ÇáãÓÇÚÏ ÇáÔÎÕí ÇáÑÞãí

ãÔÇåÏÉ ÇáäÓÎÉ ßÇãáÉ : Sharhin arba'una hadith hadisi na daya daga malam ja'afar allah ya yi masa rahama


ØÇåÑ ÌÈÑíá Ïßæ
_12 _April _2014åÜ ÇáãæÇÝÞ 12-04-2014ã, 12:59 AM
SHARHIN ARBA'UNA HADITH HADISI NA DAYA DAGA MALAM JA'AFAR ALLAH YA YI MASA RAHAMA
An karbo daga sarkin muminai, baban hafs Umar dan Khaddabi (Allah Ya kara masa yarda) yace: na ji manzon Allah (SAW) yana cewa: "lallai kadai ayyuka suna tare da niyyoyinsu, kuma lallai kowane mutum yana samun sakamakon abin da yayi niyya ne (a zuciyarsa). Wanda duk hijirarsa ta kasance saboda Allah da manzonsa, to hijirarsa tana ga Allah da manzonSa wanda yayi hijira saboda duniya da zai sameta ko dan wata mace da zai aure ta, to hijirarsa naga ga abin da yai hijira saboda shi.
Shugabanni biyu na maruwaita hadisai ne suka rawaito shi. Sune Muhammad dan isma’ila dan Ibrahim dan Mugirata da Bardizbah al-Bukhari al-ju’ufy (1,54) da abul Hussain Muslimu dan Hajjaju dan Muslimu Alkushairiy Annaisaburiy (1907) a cikin ingantatun littattafansu wadan da sune mafi ingancin littattafai da aka rubuta.

SHARHI;
Wannan hadisi yana daya daga cikin hadisai mafiya shahara daga cikin hadisian Annabi (SAW) mutum daya ne ya ji wannan hadisi daga bakin Annabi (SAW) shi ne Umar dan Khaddab mutum daya ne yaji shi daga Umar dan Khaddab shi ne Alkama bin Wakkas Allaithiyyi haka ma mutum daya ne yaji shi daga wajen Alkawama shi ne Muhammad bin Ibrahim Attaimiyyi mutum daya ne tak ya ji shi daga wajen Muhammad bin Ibrahim attaimiyyi, shine Yahaya bin sa’id Al-ansariyyi, daga kan wanna bawan allah Yahay bin Sa'id Al-ansariryyi ne wanna hadisi ya shahara.
Domin shi daya sama mutum dari biyu ne suka rawaito hadisin a wajen sa wannan itace hanyar da ta inganta cikin hanyoyin wanna hadis. Wasu malamai sukan rawaioto shi daga Sa’ad bin abi Wakkas, amma bai inganta ba wanna it ace (kadai) hanya ingantataciya da ta tabbata. Daga cikin mutanen da suka ji wanna hadisi a wurinsa akkwai Imamu Malik bin anas da Is'hak bin Rahawaihi da Ahamd bin Hambali da Shu’ub da Sufiyan bin Sa'id Aththauriy da sufiyan bin Uyayna.
Imamul Buikhari ya mayar da wannan hadisin ya zamanto shi ne gabatarwar littafinsa sahihul bukharri. Bayan bismillah sai ya kawo wanna hadisin don ya mayar da shi gabatarwa ta littafin sa domin ya nuna wa mutane cewa a wajen Allah sai in ya zamanto ka yi shi da kyakkyawar niyya, kuma domin ya nuna mana tsadar iklasi a cikin ayyuka. Malamai da dama sun yi Magana kan matsayin wanna hadisi har Abdurahaman bin Mahdi ya ke cewa; da zan sami dammar wallafa littafi mai babi –babi da hukunce hukunce, to da sai na mayar da wanna hadisi ya zamanto shi ne gabatarwar kowane babi,” Imamush Shafi’i yana cewa; shi wanna hadisi shi ne sulusin illimi gaba daya. Abin da ake nufi da sulusi illim kashi daya bisa ukun illimi, sannan ya ci gaba da cewa zai iya shi ga babi har guda saba’in daga cikin babin fikhu.
Lafazin hafs daya zo awannan hadisi, a larebce, daya ne daga cikin sunayen zaki sukan ce masa Hafs, sukan ce Asad sukan ce masa Aglab sukan ce Hizabr. Zaki yana da sunaye dai dai har guda dari idan ka duba kamus an ace wa Umar dan Khaddab Abu Hafs saboda jaruntakarsa, kuma yana alfahari da wannan da cewa abu Hafsin.
Dangane kuwa da lakabin amirul mu’umina umar dan khaddab shi ne mutum na farko daga cikin sahabbai wanda suka yi shugabanci a bayan annabi (SAW) da ake yi wa lakabi da amirul mu’uminina(RA).
MAS'ALA
Dangane da fadinsa (SAW) cewa “Lallai kadai ayyuka suna tare da niyyoyinsu…..” a nan wurin duk aiki ne ake yi wa niyya ko kuma akwai wadanda ba ayi musu niya?
Wadansu malamai sun ce akwai wadanda ake yi masu niyya akwai wadanda ba ayi nmusu niyya, abinda ake nufi da ayyuka a nan kuwa shi ne ayyukan da suka shafi shari’a kai tsaye kamar alwala da sallah da zakka da azumi da dukkan aikin da yake ibada ne tsantsa. To irin wadannan ayyukan sune suke bukatar niyya. Amma akwai ayyukan da suka shafi dabi’arka ta dan adam ta yau da gobe kamar zama da tashi da kwanciya da kishingida da cin abinci da shan ruwa da sanya tafafi da dai sauransu. Wadanna duk sunansu ayyuka amma basa bakatar niyya. Don zaka zauna ba wani bukatar niyyar zama don zaka tashi ba bukatar sai kayi niyyar tashi. Ashe lafazin ayyuka a nan ba ayyuka gaba daya ake nufi ba, abin da ake nufi shi ne dukkan ayyukan da suke shari’a ce tace a yi su. To irin wadannan ayyuka sune suke da bukatar niyya.
Hadisi yayi maganar hijira abin da ake nufi da hijira