تسجيل الدخول

مشاهدة النسخة كاملة : Darasi na ashirin da uku: Tarjaman tafsirin suratul qadar da suratul bayyinahdaga littafin: Attafisul muyassar


طاهر جبريل دكو
_22 _March _2014هـ الموافق 22-03-2014م, 02:28 AM
إِنَّا أَنْزَلْنَاهُ فِي لَيْلَةِ الْقَدْرِ (1)
Lallai ne Mu Mun saukar da shi a cikin lailatul kadari (daren mai daraja).
Sharhi: Lallai ne Mu mun saukar da Alkur'ani cikin dare mai daukaka da falala, shi (lailatul kadari) daya ne daga cikin dareren watan ramadana.
وَمَا أَدْرَاكَ مَا لَيْلَةُ الْقَدْرِ (2)
Kuma me ya sanar da kai abinda ake cewa lailatul kadari.

Sharhi: Kuma me ya sanar da kai – ya kai wannan annabin – abinda ake nufi da lailatul kadari (wato dare mai daraja dadaukaka)?
لَيْلَةُ الْقَدْرِ خَيْرٌ مِنْ أَلْفِ شَهْرٍ (3)
Lailatul kadari yafi daraja sama da watanni dubu.

Sharhi: Lailatul kadari dare ne mai albarka, aikin kwarai a cikinsa ya fi alheri sama da aiki a cikin watanni dubu wadanda babu lailatul kadari a cikinsu.
تَنَزَّلُ الْمَلَائِكَةُ وَالرُّوحُ فِيهَا بِإِذْنِ رَبِّهِمْ مِنْ كُلِّ أَمْرٍ (4)
Mala'iku da Ruhi suna sauka a cikinsa da izinin Ubangijinsu saboda kowane al'amari.

Sharhi: Saukan mala'iku da Jibrilu (A.S) a cikinsa yana yawaita da izinin Ubangijinsu game da kowane al'amari da Ya kaddara shi a cikin wannan shekaran.
سَلَامٌ هِيَ حَتَّى مَطْلَعِ الْفَجْرِ (5)
Amminci ne shi har zuwa ketowan alfijir.

Sharhi: shi aminci ne dukkanin sa har zuwa ketowar alfijir.




Suratul bayyinah


لَمْ يَكُنِ الَّذِينَ كَفَرُوا مِنْ أَهْلِ الْكِتَابِ وَالْمُشْرِكِينَ مُنْفَكِّينَ حَتَّى تَأْتِيَهُمُ الْبَيِّنَةُ (1)
Wadanda suka kafirta daga ma'abuta littafi da mushirikai basu kasance masu gushewa daga gaskiya ba har sai da hujja ta je musu.

Sharhi: Wadanda suka kafirta daga yahudawa da nasara da mushirikai basu kasance masu barin kafircinsu ba har alamar da akayi musu alkawari ta zo musu, wacce aka alkawarta musu a cikin littattafan da suka gabata.
رَسُولٌ مِنَ اللَّهِ يَتْلُو صُحُفًا مُطَهَّرَةً (2)
Wani manzo daga Allah yana karatun wasu takardu tsarkakakku.

Sharhi: Shine manzo Muhammad (s.a.w) yana karatun alkur'ani cikin wasu takardu tsarkakakku.
فِيهَا كُتُبٌ قَيِّمَةٌ (3)
Cikin su akawai wasu littattafai masu kima.

Sharhi: Cikin wadannan takardun akwai labaru na gaskiya da umurce umurce na adalci, suna shiryarwa zuwa ga gaskiya kuma zuwa tafarki ma daidaici.
وَمَا تَفَرَّقَ الَّذِينَ أُوتُوا الْكِتَابَ إِلَّا مِنْ بَعْدِ مَا جَاءَتْهُمُ الْبَيِّنَةُ (4)
Kuma wadanda aka baiwa littafi basu rarraba ba face bayan hujja ta je musu.

Sharhi: Wadanda aka baiwa littafi daga yahudawa da nasara basu yi sabani gameda kasancewar Muhammadu manzo na gaskiya ba dangane da abin da suke samu na sifansa a cikin littattafansu sai bayan ta bayyana agaresu cewa lallai shine annabin da akayi alkawari game da zuwansa a cikin attaura da injila, saboda haka sun kasance masu tarayya akan ingancin annabtansa, yayin da aka aiko shi kuma sai suka rarraba, daga cikinsu akwai wanda yayi imani dashi, daga cikinsu kuma akwai wanda yayi jayayya game da manzoncinsa saboda zalunci da hassada.
وَمَا أُمِرُوا إِلَّا لِيَعْبُدُوا اللَّهَ مُخْلِصِينَ لَهُ الدِّينَ حُنَفَاءَ وَيُقِيمُوا الصَّلَاةَ وَيُؤْتُوا الزَّكَاةَ وَذَلِكَ دِينُ الْقَيِّمَةِ (5)
Kuma ba'a umurcesu ba face da cewa su bautawa Allah suna masu tsarkake addini gare Shi suna masu karkata zuwa ga gaskiya kuma su tasyar da sallah kuma su bada zakka, kuma wannan shine addinin managarta.

Sharhi: Kuma ba'a umurcesu ba a cikin sauran shari'o'i face da cewa su bautawa Allah Shi kadai suna masu nufatan Allah da ibadarsu masu karkata daga barin shirka zuwa ga imani, kuma su tsayar da sallah su kuma bada zakka, kuma wannan shine addinin istikama, wanda shine musulunci.

إِنَّ الَّذِينَ كَفَرُوا مِنْ أَهْلِ الْكِتَابِ وَالْمُشْرِكِينَ فِي نَارِ جَهَنَّمَ خَالِدِينَ فِيهَا أُولَئِكَ هُمْ شَرُّ الْبَرِيَّةِ (6)
Lallai ne wadanda suka kafirta daga mutanen littafi da mushirikai suna cikin wutar jahannama suna masu dauwama a cikinta, wadannan sune mafi ashararancin talikai.

Sharhi: Lallai wadanda suka kafirta daga yahudu da nasara da mushirikai ukubarsu itace wutar jahannama suna masu dauwama a cikinta, wadannan sune mafi tsananin sharri cikin halittu.
إِنَّ الَّذِينَ آمَنُوا وَعَمِلُوا الصَّالِحَاتِ أُولَئِكَ هُمْ خَيْرُ الْبَرِيَّةِ (7)
Lallai ne wadanda suka yi imani kuma suka aikata ayyukan kwarai, wadannan sune mafiya alheri cikin halittu.

Sharhi: Lallai ne wadanda suka gaskata Allah, suka bi manzonSa kuma suka aikata ayyukan kwarai, sune mafiya alherin halitta.

جَزَاؤُهُمْ عِنْدَ رَبِّهِمْ جَنَّاتُ عَدْنٍ تَجْرِي مِنْ تَحْتِهَا الْأَنْهَارُ خَالِدِينَ فِيهَا أَبَدًا رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُمْ وَرَضُوا عَنْهُ ذَلِكَ لِمَنْ خَشِيَ رَبَّهُ (8)
Sakamakonsu a wurin Ubangijinsu shine gidajen aljannar zama koramu na gudana daga karkashinta, suna masu dawwama a cikinta har abada, Allah Ya yarda dasu, kuma suma sun yarda da Shi, wannan sakamako ne ga wanda ya ji tsoron Ubangijinsa.

Sharhi: Sakamakonsu a wurin Ubangijinsu ranar alkiyama shine gidajen aljannar zama kuma matabbata wanda ya kai makura wurin kyau, koramu na gudana daga karkashin benayenta, suna masu dawwama a cikin ta har abada, Allah Ya yarda dasu daon haka Ya karbi ayyukansu na kwarai, kuma suma sun yarda da Shi da abinda Ya tanadar musu na nau'ukan karama, wannan sakamako mai kyau na wanda ya ji tsoron Allah ne kuma ya nisanci sabonSa.