تسجيل الدخول

مشاهدة النسخة كاملة : Darasi na ashirin da takwas: Tarjaman tafsirin suratul ma'una daga littafin: Attafisul muyassar


طاهر جبريل دكو
_3 _April _2014هـ الموافق 3-04-2014م, 02:01 PM
أَرَأَيْتَ الَّذِي يُكَذِّبُ بِالدِّينِ (1)
Shin kaga wanda yake karyatawa game da sakamako?

Sharhi: Shin kaga wanda yake karyatawa game da tashin alkiyama da sakamako?
فَذَلِكَ الَّذِي يَدُعُّ الْيَتِيمَ (2)
To wannan shine ke tunkude maraya (daga hakkinsa)

Sharhi: To wannan shine ke tunkude maraya - wanda mahaifinsa ya mutu alhali yana karami – daga hakkinsa cikin tsanani da mugunta; saboda kekashewar zuciyarsa.
وَلَا يَحُضُّ عَلَى طَعَامِ الْمِسْكِينِ (3)
Kuma baya kwadaitarwa bisa ciyar da miskini.

Sharhi: Kuma baya kwadaitar da waninsa bisa ciyar da mabukaci wanda bai mallaki abinda zai wadatar da shi ya biya masa bukata ba, to yaya zai iya ciyar dashi da kansa?
فَوَيْلٌ لِلْمُصَلِّينَ (4)
To tsananin azaba ya tabbata ga masallatan.

الَّذِينَ هُمْ عَنْ صَلَاتِهِمْ سَاهُونَ (5)
Wadanda suke masu shagala daga sallarsu.

Sharhi: To tsananin azaba ya tabbata ga masallatan da suke wasa da sallarsu, basu tsaida ita a fuskar da ta dace, kuma basu aiwatar da ita a kan lokacinta.
الَّذِينَ هُمْ يُرَاءُونَ (6)
Wadanda suke yin riya.

Sharhi: Wadana suke bayyana ayyukan alkhairi don nunawa mutane.
وَيَمْنَعُونَ الْمَاعُونَ (7)
Kuma suke hana taimako.

Sharhi: Kuma suna hana aron abinda bada aronsa baya cutar da shi kamar kwanuka da waninsu, su basu kyautata bautar Ubangijinsu ba, kuma su basu kyautata ga halittunSa ba.