تسجيل الدخول

مشاهدة النسخة كاملة : Darasi na talatin da daya: Tarjaman tafsirin suratu- annasr daga littafin: Attafisul muyassar


طاهر جبريل دكو
_3 _April _2014هـ الموافق 3-04-2014م, 02:20 PM
إِذَا جَاءَ نَصْرُ اللَّهِ وَالْفَتْحُ (1)
Idan taimakon Allah ya zo da kuma cin Makka

Sharhi: Ya kai wannan manzon, idan ka samu nasara akan kafiran kuraishawa, kuma ka ci Makka (da yaki).
وَرَأَيْتَ النَّاسَ يَدْخُلُونَ فِي دِينِ اللَّهِ أَفْوَاجًا (2)
Kuma kaga mutane suna shiga addinin Allah jama'a jama'a.

Sharhi: Kuma kaga da yawa daga cikin mutane suna shiga musulunci jama'a jama'a.
فَسَبِّحْ بِحَمْدِ رَبِّكَ وَاسْتَغْفِرْهُ إِنَّهُ كَانَ تَوَّابًا (3)
Saboda haka kayi tasbihi game da godiya ga Ubangijinka, kuma ka nemi gafararSa, lallai Shi Ya kasance mai yawan karban tuba ne.

Sharhi: Idan hakan ya faru sai kayi shirin saduwa da Ubangijinka ta hanyar yawaita tasbihi da godiya da yawaita neman gafararSa, lallai Shi mai yawan karban tuba ne na masu tasbihi da masu neman gafara, Yana karban tubansu kuma Yana jin kansu.