تسجيل الدخول

مشاهدة النسخة كاملة : Darasi na ashirin da tara: Tarjaman tafsirin suratul kauthar daga littafin: Attafisul muyassar


طاهر جبريل دكو
_3 _April _2014هـ الموافق 3-04-2014م, 02:07 PM
إِنَّا أَعْطَيْنَاكَ الْكَوْثَرَ (1)
Lallai ne Mu Munyi maka kyauta mai yawa.

Sharhi: Lallai ne Mun baka alkhairi mai yawa - ya kai wannan annabin – a duniya da lahira, daga cikin hakan akwai tafkin alkausara a cikin aljanna wanda baki bakinsa rumfuna ne na lu'u lu'u mai fafaffiyiar tsakiya, lakansa kuma almiski ne.
فَصَلِّ لِرَبِّكَ وَانْحَرْ (2)
Saboda haka, kayi sallah domin Ubangijinka kuma kayi yanka (dominSa)

Sharhi: Saboda haka ka tsarkake sallarka dukkanin ta ga Ubangijinka, kuma ka yanka abin yankan ka domin (bauta gare Shi) kuma da sunanSa Shi kadai.
إِنَّ شَانِئَكَ هُوَ الْأَبْتَرُ (3)
Lallai mai aibanta ka shine mai yankakkiyar albarka.

Sharhi: Lallai ne mai fushi da abin da kazo dashi na shiriya da haske shine mai yankakken baya, wanda ya yanke daga dukkan alkhairi.