المساعد الشخصي الرقمي

مشاهدة النسخة كاملة : Darasi na gomasha bakwai: Tarjaman tafsirin suratul balad daga littafin attafsirul muyassar


طاهر جبريل دكو
_24 _February _2014هـ الموافق 24-02-2014م, 12:05 AM
لَا أُقْسِمُ بِهَذَا الْبَلَدِ (1)
Ina rantsuwa da wannan garin (Makka).
وَأَنْتَ حِلٌّ بِهَذَا الْبَلَدِ (2)
Alhali kai kana mai sauka a cikin wannan garin.
وَوَالِدٍ وَمَا وَلَدَ (3)
Da mahaifi da abinda ya haifa.
لَقَدْ خَلَقْنَا الْإِنْسَانَ فِي كَبَدٍ (4)
Lallaine hakika Mun halicci mutum a cikin wahala.

Sharhi: Allah Yayi rantsuwa da wannan garin mai Alfarma, shine Makkah, alhali – ya kai wannan Annabin – kana halarce a cikin wannan garin mai alfarma kana aikata abinda kake so a cikinsa, kuma bai halatta gare shi ba face (gwargwadon) sa'a daya a cikin yini. A cikin ayar akwai albishir ga Annabi (s.a.w) akan bude (garin) Makka a hanunsa (fathu Makkah) da halatta masa yaki a cikinsa. Kuma Ya rantse da uban mutane – wanda shine Adamu (amincin Allah ya tabbata gare shi) – da abinda ya yadu daga tsatsonsa na yaya, hakika Mun halicci mutum a cikin tsanani da wahala daga wahalhalun duniya.
أَيَحْسَبُ أَنْ لَنْ يَقْدِرَ عَلَيْهِ أَحَدٌ (5)
Ko yana zaton babu wani mai iya samun iko akansa?

Sharhi: Shi yana zaton cewa don abinda ya tara na dukiya Allah baShida iko aknsa ne?
يَقُولُ أَهْلَكْتُ مَالًا لُبَدًا (6)
Yana cewa; na halakar da dukiya mai yawa.
أَيَحْسَبُ أَنْ لَمْ يَرَهُ أَحَدٌ (7)
Yana zaton babu wanda ya ganshi ne?

Sharhi: Cikin alfahari yana cewa; na ciyar da dukiya mai yawa, shin yana zaton cewa acikin wannan aikin nasa Allah baYa ganinsa ne? kuma ba zai yi masa hisabi akan (zunubinsa) karami da babba ba?
أَلَمْ نَجْعَلْ لَهُ عَيْنَيْنِ (8)
Shin bamu sanya masa idanu biyu ba?
وَلِسَانًا وَشَفَتَيْنِ (9)
Da harshe da labba biyu?
وَهَدَيْنَاهُ النَّجْدَيْنِ (10)
Kuma Muka shiryar dashi hanyoyi guda biyu?

Sharhi: Shin baMu sanya masa idanu biyu bane wadanda yake gani da su? Da harce da labba biyu wadanda yake magana da su? Kuma Muka bayyana masa hanyoyi biyu na alkhairi da sharri?
فَلَا اقْتَحَمَ الْعَقَبَةَ (11)
To bai shiga akaba ba (wato bai aikata abinda zai kubutar dashi daga azabar wuta)?

Sharhi: To me yasa bai tsira daga wahalar lahira ba da abin da ya ciyar na dukiya sai ya aminta?
وَمَا أَدْرَاكَ مَا الْعَقَبَةُ (12)
Kuma me ya sanar da kai abin da ake cewa akaba?

Sharhi: To wani abune ya sanar da kai wahalar lahira? Kuma menene ke taimakawa wurin tsira daga gare ta?
فَكُّ رَقَبَةٍ (13)
Itace fansar wuyan bawa.
أَوْ إِطْعَامٌ فِي يَوْمٍ ذِي مَسْغَبَةٍ (14)
Ko kuma ciyarwa a cikin yini ma'abucin yunwa.
يَتِيمًا ذَا مَقْرَبَةٍ (15)
Ga maraya ma'abucin kusanci (dangantaka)
أَوْ مِسْكِينًا ذَا مَتْرَبَةٍ (16)
Ko kuma wani miskini wanda alamar talauci ta bayyana a gareshi.

Sharhi: Ko ciyarwa a cikin wani yini mai tsananin yunwa – maraya wanda mahaifinsa ya rasu yana karami- daga cikin ma'abuta kusanci sai falalar sadaka da ta zumunta su hadu. Ko fakiri wanda bashi da komai.
ثُمَّ كَانَ مِنَ الَّذِينَ آمَنُوا وَتَوَاصَوْا بِالصَّبْرِ وَتَوَاصَوْا بِالْمَرْحَمَةِ (17)
Sa'annan kuma ya kasance daga wadanda sukayi imani kuma sukayi wa juna wasiyya da hakuri kuma sukayiwa juna wasiyya da tausayi.

Sharhi: Sa'annan tare da abinda aka ambata na aikin alheri daga wadanda suka tsarkake imaninsu ga Allah, kuma sashinsu yayi wa sashi wasiyya da hakuri akan yiwa Allah da'a da barin sabonSa, kuma suka yiwa juna wasiyya da tausayawa halittu.
أُولَئِكَ أَصْحَابُ الْمَيْمَنَةِ (18)
Wadannan sune ma'abuta dama (muminai).

Sharhi: Wadanda suka aikata wadannan ayyukan sune ma'abuta hanun dama, wadanda za'a yi ta hanun dama dasu zuwa aljanna.
وَالَّذِينَ كَفَرُوا بِآيَاتِنَا هُمْ أَصْحَابُ الْمَشْأَمَةِ (19)
Kuma wadanda suka kafirce wa ayoyinmu sune ma'abuta shu'umci.

Sharhi: Wadanda suka kafita da alkur'ani, sune za'a yi ta hanun hagu dasu ranar kiyama zuwa wuta.
عَلَيْهِمْ نَارٌ مُؤْصَدَةٌ (20)
Akansu akwai wata wuta kullalliya.

Sharhi: Sakamakonsu shine jahannama, tana mai yin daidai da su garkamammiya akan su.