المساعد الشخصي الرقمي

مشاهدة النسخة كاملة : Darasi na goma sha shida:tarjaman tafsirin suratul fajri daga littafin attafsisul muyassar


طاهر جبريل دكو
_27 _January _2014هـ الموافق 27-01-2014م, 01:48 AM
وَالْفَجْرِ (1)

Ina rantsuwa da alfijir.



وَلَيَالٍ عَشْرٍ (2)

Da darere goma.



وَالشَّفْعِ وَالْوَتْرِ (3)

Da adadi na cika dana mara.



وَاللَّيْلِ إِذَا يَسْرِ (4)

Da dare idan yana shudewa.



هَلْ فِي ذَلِكَ قَسَمٌ لِذِي حِجْرٍ (5)

Shin ko a cikin wannan akwai rantsuwa ga mai hankali?





Sharhi: Allah (tsarkakakke) Ya rantse da lokacin safiya, da darere goma na farkon zulhijja da abinda ta daukaka sabodashi, da dukkanin adadi na cika da na mara, da dare idan duhunsa na shudewa, ashe acikin wadannan rantse rantsen da aka amabta babu abinda ke gamsar da mai hankali?

أَلَمْ تَرَ كَيْفَ فَعَلَ رَبُّكَ بِعَادٍ (6)

Baka ga yadda Ubangijinka Ya aikata da Adawa ba?



إِرَمَ ذَاتِ الْعِمَادِ (7)

Iramawa ma'abuta kira (mai girma)



الَّتِي لَمْ يُخْلَقْ مِثْلُهَا فِي الْبِلَادِ (8)

Wadanda ba'a halicci kwatankwacinsu ba a cikin garuruwa.





Sharhi: Ashe – ya kai wannan manzo- baka ga yadda Ubangijinka Yayi da Adawa ba kabilar Iram? Ma'abuta karfi da gine gine madaukaka bisa gimshikai, wacce ba'a halicci misalinsu ba – a girman jiki da karfin yaki - a cikin garuruwa

وَثَمُودَ الَّذِينَ جَابُوا الصَّخْرَ بِالْوَادِ (9)

Da Samudawa da suka fafe duwatsu a cikin wadi sukayi gidaje.





Sharhi: Kuma yadda Ya aikata ga Samudawa mutanen Salihu wadanda suka fafe duwatsu suka rike su gidaje?

وَفِرْعَوْنَ ذِي الْأَوْتَادِ (10)

Da fir'auna mai turaku.





Sharhi: Kuma yadda Ya aikata ga fir'auna sarkin Masar ma'abucin rundunoni wadanda suka tabbatar da mulkinsa, kuma suka karfafi a'amuransa?

الَّذِينَ طَغَوْا فِي الْبِلَادِ (11)

Wadanda suka ketare iyaka a cikin garuruwa.



فَأَكْثَرُوا فِيهَا الْفَسَادَ (12)

Sai suka yawaita barna a cikinsu.



فَصَبَّ عَلَيْهِمْ رَبُّكَ سَوْطَ عَذَابٍ (13)

Saboda haka sai Ubangijinka Ya zuba musu nau'ukan azaba.



إِنَّ رَبَّكَ لَبِالْمِرْصَادِ (14)

Lallaine Ubangijinka tabbas Yana nan a madakata.





Sharhi: Wadannan sune wadanda suka kadaita, kuma suka yi zalunci a cikin garuruwan Allah, kuma suka yawaita barna a cikinsu, sai Ubangijinka Ya kwarara azaba mai tsanani a kansu. Lallai Ubangijinka - ya kai wannan manzon- tabbas Yana nan a madakata, Yana jinkirta wa mai saba maSa, sannu sannu, sa'annan sai Yayi masa kamu kamun mabuwayi mai cikakken kudura.

فَأَمَّا الْإِنْسَانُ إِذَا مَا ابْتَلَاهُ رَبُّهُ فَأَكْرَمَهُ وَنَعَّمَهُ فَيَقُولُ رَبِّي أَكْرَمَنِ (15)

To amma fa mutum idan Ubangijinsa Ya jarrabeshi, wato Ya girmamashi kuma Yayi masa ni'ima sai yace; Ubangijina Ya girmamani.





Sharhi: Amma shi mutum duk sa'adda Ubangijinsa Ya jarrabeshi da wata ni'ima kuma Ya yalwata masa arzikinsa, kuma Ya sanya shi a cikin rayuwa mai dadi, sai ya dauka wadannan abubuwan duka ya samesu ne saboda karimcinsa a wurin Ubangijinsa, saboda haka sai ya rika cewa; Ubangijina Ya karrama ni.

وَأَمَّا إِذَا مَا ابْتَلَاهُ فَقَدَرَ عَلَيْهِ رِزْقَهُ فَيَقُولُ رَبِّي أَهَانَنِ (16)

Kuma idan Ya jarrabeshi, wato Ya kuntata masa arzikinsa, sai yace Ubangijina Ya walakantani.





Sharhi: Kuma idan Ya jarrabeshi, Ya kuntata masa arzikinsa, sai yayi zaton cewa lallai hakan ya kasance ne sakamakon rashin matsayinsa ( a wurin Allah) saboda haka sai ya rika cewa; Ubangijina Ya walakantani.

كَلَّا بَلْ لَا تُكْرِمُونَ الْيَتِيمَ (17)

A'aha! Bahakaba, ai baku girmama marayu.



وَلَا تَحَاضُّونَ عَلَى طَعَامِ الْمِسْكِينِ (18)

Kuma baku kwadaitar da junanku gameda ciyar da miskini.



وَتَأْكُلُونَ التُّرَاثَ أَكْلًا لَمًّا (19)

Kuma kuna cin dukiyar gado ci na handama.



وَتُحِبُّونَ الْمَالَ حُبًّا جَمًّا (20)

Kuma kuna son dukiya so mai yawa.





Sharhi: Al'amarin ba kamar yadda wannan mutumin yake zato bane, a'a! karramawa sababinsa shine yiwa Allah da'a, walankantuwa kuma sababinsa shine sabon Allah. Ku kuma bakwa karrama maraya, wanda mahaifinsa ya rasu tun yana karami, kuma bakwa kyautata mu'amala gareshi, kuma sashinku baya kwadaitar da sashi akan ciyar da mabukaci, wanda bai mallaki abinda zai isheshi ba kuma ya biya masa bukata, kuma kuna danne hakkokin wasu a cikin gado dannewa mai tsanani, kuma kuna son dukiya son da ya wuce misali.

كَلَّا إِذَا دُكَّتِ الْأَرْضُ دَكًّا دَكًّا (21)

A'aha! Idan aka nike kasa nikewa mai tsanani.



وَجَاءَ رَبُّكَ وَالْمَلَكُ صَفًّا صَفًّا (22)

Kuma Ubangijinka yazo alhali mala'iku suna jere sahu sahu.





Sharhi: Ba haka ya kamata halinku ya kasance ba, idan aka girgiza kasa kuma sashinta ya karya sashi, kuma Ubangijinka Ya taho domin yin hukunci a tsakanin halittunSa alhali mala'iku suna (jere) sahu sahu

وَجِيءَ يَوْمَئِذٍ بِجَهَنَّمَ يَوْمَئِذٍ يَتَذَكَّرُ الْإِنْسَانُ وَأَنَّى لَهُ الذِّكْرَى (23)

Kuma a ranan nan za'a zo da jahannama, a wannan ranar mutum zai yi tunani, to infa tunani zai amfaneshi.



يَقُولُ يَا لَيْتَنِي قَدَّمْتُ لِحَيَاتِي (24)

Yana cewa; ya kaitona! Da na gabatar (da aikin kwrai) domin rayuwata.





Sharhi: Kuma a taho da jahannama a wannan yinin mai girma, a wannan yinin kafiri zai wa'aztu kuma ya tuba, amma ta yaya wa'aztuwa da tuba zasu amfaneshi bayan ya riga yayi sakaci a cikinsu a duniya kuma lokacin su ya kure? Zai rika cewa; ya kaito na! inama da na gabatar – tun a dunia - ayyukan da zasu amfaneni a rayuwata ta lahira.

فَيَوْمَئِذٍ لَا يُعَذِّبُ عَذَابَهُ أَحَدٌ (25)

To a ranar nan babu wani mai yin azaba irin azabar Allah.



وَلَا يُوثِقُ وَثَاقَهُ أَحَدٌ (26)

Kuma babu wani mai dauri irin daurinSa.





Sharhi: A wannan ranan mai tsananin wahala babu wanda zai iya yin azaba irin azabar Allah ga wanda ya saba masa, kuma babu wanda zai iya yin dauri irin daurin Allah, babu wanda zai iya kaiwa matuka cikin haka kamar naSa.

يَا أَيَّتُهَا النَّفْسُ الْمُطْمَئِنَّةُ (27)

Ya ke rai mai natsuwa.





ارْجِعِي إِلَى رَبِّكِ رَاضِيَةً مَرْضِيَّةً (28)

Ki koma zuwaga Ubangijinki alhali kina mai yarda (da sakamakon da za'a baki a lahira) kuma abar yardarwa (daga Ubangijinki).



فَادْخُلِي فِي عِبَادِي (29)

Saboda haka ki shiga cikin bayiNa (masu biyayya gareNi a duniya).



وَادْخُلِي جَنَّتِي (30)

Kuma ki shiga aljannaTa.





Sharhi: Ya ke rai wacce ta natsu da ambaton Allah da imani daShi da abinda Ya tanadar na ni'ima ga muminai, ki koma zuwa ga Ubangijinki kina mai yarda da karramawar Allah gare ki, kuma hakika Allah Ya yarda da ke. Saboda haka ki shiga cikin bayin Allah salihai, kuma ki shiga aljannaTa tare da su.