المساعد الشخصي الرقمي

مشاهدة النسخة كاملة : Darasi na goma sha tara: Tarjaman tafsirin suratul -lail daga littafin attafsirul muyassar


طاهر جبريل دكو
_25 _February _2014هـ الموافق 25-02-2014م, 02:36 AM
وَاللَّيْلِ إِذَا يَغْشَى (1)
Ina rantsuwa da dare a lokacinda yake rufewa.
وَالنَّهَارِ إِذَا تَجَلَّى (2)
Da yini idan ya kuranyewa.
وَمَا خَلَقَ الذَّكَرَ وَالْأُنْثَى (3)
Da abinda Ya halitta na miji da ta mace.
إِنَّ سَعْيَكُمْ لَشَتَّى (4)
Lallai ne ayyukanku dabam dabam suke.

Sharhi: Allah (madaukakin sarki) Yayi rantsuwa da dare a yayin da ya lullube kasa da abinda ke cikinta da duhunsa (kuma Yayi rantsuwa) da yini idan ya yaye duhun dare da haskensa (kuma Yayi rantsuwa) da halittan nau'i biyu (cikin komai) na miji da ta mace. Lallai ayyukanku mabambanta ne, tsakanin mai aiki don duniya mai aiki don lahira.
فَأَمَّا مَنْ أَعْطَى وَاتَّقَى (5)
To amma wanda yayi kyauta kuma yayi takawa.
وَصَدَّقَ بِالْحُسْنَى (6)
Kuma ya gaskata game da kalma mai kyau.
فَسَنُيَسِّرُهُ لِلْيُسْرَى (7)
To da sannu zamu saukake masa har ya kai ga sauki.

فأمَّا من بذل من ماله واتقى الله في ذلك، وصدَّق بـ «لا إله إلا الله» وما دلت عليه، وما ترتب عليها من الجزاء، فسنرشده ونوفقه إلى أسباب الخير والصلاح ونيسِّر له أموره.
Sharhi: To amma wanda ya ciyar daga dukiyarsa kuma ya ji tsoron Allah kuma ya gaskata game da la'ilaha-illa-llahu da abinda take nuni zuwa gare shi da abin da zai kasance a game da shi na sakamako, to da sannu zaMu karfafe shi kuma Mu datar da shi zuwa ga sabubba na alheri da nagarta kuma Mu saukake masa al'amuransa.
وَأَمَّا مَنْ بَخِلَ وَاسْتَغْنَى (8)
kuma amma wanda yayi rowa kuma ya wadatu da kansa.
وَكَذَّبَ بِالْحُسْنَى (9)
Kuma ya karyata gameda kalma mai kyau.
Sharhi: To amma wanda yayi rowan dukiyarsa kuma ya wadatu daga sakamakon Ubangijinsa, kuma ya karyata game da la'laha-illa-llahu da abinda yake nuni zuwa gareshi, da abinda yake kasancewa a sanadin haka na sakamako.
فَسَنُيَسِّرُهُ لِلْعُسْرَى (10)
To da sannu zamu saukake masa har ya kai ga tsanani.
وَمَا يُغْنِي عَنْهُ مَالُهُ إِذَا تَرَدَّى (11)


Sharhi: To da sannu zaMu sawwake masa sabubban waraka, kuma dukiyarsa da yake rowanta bazata amfaneshi ba idan ya fada a wuta.
إِنَّ عَلَيْنَا لَلْهُدَى (12)
Lallai ne aikinMu ne Mu bayyana shiriya.
وَإِنَّ لَنَا لَلْآخِرَةَ وَالْأُولَى (13)
Kuma lallai ne tabbas lahira da duniya namu ne.

Sharhi: Lallai bayanin hanyar shiriya wanda ke sadarwa zuwa ga Allah da aljannansa daga tafarkin bata akanMu yake da falalarMu da hikimarMu. Kuma lallai mallakar rayuwar duniya da rayuwar lahira taMu ce.
فَأَنْذَرْتُكُمْ نَارًا تَلَظَّى (14)
Saboda haka nayi muku gargadi da wuta mai babbaka.

Sharhi: Na gargadeku ya ku mutane, kuma Na tsauratar daku wata irin wuta wacce take balbala, itace wutar jahannama.
لَا يَصْلَاهَا إِلَّا الْأَشْقَى (15)
Babu mai shiganta face mafi shakawa.
الَّذِي كَذَّبَ وَتَوَلَّى (16)
Wanda ya karyata kuma ya juya baya.

Sharhi: Babu mai shigar ta face mai tsananin shakiyanci, wanda ya karyata annabin Allah Muhammadu (s.a.w) kuma ya kau da kai daga yin imani da Allah da yi musu da'a.
وَسَيُجَنَّبُهَا الْأَتْقَى (17)
Kuma mafi takawa zai nisanceta
الَّذِي يُؤْتِي مَالَهُ يَتَزَكَّى (18)
Wanda yake bayar da dukiyarsa alhali yana tsarkaka.
وَمَا لِأَحَدٍ عِنْدَهُ مِنْ نِعْمَةٍ تُجْزَى (19)
Alhali babu wani mai wata ni'ima a wurinsa wacce ake bukata sakamakonta.
إِلَّا ابْتِغَاءَ وَجْهِ رَبِّهِ الْأَعْلَى (20)
face neman yardan Ubangijinsa madaukaki.
وَلَسَوْفَ يَرْضَى (21)
Kuma lallai ne da sannu zai yarda (da sakamakon da za'a bashi).

Sharhi: Kuma da sannu za'a nisantar da mai tsananin tsoron Allah daga gareta. Wanda ya sanya dukiyarsa don neman karin alheri. Kuma ba wai yana ciyar da dukiyar tasa bane don sakantawa wanda ya kyautata masa, sai dai kawai shi yana neman fuskan Ubangijinsa ne madaukaki da yardanSa, kuma da sannu Allah zai bashi abin da zai yarda da shi a cikin Allah.