تسجيل الدخول

مشاهدة النسخة كاملة : Darasi na goma sha shida tarjaman tafsirin suratul ghashiya daga littafin attafsirul muyassar


طاهر جبريل دكو
_23 _January _2014هـ الموافق 23-01-2014م, 09:31 AM
هَلْ أَتَاكَ حَدِيثُ الْغَاشِيَةِ (1)
Hakika labarin (alkiyama) mai rufe mutane da abinda ke cikinta na firgici yazo maka.

Sharhi: shin – ya kai wannan manzon- labarin tashin alkiyama wanda ke lullube mutane da wahalhalunsa ya zo maka?
وُجُوهٌ يَوْمَئِذٍ خَاشِعَةٌ (2)
Wasu fuskoki a wannan yinin, makaskantane.
عَامِلَةٌ نَاصِبَةٌ (3)
Masu aikin wahalane gajiyayyu.
تَصْلَى نَارًا حَامِيَةً (4)
Zasu shiga wuta mai tsananin zafi.
تُسْقَى مِنْ عَيْنٍ آنِيَةٍ (5)
Ana shayar dasu daga wani marmaro mai zafin ruwa.
لَيْسَ لَهُمْ طَعَامٌ إِلَّا مِنْ ضَرِيعٍ (6)
Basu da wani abinci face dai daga danyi.
لَا يُسْمِنُ وَلَا يُغْنِي مِنْ جُوعٍ (7)
Baya sanya kiba kuma baya wadatarwa daga yunwa.

Sharhi: Fusakun kafirai a wannan ranar kaskantattune saboda azaba, aiki ya wahalar da su sun gaji, wata wuta zata shafe su mai tsananin ruruwa, za'a shayar dasu daga wani idon ruwa wanda ya kai makura a zafi, yan wuta basu da wani abinci face wani tsiro mai kayoyi wanda yake manne da kasa kuma shi yana daga cikin mafi sharrin abinci kuma mafi muninsa, baya sanya jikin mai cinsa yayi kiba daga rama, kuma baya magance yunwarsa.
وُجُوهٌ يَوْمَئِذٍ نَاعِمَةٌ (8)
Wasu fuskokin kuma a wannan yinin sun cikin ni'ima.
لِسَعْيِهَا رَاضِيَةٌ (9)
Gameda aikinsu (na kwarai a duniya) masu yardane (da sakamakon da zasu gani a lahira).
فِي جَنَّةٍ عَالِيَةٍ (10)
A cikin aljanna madaukakiya.
لَا تَسْمَعُ فِيهَا لَاغِيَةً (11)
Ba zasu jin wata yasashshiyar magana.
فِيهَا عَيْنٌ جَارِيَةٌ (12)
A cikinta akwai marmaro mai gudana.
فِيهَا سُرُرٌ مَرْفُوعَةٌ (13)
Da gadaje madaukaka.
وَأَكْوَابٌ مَوْضُوعَةٌ (14)
Da kofuna ajiyayyu.
وَنَمَارِقُ مَصْفُوفَةٌ (15)
Da filulluka jerarru.
وَزَرَابِيُّ مَبْثُوثَةٌ (16)
Da katifu shimfidaddu.

Sharhi: Fusakum muminai a ranar kiyama ma'abuta ni'ima ce. Saboda ayyukansu a duniya, su yardaddune a lahira, a cikin aljanna ma'abuciyar daukaka, (daukaka) na wuri da(daukaka) na matsayi, basu jin yasashshiyar kalma koda daya, cikinta akwai marmaro da ruwanta ke bubbuga, cikinta akwai gadaje madaukaka, da kofuna da aka tanadar ga mashaya, da filulluka jerarru wani gefen wani, da katifu masu yawa shimfidaddu.
أَفَلَا يَنْظُرُونَ إِلَى الْإِبِلِ كَيْفَ خُلِقَتْ (17)
Ashe ba zasu yi dubi ba zuwa ga rakuma, yadda aka halitta su?
وَإِلَى السَّمَاءِ كَيْفَ رُفِعَتْ (18)
Kuma zuwa ga sama yadda aka daukaka ta.
وَإِلَى الْجِبَالِ كَيْفَ نُصِبَتْ (19)
Kuma zuwa ga duwatsu yadda aka kafa su.
وَإِلَى الْأَرْضِ كَيْفَ سُطِحَتْ (20)
Kuma zuwa ga kasa yadda aka shimfida ta.

Sharhi: Wai shin kafirai masu karyatawa baza suyi dubi (da idon basira) bane zuwa rakuma; yadda aka halittasu irin wannan halittan mai ban mamaki? Da kuma sama yadda aka daukaka ta irin wannan daukakawar da ba kamarsa? Da kuma duwatsu yadda aka kafasu sai kasa ta samu kafuwa da tabbatuwa dasu? Da kuma kasa yadda aka shimfida ta kuma aka fadada ta?
فَذَكِّرْ إِنَّمَا أَنْتَ مُذَكِّرٌ (21)
Saboda haka kayi wa'azi, kai mai wa'azine kawai.
لَسْتَ عَلَيْهِمْ بِمُصَيْطِرٍ (22)
Baka kasance mai tilastawa ba akansu.

Sharhi: Saboda haka, kayi wa'azi – ya kai wannan manzon- ga masu kawar da kai, da abinda aka aiko ka da shi zuwa gare su, kuma kada kayi bakin ciki game da juya bayansu, kai kawai mai wa'azi ne gare su, tilastasu akan yin imani ba akan ka yake ba.
إِلَّا مَنْ تَوَلَّى وَكَفَرَ (23)
Face dai wanda ya juya baya kuma ya kafirtce.
فَيُعَذِّبُهُ اللَّهُ الْعَذَابَ الْأَكْبَرَ (24)
Sai Allah Ya azabtar da shi wannan azabar mafi girma.

Sharhi: Sai dai wanda ya kawar da kai daga gargadi da wa'azi kuma ya doge akan kafircinsa, to Allah zai masa azaba, azaba mai tsanani a cikin wuta.
إِنَّ إِلَيْنَا إِيَابَهُمْ (25)
Lallaine makomarsu zuwa garemu take.
ثُمَّ إِنَّ عَلَيْنَا حِسَابَهُمْ (26)
Sa'annan aikinMu ne Muyi musu hisabi.

Sharhi: Lallai makomarsu bayan mutuwa gareMu take, sa'annan lallai sakanta musu akan abinda suka aiwatar akan Mu yake.