المساعد الشخصي الرقمي

مشاهدة النسخة كاملة : Darasi na ashirin: Tarjaman tafsirin suratu -dduha daga littafin attafsirul muyassar


طاهر جبريل دكو
_26 _February _2014هـ الموافق 26-02-2014م, 12:19 AM
وَالضُّحَى (1)
Ina rantsuwa da hantsi.
وَاللَّيْلِ إِذَا سَجَى (2)
Da dare a lokacinda ya rufe da (duhunsa).
مَا وَدَّعَكَ رَبُّكَ وَمَا قَلَى (3)
Ubangijinka bai kyaleka ba kuma bai yi fushi da kai ba.

Sharhi: Allah Yayi rantsuwa da lokacin hantsi, abin da ake nufi da shi shine dukkan yini, (kuma Yayi rantsuwa) da dare idan yayi tsit da halittu kuma duhunsa ya tsananta. Kuma Allah Yana rantsuwa da abinda Yaso daga halittunSa, amma ababen halitta kam, baya halatta gare su suyi rantsuwa da wanin mahaliccinsa, saboda rantsuwa da wanin Allah shirkane. Ubangijinka bai barka ba- ya kai wannan annabin- kuma bai yi fushi da kai ba da jinkirin (saukan) wahayi gareka.
وَلَلْآخِرَةُ خَيْرٌ لَكَ مِنَ الْأُولَى (4)
Kuma lallai ne ta karshe ta fi alkhairi gareka bisa ga ta farko.
وَلَسَوْفَ يُعْطِيكَ رَبُّكَ فَتَرْضَى (5)
Kuma lallai ne da sannu Ubangijinka zai yi ta baka har sai ka yarda.

Sharhi: Kuma lallai gidan lahira shi yafi alkhairi a gareka sama da gidan duniya, kuma tabbas da sannu Ubangijinka zai baka daga nau'uka na ni'imomi a lahira- ya kai wannan annabin- sai ka yarda da hakan.
أَلَمْ يَجِدْكَ يَتِيمًا فَآوَى (6)
Ashe bai sameka marayaba sa'annan Yayi maka makoma?
وَوَجَدَكَ ضَالًّا فَهَدَى (7)
Kuma Ya sameka Ya sameka baka da shari'a sai Ya shiryar da kai?
وَوَجَدَكَ عَائِلًا فَأَغْنَى (8)
Kuma Ya sameka matalauci sai Ya wadataka?

Sharhi: Ashe kafin nan bai sameka maraya ba mahaifinka ya rasu tun kana cikin mahaifiyarka sai Ya maka gata kuma Ya baka kulawa? Kuma ya sameka baka san littafi ba baka san imani ba kuma Ya sanar da kai abinda baka sani ba, kuma Ya datar da kai zuwa ga mafi kyawun ayyuka? Kuma Ya taradda kai fakiri amma ya koro maka arzikin ka zuwa gare ka kuma Ya wadata zuciyar ka da kana'a da hakuri?
فَأَمَّا الْيَتِيمَ فَلَا تَقْهَرْ (9)
Saboda haka maraya, to kada ka rinjaye shi.
وَأَمَّا السَّائِلَ فَلَا تَنْهَرْ (10)
Kuma matambayi, to kada ka yi masa tsawa.
وَأَمَّا بِنِعْمَةِ رَبِّكَ فَحَدِّثْ (11)
Kuma game da ni'imar Ubangijinka, to ka bada labari (don godiya).

Sharhi: To amma maraya kam kada ka munana masa mu'amala, mai roko kuma kada ka tsauratashi, a'a ka ciyar dashi, kuma ka biya masa bukatansa, kuma gameda ni'imar Ubangijinka wacce Ya rina ka da ita, to ka bada labari game da shi.