تسجيل الدخول

مشاهدة النسخة كاملة : Darasi na ashirin da daya: Tarjaman tafsirin suratu-ashsharh daga littafin attafsirul muyassar


طاهر جبريل دكو
_28 _February _2014هـ الموافق 28-02-2014م, 06:13 PM
أَلَمْ نَشْرَحْ لَكَ صَدْرَكَ (1)
Ashe baMu buda maka zuciyarka ba?
وَوَضَعْنَا عَنْكَ وِزْرَكَ (2)
Kuma Muka saryar maka da nauyinka?

Sharhi: Ashe bamu yalwata maka zuciyarka ba domin shari'o'in addini, da kuma kira zuwa ga Allah, da sifantuwa da dabi'un kwarai kai wannan annabin, kuma Muka sauke maka nuyinka?
الَّذِي أَنْقَضَ ظَهْرَكَ (3)
Wanda ya nauyaya bayanka?
وَرَفَعْنَا لَكَ ذِكْرَكَ (4)
Kuma Muka daukaka maka ambatonka?

Sharhi: Wanda Ya nauyaya bayanka, kuma Mum sanyaka a wani matsayi madaukaki- saboda ni'imar da mukayi akanka da karramawa.
فَإِنَّ مَعَ الْعُسْرِ يُسْرًا (5)
To lallai ne tare da tsananin nan akwai wani sauki.
إِنَّ مَعَ الْعُسْرِ يُسْرًا (6)
Lallai ne tare da tsananin nan akwai wani sauki.

Sharhi: Kada cutarwan makiyanka ya karkatar da kai daga yada sakon (Allah) domin lallai tare da kuncin akwai mafita, lallai ne tareda kuncin akwai mafita.
فَإِذَا فَرَغْتَ فَانْصَبْ (7)
Saboda haka idan ka kare ibada sai ka kafu (kana rokon Allah).
وَإِلَى رَبِّكَ فَارْغَبْ (8)
Kuma zuwa ga Ubangijinka ka kayi kwadayi.

Sharhi: idan ka kamala daga al'amuran duniya da shagulgulan ta sai ka yi kokari cikin ibada, kuma zuwa ga Ubanjikinka Shi kadai ka kwadaitu da abin da ke wurinsa.