المساعد الشخصي الرقمي

مشاهدة النسخة كاملة : Darasi na talatin: Tarjaman tafsirin suratul kafirun daga littafin: Attafisul muyassar


طاهر جبريل دكو
_3 _April _2014هـ الموافق 3-04-2014م, 02:13 PM
قُلْ يَا أَيُّهَا الْكَافِرُونَ (1)
Kace yaku wadannan kafiran.

Sharhi: Kace – ya kai wannan manzon – ga wadanda suka kafirce ga Allah da manzonSa: ya ku wadanda suka kafice wa Allah!
لَا أَعْبُدُ مَا تَعْبُدُونَ (2)
Bana bautawa abinda kuke bauta wa.

Sharhi: Bana bauta wa abinda kuke bauta wa na gumaka da ababen bauta na karya.
وَلَا أَنْتُمْ عَابِدُونَ مَا أَعْبُدُ (3)
Kuma ku ba masu bauta bane ga wanda bautawa ba

Sharhi: Kuma ku ba masu bauta bane ga abin bauta daya, Shine Allah Ubangijin talikai, wanda Shi kadai Ya cancanci bauta.
وَلَا أَنَا عَابِدٌ مَا عَبَدْتُمْ (4)
Kuma ni ba zan zama mai bauta wa abinda kuke bauta wa ba.

Sharhi: Kuma ni ba zan bauta wa abinda kuke bauta wa bane na gumaka da ababen bauta na karya.
وَلَا أَنْتُمْ عَابِدُونَ مَا أَعْبُدُ (5)
Kuma ku ma ba zaku zama masu bautawa wanda nake bauta wa ba.

Sharhi: Kuma, kuma nan gaba ba masu bauta bane ga wanda nake bauta wa.

Sharhi: Wannan ayar ta sauka ne game da wasu mutane sanannu daga cikin mushirikai, hakika Allah Ya san cewa baza suyi imani ba har abada.
لَكُمْ دِينُكُمْ وَلِيَ دِينِ (6)
Addininku (na kafirci) yana gare ku, kuma nima addinina (na musulunci yana gareni).

Sharhi: Addinin da kuka doge akan binsa yana gare ku, kuma nima addini na wanda bana bidan waninsa yana gare ni.