المساعد الشخصي الرقمي

مشاهدة النسخة كاملة : Darasi na ashirin da hudu: Tarjaman tafsirin suratul zalzalah zuwa suratu - attakathur daga littafin: Attafisul muyassar


طاهر جبريل دكو
_3 _April _2014هـ الموافق 3-04-2014م, 01:45 AM
إِذَا زُلْزِلَتِ الْأَرْضُ زِلْزَالَهَا (1)
Idan aka girgiza kasa girgizawarta.

وَأَخْرَجَتِ الْأَرْضُ أَثْقَالَهَا (2)
Kuma kasa ta fitar da nauye nauyenta.

وَقَالَ الْإِنْسَانُ مَا لَهَا (3)
Kuma mutum yace; manene ya sameta?

Sharhi:Idan aka girgiza kasa girgizawa mai tsanani, kuma ta fitar da abinda ke cikinta na matattu da taskoki, kuma mutum ya rika tambaya cikin firgici; menene ya faru da ita?
يَوْمَئِذٍ تُحَدِّثُ أَخْبَارَهَا (4)
A wannan ranar (kasa) zata bada labarinta.

بِأَنَّ رَبَّكَ أَوْحَى لَهَا (5)
Cewa Ubangijinka Yayi umurni zuwa gareta.

Sharhi:Ranar kiyama kasa zata bada labari gameda abinda aka aikata akanta na alheri da na sharri, kuma da cewa Allah (mai tsarki da daukaka) Ya umurce ta da bada labari gameda abinda aka aikata a kanta.
يَوْمَئِذٍ يَصْدُرُ النَّاسُ أَشْتَاتًا لِيُرَوْا أَعْمَالَهُمْ (6)
A ranar nan mutane zasu fito dabam dabam domin a nuna musu ayyukansu.
Sharhi:Ranar da mutane zasu komo daga filin hisabi a rarrabe domin Allah Ya nuna musu abinda suka aikata mummuna da kyakkyawa kuma Ya sakanta musu akan ta.
فَمَنْ يَعْمَلْ مِثْقَالَ ذَرَّةٍ خَيْرًا يَرَهُ (7)
To wanda ya aikata gwargwadon nauyin zarra na alheri zai gan shi.

وَمَنْ يَعْمَلْ مِثْقَالَ ذَرَّةٍ شَرًّا يَرَهُ (8)
Kuma wanda ya aikata gwargwadon nauyin zarra na sharri zai ganshi.

Sharhi: haka wanda ya aikata gwargwadon nauyin dan kiyashi na alheri zai ga sakamakonsa a lahira, wanda kuma ya aikata gwargwadon nauyin dan kiyashi na sharri zai ga ukubarsa a lahira.
TAFSIRIN SURATUL ADIYATI




وَالْعَادِيَاتِ ضَبْحًا (1)
Ina rantsuwa da dawaki masu gudu suna fidda kukan ciki.

Sharhi: Allah Yayi rantsuwa da dawaki masu gudu saboda Allah suna fuskantan abokan gaba yayin da sautinsu ke bayyana saboda tsananin gudunsu. Baya halatta ga wani abin halitta yayi rantsuwa sai da Allah, saboda rantsuwa da wanin Allah shirkane.
فَالْمُورِيَاتِ قَدْحًا (2)
Masu kyasta wuta (da kofatunsu a kan dutse) kyastawa.

Sharhi: Sa'nnan (Yayi rantsuwa) da dawaki masu kyasta wuta saboda karfin kofatunsu da tsananin gudunsu.
فَالْمُغِيرَاتِ صُبْحًا (3)
Sa'annan masu kai hari bayan asuba.

Sharhi: Sa'annan (Yayi rantsuwa) da dawakin da ke kai hari da mahayansu kan abokan gaba a lokacin asuba.
فَأَثَرْنَ بِهِ نَقْعًا (4)
Sai suna tayar da kura game da shi.

Sharhi: Sai su tayar da kura da wannan gudun.
فَوَسَطْنَ بِهِ جَمْعًا (5)
Sai su kutsa (da ita kurar) tsakanin taron makiya.

Sharhi: Sai su kutsa da mahayasu cikin taron makiya.
إِنَّ الْإِنْسَانَ لِرَبِّهِ لَكَنُودٌ (6)
Lallai ne mutum mai tsananin butulci ne ga Ubangijinsa.

وَإِنَّهُ عَلَى ذَلِكَ لَشَهِيدٌ (7)
Kuma lallai ne shi game da hakan mai shaidawa ne.

وَإِنَّهُ لِحُبِّ الْخَيْرِ لَشَدِيدٌ (8)
Kuma lallai ne ga dukiya, shi mai tsananin so ne.

Sharhi: Lallai ne mutum, game da ni'imomin Ubangijinsa mai karyatawa ne, kuma lallai ne shi da wannan karyatawan nasa tabbatarwa yake yi. Kuma shi lallai game da son dukiya mai tsanani ne.
أَفَلَا يَعْلَمُ إِذَا بُعْثِرَ مَا فِي الْقُبُورِ (9)

Shin baya da sanin cewa idan aka tone abinda ke cikin kaburbura.
Sharhi: Shin mutum baya sanin abin da yake jiran sa idan Allah Ya fitar da matattu daga kaburbura domin hisabi da sakamako.
وَحُصِّلَ مَا فِي الصُّدُورِ (10)
Kuma aka bayyana abinda ke cikin zukata.

Sharhi: Kuma aka fitar da abinda ya buya a cikin zukata na alheri ko sharri.
إِنَّ رَبَّهُمْ بِهِمْ يَوْمَئِذٍ لَخَبِيرٌ (11)
Lallai ne Ubangijinsu game dasu a wannan ranan mai kididdigewa ne.

Sharhi:Lallai ne Ubangijinsu game dasu da ayyukansu a wannan ranan mai kididdigewa ne babu abinda yake buya gareShi daga hakan.

TAFSIRIN SURATUL KARI'AH




الْقَارِعَةُ (1)
Mai kwankwasa.
Sharhi: Tashin alkiyama wacce take kwankwasar zukatan mutane da firgicinta.
مَا الْقَارِعَةُ (2)
Menene mai kwankwasa?
Sharhi: Wane abu ne wannan mai kwankwasan?
وَمَا أَدْرَاكَ مَا الْقَارِعَةُ (3)
Kuma me ya sanar da kai abinda ake cewa mai kwankwasa?

Sharhi: Kuma wane abu ne ya sanar da kai game da ita?
يَوْمَ يَكُونُ النَّاسُ كَالْفَرَاشِ الْمَبْثُوثِ (4)
Ranan da mutane zasu kasance kamar fari watsatstsu.

Sharhi: A wannan ranan mutane - cikin yawansu da rarrabuwan su da motsawarsu - zasu kasance tamkar watsatstsun fari, sune masu faffadawa cikin wuta.
وَتَكُونُ الْجِبَالُ كَالْعِهْنِ الْمَنْفُوشِ (5)
Kuma duwatsu su kasance kamar gashin sufin da aka sabe.

Sharhi: Kuma duwatsu su kasance kamar gashin dabba ma'abucin launuka mabambanta wanda ake figewa da hannu, sai ya koma kura kuma ya gushe.
فَأَمَّا مَنْ ثَقُلَتْ مَوَازِينُهُ (6)
To amma wanda ma'aunansa suka yi nauyi.

فَهُوَ فِي عِيشَةٍ رَاضِيَةٍ (7)
To shi kam yana cikin wata rayuwa yardajjiya.

Sharhi: To amma wanda ma'aunan kyawawan ayyukansa suka yi rinjaye, to shi yana cikin wata rayuwa abar yarda a cikin aljanna.
وَأَمَّا مَنْ خَفَّتْ مَوَازِينُهُ (8)
Kuma amma wanda ma'aunansa suka yi rashin nauyi.

فَأُمُّهُ هَاوِيَةٌ (9)
To uwarsa itace (wutar) hawiya.

Sharhi: Kuma amma wanda ma'aunan kyawawan ayyukansa suka yi rashin nauyi kuma ma'aunan munanan ayyukansa suka yi rinjayi, to makomar sa itace wutar jahannama.
وَمَا أَدْرَاكَ مَا هِيَهْ (10)
Kuma me ya sananr da kai ita?

Sharhi: Kuma me ya sananr da kai – ya kai wannan manzon – mecece wannann hawiyar?
نَارٌ حَامِيَةٌ (11)
Wata wuta ce mai tsananin zafi.

Sharhi: Lallai ita wata wuta ce da zafinta ya tsananta saboda kunnata da akeyi.

TAFSIRIN SURATU-TTAKATHUR





أَلْهَاكُمُ التَّكَاثُرُ (1)
Alfahari da yawan dukiya da dangi ya shagaltar daku (daga ibada mai amfanar ku).
Sharhi: Alfahari da yawan dukiya da dangi ya shagaltar daku daga yiwa Allah da'a.
حَتَّى زُرْتُمُ الْمَقَابِرَ (2)
Har sai da ku ka ziyarci kaburbura.

Sharhi:Shagaltuwar ku da hakan ya ci gaba har sai da kuka zarce zuwa makabarta kuma aka binne ku a cikinsa.
كَلَّا سَوْفَ تَعْلَمُونَ (3)
A'aha! Nan gaba zasu sani.

Sharhi:Ba haka ya dace ace gasan tara dukiya ya shagaltar da ku ba, da sannu zaku gane cewa lallai gidan lahira shi yafi alheri gare ku.
ثُمَّ كَلَّا سَوْفَ تَعْلَمُونَ (4)
Sa'annan tabbas zaku sani.

Sharhi:Sa'annan ku kiyayi (kanku)! da sannu zaku san munin karshe na shagaltuwar ku daga barin ta.
كَلَّا لَوْ تَعْلَمُونَ عِلْمَ الْيَقِينِ (5)
A'aha! Da kuna sani sani na yakini.

لَتَرَوُنَّ الْجَحِيمَ (6)
Lallai ne zaku ga (wutar) jahima.

ثُمَّ لَتَرَوُنَّهَا عَيْنَ الْيَقِينِ (7)
Sa'annan lallai ne zaku ganta da idanu bayyane.

ثُمَّ لَتُسْأَلُنَّ يَوْمَئِذٍ عَنِ النَّعِيمِ (8)
Sa'annan lallai ne za'a tambaye ku a wannan ranan game da ni'imar (da aka muku)

Sharhi:Ba haka ya dace ace gasan tara dukiya ya shagaltar da ku ba, da kuna sani hakikanin sani, da kun fadaka, kuma da kun yi gaggawan ceto kawukanku daga halaka. Tabbas zaku ganta ba tare da wani kokwanto ba. Sa'annan kuma tabbas za'a tambaye ku ranar kiyama game da dukkanin nau'uka ta ni'ima.