تسجيل الدخول

مشاهدة النسخة كاملة : الدرس الخامس عشر: ترجمة تفسير سورة الأعلى من كتاب: التفسير الميسر


طاهر جبريل دكو
_22 _January _2014هـ الموافق 22-01-2014م, 09:24 AM
سَبِّحِ اسْمَ رَبِّكَ الْأَعْلَى (1)
Ka tsarkake sunan Ubangijin ka madaukaki.
الَّذِي خَلَقَ فَسَوَّى (2)
Wanda Yayi halitta kuma Ya daidaita abin halittar.
وَالَّذِي قَدَّرَ فَهَدَى (3)
Wanda Ya kaddara, sa'annan Ya shiryar.
وَالَّذِي أَخْرَجَ الْمَرْعَى (4)
Wanda Ya fitar da makiyaya.
فَجَعَلَهُ غُثَاءً أَحْوَى (5)
Sa'annan Ya maida ita baka kekasashshiya.

Sharhi: tsarkake sunan Ubangijinka madaukaki daga abokin tarayya da nakasoshi tsarkakewan da yake dacewa da girmama Sa (tsarkakakke) wanda Ya halicci dukkanin halittu, kuma Ya kyautata halittanta kuma Ya inganta shi. Wanda Ya kaddara dukkan kaddararrun abubuwa sa'annan Ya shiyaryar da kowace halitta zuwa ga abinda ke dacewa da ita, kuma (Shine) wanda Ya tsirar da korayen ciyayi sai Ya sanyashi yamutsatstse busashshe wanda ya jirkita zuwa bakin launi bayan da ya kasance danye sharaf.
سَنُقْرِئُكَ فَلَا تَنْسَى (6)
zaMu karantar da kai (Alkur'ani) saboda haka baza ka manta (shi) ba.
إِلَّا مَا شَاءَ اللَّهُ إِنَّهُ يَعْلَمُ الْجَهْرَ وَمَا يَخْفَى (7)
Sai dai abinda Allah Yaso, lallaine Shi Ya san bayyananne da abinda ke boye.

Sharhi: Da sannu zaMu karantar da kai – ya kai wannan manzon- wannan Alkur'anin karantarwan da ba zaka manta shi ba, sai dai abinda Allah Ya nufa, daga cikin abin da hikimarSa ta hukunta Ya mantar da shi saboda wata maslaha wacce Shi Ya sani, lallai Shi – subhanahu- Yana sanin abin da ke bayyane na magana da aiki da abinda ya buya daga ciki.
وَنُيَسِّرُكَ لِلْيُسْرَى (8)
Kuma zaMu sawwake maka zuwa ga sauki.
Sharhi: Kuma zaMu sawwake maka zuwa ga sauki cikin dukkan al'amura, daga cikin haka; akwai sawwake daukan nauyi da wahalhalun manzanci, da sanya addininka mai sauki babu tsanani a cikinsa.
فَذَكِّرْ إِنْ نَفَعَتِ الذِّكْرَى (9)
Saboda haka ka tunatar, idan tunatarwar zata yi amfani.
سَيَذَّكَّرُ مَنْ يَخْشَى (10)
Wanda yake tsoron Allah zai fadaka.

Sharhi: Saboda haka – ya kai wannan manzon- kayi gargadi ga mutanenka da abinda ake maka wahayinsa gwargwadon yadda Muka sawwake maka, kuma ka shiryar dasu zuwa ga abinda alkhairinsu ke cikinsa, ka kebance wanda ake masa tsammanin shiryuwa da tunatarwarka kada ka gajiyar da kanka a cikin tunatar da wanda tunatarwa bata kara masa komai face kangara da gudun (gaskiya), da sannu mai tsoron Ubangijinsa zai wa'aztu.
وَيَتَجَنَّبُهَا الْأَشْقَى (11)
Shakiyyi kuma zai nisanceta.

الَّذِي يَصْلَى النَّارَ الْكُبْرَى (12)
Wanda zai shiga wutannan mai girma.
ثُمَّ لَا يَمُوتُ فِيهَا وَلَا يَحْيَى (13)
Sa'annan bazai mutu ba a cikinta kuma ba zai rayu ba.
قَدْ أَفْلَحَ مَنْ تَزَكَّى (14)
Hakika wanda ya tsarkaka (daga kafirci da sabo) ya rabauta
وَذَكَرَ اسْمَ رَبِّهِ فَصَلَّى (15)
Kuma ya ambaci sunan Ubangijinsa sa'annan yayi sallah.

Sharhi: Kuma shakiyyi wanda baya tsoron Ubangijinsa zai nisanci wannan tunatarwan, wanda da sannu zai shiga wutar jahannama mai girma ya dandani zafinta, sa'annan kuma ba zai mutu ba a cikinta ballantana ya huta haka nan kuma ba zai rayu ba rayuwar da zata amfane shi. Hakika wanada ya tsarkake ransa daga munanan dabi'u kuma ya ambaci Allah, ya kadaitaShi, ya kirayeShi ya kuma aikata abinda ke yardar da Shi, kuma ya tsaida salla a cikin lokutanta alhali yana mai neman yardan Allah da bin shari'arSa ya rabauta.
بَلْ تُؤْثِرُونَ الْحَيَاةَ الدُّنْيَا (16)
Ba haka ba! Kuna fifita rayuwar duniya ce.

Sharhi: Lallai ku – mutane- kuna fifita kawa ta rayuwar duniya akan ni'imar lahira.
وَالْآخِرَةُ خَيْرٌ وَأَبْقَى (17)
Alhali lahira itace mafi alkhairi kuma mafi wanzuwa.

Sharhi: Alhali gidan lahira da abinda ke cikinta na ni'ima dawwamammiya itace mafi alkhairi sama da duniya kuma ita tafi wanzuwa.
إِنَّ هَذَا لَفِي الصُّحُفِ الْأُولَى (18)
Lallaine wannan yana cikin littattafan farko.
صُحُفِ إِبْرَاهِيمَ وَمُوسَى (19)
Littattafan Ibrahima da Musa.
Sharhi: Lallai abinda aka labarta muku a cikin wannan surar, shine abinda ma'anarsa ta tabbata a cikin littattafan da aka saukar kafin Alkur'ani, sune littattafan Ibrahima da Musa (amincin Allah ya tabbata a garesu.