تسجيل الدخول

مشاهدة النسخة كاملة : Darasi na ashirin da shida: Tarjaman tafsirin suratul fil daga littafin: Attafisul muyassar


طاهر جبريل دكو
_3 _April _2014هـ الموافق 3-04-2014م, 01:30 PM
أَلَمْ تَرَ كَيْفَ فَعَلَ رَبُّكَ بِأَصْحَابِ الْفِيلِ (1)
Ashe baka ga yadda Ubangijinka Ya aikata da ma'butan giwa ba?

Sharhi: Shin baka sani bane – ya kai wannan manzon – yadda Ubangijinka Ya aikata da ma'abuta giwa ba? Abraha bahabashen nan da shi da rundunarsa wadanda suka yi nufin rusa (dakin) ka'aba mai albarka?
أَلَمْ يَجْعَلْ كَيْدَهُمْ فِي تَضْلِيلٍ (2)
Ashe bai sanya kaidinsu cikin tabewa ba?

Sharhi: Shin bai sanya abinda suka shirya na sharri cikin asara da baci ba?
وَأَرْسَلَ عَلَيْهِمْ طَيْرًا أَبَابِيلَ (3)
Kuma Ya aiko musu da tsuntsaye jama' jama'a.

تَرْمِيهِمْ بِحِجَارَةٍ مِنْ سِجِّيلٍ (4)
Suna jifan su da duwatsu na yunbun wuta.

Sharhi: Kuma Ya aika musu da tsuntsaye jama'a jama'a wasu na biye da wasu, suna jifan su da wasu irin duwatsu da suka sandare.
فَجَعَلَهُمْ كَعَصْفٍ مَأْكُولٍ (5)
Sai Ya sanya su kamar karmami da aka cinye.

Sharhi: Sai Ya sanya su rududdugaggu kamar busassun ganyayen da dabbobi suka ci suka furzar.