طاهر جبريل دكو
_19 _March _2014هـ الموافق 19-03-2014م, 01:38 AM
وَالتِّينِ وَالزَّيْتُونِ (1)
Ina rantsuwa da Attinu da Azzaitun.
وَطُورِ سِينِينَ (2)
Da duru Sinina.
وَهَذَا الْبَلَدِ الْأَمِينِ (3)
Da wannan garin amintacce.
لَقَدْ خَلَقْنَا الْإِنْسَانَ فِي أَحْسَنِ تَقْوِيمٍ (4)
hakika tabbas Mun halicci mutum cikin mafi kyawun tsayuwa.
ثُمَّ رَدَدْنَاهُ أَسْفَلَ سَافِلِينَ (5)
Sa'annan Muka mayar da shi mafi kaskancin makaskanta.
إِلَّا الَّذِينَ آمَنُوا وَعَمِلُوا الصَّالِحَاتِ فَلَهُمْ أَجْرٌ غَيْرُ مَمْنُونٍ (6)
Face wadanda suka yi imani kuma suka aikata kyawawan ayyuka, to (su kam), suna da wani sakamako wanda baya yankewa.
Sharhi: Allah Yayi rantsuwa da tinu da zaituna, su wasu yayan itatuwane shahararru. Kuma Yayi rantsuwa da dutsen saina'a wanda Allah Yayi magana da (Annabi) Musa a kansa magana (ta hakika). Kuma Yayi rantsuwa da wannan garin wanda ya aminta daga dukkanin (abin) tsoro shine Makka wurin da wahayi ya sauka. Hakika Mun halicci mutum cikin mafi kyawun sura, sannan Muka maido shi zuwa ga wuta idan bai yiwa Allah da'a ba kuma bai bi manzon Allah ba, sai dai wadanda suka yi imani kuma suka aikata ayyukan kwarai , suna da wani sakamako mai girma wanda babu yankewa a gare shi kuma baya tauyewa.
فَمَا يُكَذِّبُكَ بَعْدُ بِالدِّينِ (7)
To bayan haka, me ya sanya ka karyata game da sakamakon?
Sharhi: Menen ya kai ka – ya kai mutum – ga karyatawa game da tashin alkiyama da sakamako tareda bayyanan dalilai game da kuduran Allah Madaukakin sarki akan hakan?
أَلَيْسَ اللَّهُ بِأَحْكَمِ الْحَاكِمِينَ (8)
Ashe Allah ba Shine mafi kyawun hukuncin masu hukunci ba?
Sharhi: Ashe Allah da Ya sanya wannan yinin domin yin hukunci tsakanin mutane ba shine fiyayye ba a cikin hukunci daga dukkan mahukunta cikin dukkanin abin da Ya halitta? (amsar itce) Ee! To shin za'a bar halittu hakanan kara zube ba'a umurtansu kuma ba'a hanasu kuma ba'a musu sakamako na lada ba'a yi musu ukuba? Hakan bai dace ba kuma ba zai kasance ba.
SURTUL ALAK
اقْرَأْ بِاسْمِ رَبِّكَ الَّذِي خَلَقَ (1)
Kayi karatu da sunan Ubangijinka wanda Yayi halitta.
خَلَقَ الْإِنْسَانَ مِنْ عَلَقٍ (2)
Ya halicci mutum daga gudan jinni.
اقْرَأْ وَرَبُّكَ الْأَكْرَمُ (3)
Kayi karatu, kuma Ubangijinka shine mafi karimci.
الَّذِي عَلَّمَ بِالْقَلَمِ (4)
Wanda Ya sanar ta hanyar alkalami.
عَلَّمَ الْإِنْسَانَ مَا لَمْ يَعْلَمْ (5)
Ya sanar da mutum abinda bai sani ba.
Sharhi: Kayi karatu – ya kai wannan annabin – na abinda aka saukar maka daga alkur'ani kana mai farawa da sunan Ubangijinka wanda Ya kadaita da halitta, wanda Ya halicci kowane mutum daga wani yanki na jinni mai kauri kuma (launin) ja. Kayi karatu – ya kai wannan annabin – na abinda aka saukar maka lallai Ubangijinka mai yawan kyautatawa ne. mai fadin baiwa, wanda Ya sanar da halittunSa (yadda) ake rubutu da alkalami, Ya sanar da mutum abinda da can bai sani ba, sai Ya kauratar da shi daga duhun jahilci zuwa hasken ilimi.
كَلَّا إِنَّ الْإِنْسَانَ لَيَطْغَى (6)
A'aha! Lallai mutum yayi dagawa.
أَنْ رَآهُ اسْتَغْنَى (7)
Domin yaga (kansa) ya wadata
إِنَّ إِلَى رَبِّكَ الرُّجْعَى (8)
Lallai ne makoma wurin Ubangijinka take.
Sharhi: Tabbas lallai mutum yana ketare iyakokin Allah idan wadata ta sa shi girman kai, saboda haka duk wani mai ketare haddi ya san cewa makoma ga Allah take, zai sakantawa ko wane mutum da aikinsa.
أَرَأَيْتَ الَّذِي يَنْهَى (9)
Shin ka ga wanda ke hana?
عَبْدًا إِذَا صَلَّى (10)
Bawa idan yayi sallah?
أَرَأَيْتَ إِنْ كَانَ عَلَى الْهُدَى (11)
Shin ka gani, idan (bawan) ya kasance akan shiriya?
أَوْ أَمَرَ بِالتَّقْوَى (12)
Ko kuma yayi umurni da takawa?
Sharhi: Shin kaga abinda ya fi ban mamaki sama da ketare haddin wannan mutumin, wanda shine Abujahal, wanda yake hana bawanMu wanada shine Muhammad (s.a.w) idan yana salla ga Ubangijinsa? Shin bani labari kana ganin idan wanda ake hanawa sallan ya kasance a kan shiriya to ta yaya zai hana shi? Ko kuma idan ya kasance mai umurtan waninsa ne da tsoron Allah sai ya hana shi aikata hakan?
أَرَأَيْتَ إِنْ كَذَّبَ وَتَوَلَّى (13)
Shin ka gani idan (shi mai hanin) ya karyata kuma ya juya baya?
أَلَمْ يَعْلَمْ بِأَنَّ اللَّهَ يَرَى (14)
Ashe bai sani bane cewa Allah Yana gani?
كَلَّا لَئِنْ لَمْ يَنْتَهِ لَنَسْفَعًا بِالنَّاصِيَةِ (15)
A'aha! Idan bai hanu ba, lallaizaMu ja gashin makwarkwada.
نَاصِيَةٍ كَاذِبَةٍ خَاطِئَةٍ (16)
Makwarkwada makaryaciya mai laifi.
فَلْيَدْعُ نَادِيَهُ (17)
Sai ya kirayi kungiyarsa.
سَنَدْعُ الزَّبَانِيَةَ (18)
ZaMu kirayi Zabaniyawa (wato mala'iku)
كَلَّا لَا تُطِعْهُ وَاسْجُدْ وَاقْتَرِبْ (19)
A'aha! Kada ka biye masa, kuma kayi tawalu'u ka kusanci (Ubangijinka).
Sharhi: Bani labara, idan wannan mai hanin ya karyata abinda ake kiransa zuwa gare shi, kuma ya kawar da kai daga barinsa, shin bai sani bane cewa Allah Yana ganin duk abinda yake aikatawa? Al'amarin ba yadda Abujahal yake zato bane, lallai idan bai tuba bay a janye daga sassabawarsa da cutarwarsa ba, lallai zaMu yi kamu ga magabacin kansa kamu mai tsanani, kuma a jefa shi cikin wuta, makwarkwadarsa makwarkwada makaryaciya cikin abin fadinta, mai kuskure cikin ayyukanta, kamar kace karya da kuskure sun fito fili akanta. Saboda haka shi wannan mai ketare haddin ya halarto da yan dandalinsa wadanda yake neman cin nasara dasu, da sannu zaMu kira mala'ikun azaba, al'amarin ba yadda Abujahal ke zato bane, lallai – ya kai wannan annabin – ba zai taba iya shafanka da wata munanawa ba, saboda haka kada kayi masa biyayya cikin abin da yake kiran ka zuwa gare shi na barin sallah, kuma kayi sujjada ga Ubangijinka kuma ka kusance Shi ta hanyar neman soyayyarSa da yi masa da'a.