika Mun aika a cikin ko wace al'umma da wani manzo, (ya na cewa) ku bauta wa Allah kuma ku nisanci Dagutu. (Nahal 36)
Kuma Allah Ya farlanta wa dukkan bayi kafirce wa dagutu da kuma Imani da Allah. Ibnul kayyim – Allah madaukaki Ya yi masa rahama ya ce ; Dagutu shi ne duk wani abu da bawa ya wuce iyakansa game da shi, daga abin da ake bauta wa ko abin da ake bi ko abin da ake yiwa da'a, kuma dagutai suna da yawa, manya manyan su guda biyar ne : Ibilisu – Allah Ya tsine masa – da wanda aka bauta wa alhali yana mai yarda (da bautan), da wanda ya kirayi mutane zuwa ga bautan kansa, da wanda ya yi da'awar sanin wani abu daga ilimin gaibu, da wanda ya yi hukunci da sabanin abin da Allah Ya saukar.
Dalili akan haka shine fadinSa – Madaukaki
لَا إِكْرَاهَ فِي الدِّينِ قَدْ تَبَيَّنَ الرُّشْدُ مِنَ الْغَيِّ فَمَنْ يَكْفُرْ بِالطَّاغُوتِ وَيُؤْمِنْ بِاللَّهِ فَقَدِ اسْتَمْسَكَ بِالْعُرْوَةِ الْوُثْقَى لَا انْفِصَامَ لَهَا وَاللَّهُ سَمِيعٌ عَلِيمٌ (256)
Ma'ana : Babu tilastawa a cikin addini,hakika shiriya ta bayyana daga bata,saboda haka wanda ya kafirta da dagutu kuma ya yi imani da Allah, to hakika ya yi riko da igiya amintacciya babu yankewa a gare ta, kuma Allah Mai ji ne Masani. (Bakara 256)
Kuma wannan shi ne ma'anan La'ilaha illa llahu, kuma ya zo a cikin hadisi (cewa) :"Kan al'amari shi ne Musulunci, gimshikinsa kuma shi ne salla, tsololuwar tozonsa kuma shi ne Jihadi saboda Allah.
Allah Shi ne mafi sani
Allah Ya yi salati da sallama ga (Annabi) Muhammadu da Alayensa da sahabbansa