المساعد الشخصي الرقمي

مشاهدة النسخة كاملة : Darasi na ashirin da biyar: Tarjaman tafsirin suratul asr da suratul humazh daga littafin: Attafisul muyassar


طاهر جبريل دكو
_3 _April _2014هـ الموافق 3-04-2014م, 01:59 AM
TAFSIRIN SURATUL ASR

وَالْعَصْرِ (1)
Ina rantsuwa da zamani.

إِنَّ الْإِنْسَانَ لَفِي خُسْرٍ (2)
Lallai ne mutum tabbas yana cikin hasara.

Sahrhi: Allah Yayi rantsuwa da zamani saboda abinda ke cikin sa na abubuwan ban mamaki na kudurar Allah wadanda suke nuni zuwa ga girmanSa, kan cewa lallai yayan Adamu suna cikin halaka da tawaya. Baya halatta ga bawa yayi rantsuwa face da Allah, domin lallai rantsuwa da wanin Allah shirka ne.
إِلَّا الَّذِينَ آمَنُوا وَعَمِلُوا الصَّالِحَاتِ وَتَوَاصَوْا بِالْحَقِّ وَتَوَاصَوْا بِالصَّبْرِ (3)
Face wadanda suka yi imani kuma suka aikata ayyukan kwarai kuma suka yiwa juna wasiyya da bin gaskiya kuma suka yiwa juna wasiyya da yin hakuri.

Sahrhi: Face wadanda suka yi imani kuma suka yi aiki aiki na gari, kuma sashinsu yayi wa sashi wasiyya da riko da gaskiya da kuma aiki na da'a ga Allah, da kuma hakuri akan hakan.

TAFSIRIN SURATUL HUMAZAH

وَيْلٌ لِكُلِّ هُمَزَةٍ لُمَزَةٍ (1)
Bone ya tabbata ga duk mai nune, mai zunde (mai rada)

Sahrhi: Sharri da halaka ya tabbata ga duk wani mai yi da mutane, mai yawan suka gare su.
الَّذِي جَمَعَ مَالًا وَعَدَّدَهُ (2)
Wanda ya tara dukiya kuma ya mai da ita abar tattalinsa.

Sahrhi: Wanda babban damuwar sa itace tara dukiya da tattalin ta.
يَحْسَبُ أَنَّ مَالَهُ أَخْلَدَهُ (3)
Yana zaton cewa dukiyarsa zata dawwamar da shi.

Sahrhi: Yana zaton cewa; shi da wannan dukiyar da ya tara, ya lamuncewa kansa dawwama ne a duniya da kuma kubuta daga hisabi.
كَلَّا لَيُنْبَذَنَّ فِي الْحُطَمَةِ (4)
A'aha! Lallai ne za'a jefa shi a cikin hudama.

Sahrhi: Al'amarin ba kamar yadda ya zata bane, lallai ne za'a jefa shi cikin wuta wacce take kacancana duk wanda aka jefa a cikinta.
نَارُ اللَّهِ الْمُوقَدَةُ (6)
Wutar Allah ce da ake hurawa.

الَّتِي تَطَّلِعُ عَلَى الْأَفْئِدَةِ (7)
Wacce take lekawa a kan zukata.

Sahrhi: Lallai ita wata wuta ce hurarriya mai balbalin tsiya wacce saboda tsananin zafinta take ratsa jikkuna har zuwa zukata.
إِنَّهَا عَلَيْهِمْ مُؤْصَدَةٌ (8)
Lallai ne ita abar kullewa ce akansu.

فِي عَمَدٍ مُمَدَّدَةٍ (9)
Cikin wasu gimshikai mikakku.

Sahrhi: Lallai ne ita (wutar) akansu mai rufewa ce (suna) cikin wasu sarkoki da kukumai masu tsayi; saboda kada su fice daga cikinta.