طاهر جبريل دكو
_24 _February _2014هـ الموافق 24-02-2014م, 01:39 AM
وَالشَّمْسِ وَضُحَاهَا (1)
Ina rantsuwa da rana da hantsinta.
وَالْقَمَرِ إِذَا تَلَاهَا (2)
Kuma da wata idan ta biyo ta.
وَالنَّهَارِ إِذَا جَلَّاهَا (3)
Kuma da yini idan ta bayyana ta.
وَاللَّيْلِ إِذَا يَغْشَاهَا (4)
Kuma da dare idan ya lullubeshi.
وَالسَّمَاءِ وَمَا بَنَاهَا (5)
Kuma da sama da abinda ya ginata.
وَالْأَرْضِ وَمَا طَحَاهَا (6)
Kuma da kasa da abinda ya shimfidata.
وَنَفْسٍ وَمَا سَوَّاهَا (7)
Kuma da rai da abinda ya daidaitashi.
فَأَلْهَمَهَا فُجُورَهَا وَتَقْوَاهَا (8)
Sa'annan ya sanar dashi fajircinsa da shiriyarsa.
قَدْ أَفْلَحَ مَنْ زَكَّاهَا (9)
Hakika wanda ya tsarkaketa ya rabauta.
وَقَدْ خَابَ مَنْ دَسَّاهَا (10)
Kuma hakika wanda ya turbudeta (da zunubbai) ya tabe.
Sharhi: Allah Yayi rantsuwa da rana da yininta da hudowarta da hantsinta. (kuma Yayi rantsuwa) da wata idan ta bita (wato tabi rana) yayin hudowarta da buyanta, (kuma Yayi rantsuwa) da yini idan ya yaye duhu ya kuranyeshi (kuma Yayi rantsuwa) da dare yayin da ya lullube kasa sai abinda ke kanta ya kasance duhu, (kuma Yayi rantsuwa) da sama da gininta kyautatacce, (kuma Yayi rantsuwa) kasa da shimfidarta, (kuma Yayi rantsuwa) da kowace rai da kammalawar da Allah Yayi na halittanta domin su aiwatar da al'amuranta, sai Ya bayyana mata hanyar sharri da hanyar alheri. Hakika wanda ya tsarkake ta ya habaka ta ya rabauta, wanda kuma ya turbude ransa da zunubbai yayi asara.
كَذَّبَتْ ثَمُودُ بِطَغْوَاهَا (11)
Samudawa sun karyata (annabinsu) saboda dagawarsu.
إِذِ انْبَعَثَ أَشْقَاهَا (12)
A lokacinda suka aika shakiyyin cikinsu (don ya soke rakumar Salihu).
فَقَالَ لَهُمْ رَسُولُ اللَّهِ نَاقَةَ اللَّهِ وَسُقْيَاهَا (13)
Sai manzon Allah (Salihu) yace musu; ina tsauratar daku taguwar Allah da ruwan shanta.
فَكَذَّبُوهُ فَعَقَرُوهَا فَدَمْدَمَ عَلَيْهِمْ رَبُّهُمْ بِذَنْبِهِمْ فَسَوَّاهَا (14)
Sai suka karyata shi, sa'annan suka soketa, saboda haka sai Ubangijinsu Ya darkakesu saboda zunubbansu kuma ya daidaita ta (wato azabar a tsakaninsu babu wanda ya kubuta).
وَلَا يَخَافُ عُقْبَاهَا (15)
Kuma baya tsoron akibarta (ita halakarwan).
Sharhi: Samudawa sun karyata annabinsu saboda kaiwarsu makura a cikin sabon Allah, yayin da mafi yawan yan kabilar (Samudawa) suka yunkura domin soke taguwar saboda tabewa. Sai manzon Allah Salihu (amincin Allah ya tabbata gareshi) ku kiyayi taba taguwar nan da wata cutarwa domin ita ayace Allah Ya aiko ta gareku tana nuni zuwaga gaskiyar annabinku, ku kiyayi kanku! Kada ku wuce iyaka gameda ruwan shanta, domin tana da yinin ta na shan ruwa, kuma kuna da wani yini sananne na shanku. Sai hakan yayi musu nauyi, sai suka karyata shi gameda alkawarin da yayi musu na azaba, saboda haka sai suka soke ta, sai Ubangijinsu Ya game su cikin azaba saboda laifinsu, Ya daidaita su a cikin ta babu wanda ya kubuta daga cikinsu. Kuma (Allah) - mai girman kudura- baYa tsoron abinda zai biyo bayan saukar musu da azaban da Yayi.