المساعد الشخصي الرقمي

مشاهدة النسخة كاملة : عشرة موارد للذكر في القرآن الكريم


هيئة الإشراف
_16 _January _2014هـ الموافق 16-01-2014م, 12:36 AM
عشرة موارد للذكر في القرآن الكريم


قال رحمه الله في "مدارج السالكين" في موارد الذكر في القرآن الكريم: (فصل: وهو في القرآن على عشرة أوجه:
الأول: الأمرُ به مطلقا ومقيدا.
الثاني: النهيُ عن ضدِّه من الغفلةِ والنسيان.
الثالث: تعليقُ الفلاحِ باستدامتِه وكثرتِه.
الرابع: الثناءُ على أهلهِ، والإخبارُ بما أعدَّ الله لهم من الجنة والمغفرة.
الخامس: الإخبارُ عن خُسرانِ من لَها عنه بغيره.
السادس: أنَّه سبحانه جعلَ ذِكْرَهُ لهم جزاءَ لذِكْرِهِم له.
السابع: الإخبارُ أنَّه أكبرُ من كلَّ شيء.
الثامن: أنه جعلَه خاتمةَ الأعمالِ الصالحةِ كما كان مفتاحَها.
التاسع: الإخبارُ عن أهلِه بأنَّهم هم أهلُ الانتفاعِ بآياتهِ وأنَّهمْ أولو الألبابِ دونَ غيرهم.
العاشر: أنه جعلَه قرينَ جميعِ الأعمالِ الصالحةِ ورُوحَها فمتَى عَدِمَتْهُ كانت كالجسدِ بلا رُوح.

فصل في تفصيل ذلك:
- أما الأول: فكقوله تعالى: {يا أيها الذين آمنوا اذكروا الله ذكرا كثيرا وسبحوه بكرة وأصيلا هو الذي يصلي عليكم وملائكته ليخرجكم من الظلمات إلى النور وكان بالمؤمنين رحيما}، وقوله تعالى: {واذكر ربك في نفسك تضرعا وخيفة}، وفيه قولان:
أحدهما: في سرِّكَ وقلبِكَ.
والثاني: بلسَانِك بحيثُ تُسْمِعُ نفسَك.
- وأما النهيُ عن ضدِّهِ؛ فكقوله: {ولا تكن من الغافلين}، وقوله: {ولا تكونوا كالذين نسوا الله فأنساهم أنفسهم}.
- وأما تعليق الفلاح بالإكثار منه ؛ فكقوله: {واذكروا الله كثيرا لعلكم تفلحون}.
- وأما الثناءُ على أهله وحسنِ جزائِهم ؛ فكقوله: {إن المسلمين والمسلمات..} إلى قوله: {والذاكرين الله كثيراً والذاكرات أعدَّ الله لهم مغفرة وأجراً عظيما}.
- وأما خُسْران من لها عنه ؛ فكقوله تعالى: {يا أيها الذين آمنوا لا تلهكم أموالكم ولا أولادكم عن ذكر الله ومن يفعل ذلك فأولئك هم الخاسرون}.
- وأما جعل ذِكْرِهِ لهم جزاءً لِذِكْرِهِمْ له ؛ فكقوله: {فاذكروني أذكركم واشكروا لي ولا تكفرون}
- وأما الإخبارُ عنه بأنَّه أكبرُ من كلِّ شيء ؛ فكقوله تعالى: {اتل ما أوحي إليك من الكتاب وأقم الصلاة إن الصلاة تنهى عن الفحشاء والمنكر ولذكر الله أكبر} ، وفيها أربعة أقوال:
* أحدها: أنَّ ذِكْرَ اللهِ أكبرُ من كلِّ شيء فهو أفضلُ الطاعات لأن المقصودَ بالطاعات كلها إقامةُ ذكرِه؛ فهو سرُّ الطاعاتِ ورُوحها.
* الثاني: أنَّ المعنى: أنكم إذا ذكرتموه ذكَرَكم فكان ذِكْرُه لكم أكبرُ من ذكرِكُم له؛ فعلى هذا: المصدر مضاف إلى الفاعل، وعلى الأول: مضاف إلى المذكور.
* الثالث: أنَّ المعنى: ولذكر الله أكبرُ من أن يبقى معه فاحشة ومنكر، بل إذا تم الذِّكْرُ مَحَقَ كلَّ خطيئةٍ ومعصيةٍ.
هذا ما ذكره المفسرون.
* وسمعت شيخ الإسلام ابن تيمية رحمه الله يقول: (معنى الآية: أن في الصلاة فائدتين عظيمتين إحداهما : نهيها عن الفحشاء والمنكر، والثانية : اشتمالها على ذكر الله وتضمنها له، ولَمَا تضمنتْهُ من ذِكْرِ اللهِ أعظمُ من نهيها عن الفحشاء والمنكر).
- وأما ختم الأعمال الصالحة به؛ فكما ختم به عمل الصيام بقوله : {ولتكملوا العدة ولتكبروا الله على ما هداكم ولعلكم تشكرون}، وختم به الحج في قوله: {فإذا قضيتم مناسككم فاذكروا الله كذكركم آباءكم أو أشد ذكرا}.
وختم به الصلاة كقوله: {فإذا قضيتم الصلاة فاذكروا الله قياما وقعودا وعلى جنوبكم}.
وختم به الجمعة كقوله: {فإذا قضيت الصلاة فانتشروا في الأرض وابتغوا من فضل الله واذكروا الله كثيرا لعلكم تفلحون}.
ولهذا كان خاتمة الحياة الدنيا، وإذا كان آخر كلام العبد: أدخله الله الجنة.
- وأما اختصاص الذاكرين بالانتفاع بآياته وهم أولو الألباب والعقول؛ فكقولِهِ تعالى: {إن في خلق السموات والأرض واختلاف الليل والنهار لآيات لأولى الألباب الذين يذكرون الله قياما وقعوداوعلى جنوبهم}.
- وأما مصاحبتُه لجميعِ الأعمالِ واقترانِهِ بها وأنَّه رُوحُها: فإنَّه سبحانه قرَنَه بالصَّلاةِ كقوله: {وأقم الصلاة لذكري}، وقَرَنَه بالصيامِ وبالحجِّ ومناسكِه، بل هو رُوحُ الحجِّ ولبُّه ومقصودُه كما قالَ النبيُّ صلى الله عليه وسلم: (( إنما جعل الطواف بالبيت والسعي بين الصفا والمروة ورمي الجمار : لإقامة ذكر الله)).
وقرنه بالجهاد وأمر بذكرِه عند ملاقاةِ الأقرانِ ومكافحةِ الاعداءِ؛ فقال تعالى: {يا أيها الذين آمنوا إذا لقيتم فئة فاثبتوا واذكروا الله لعلكم تفلحون}.
وفي أثر إلهي يقول الله تعالى: (إن عبدي كلَّ عبدي الذي يذكرني وهو ملاقٍ قِرْنَه).
سمعت شيخ الإسلام ابن تيمية قدس الله روحه يستشهد به، وسمعته يقول: المحبون يفتخرون بذكر من يحبونه في هذه الحال كما قال عنترة:
ولقد ذكرتكِ والرماحُ كأنها ... أشطانُ بئرٍ في لَبَانِ الأدهَمِ

وقال الآخر :
ذكرتُكِ والخطيُّ يخطُرُ بيننا ... وقد نهلتْ منا المثقَّفَةُ السُّمْرُ

وقال آخر :
ولقد ذكرتُكِ والرِّمَاحُ شواجرٌ ... نَحْوِي وبِيضُ الهندِ تقطرُ من دَمِي

وهذا كثير في أشعارهم وهو مما يدلّ على قوة المحبة؛ فإنَّ ذكرَ المحبِّ محبوبَهُ في تلكِ الحالِ التي لا يهمُّ المرءَ فيها غيرُ نفسِهِ يدلُّ علَى أنَّهُ عندَهُ بمنزلةِ نفسِهِ أو أعزُّ منها، وهذا دليلٌ على صدقِ المحبَّةِ، والله أعلم).

طاهر جبريل دكو
_13 _November _2014هـ الموافق 13-11-2014م, 11:14 PM
عشرة موارد للذكر في القرآن الكريم
HANYOYI GOMA NA ZUWAN ZIKIRI A CIKIN ALKUR'ANI MAI GIRMA.

Fuskoki ne guda goma.
Na daya: Umurni da shi a umurni a sake da (umurni) kayyadajje.
Na biyu: Hani game da kishiyarsa kamar gafala da mantuwa.
Na uku: Rataya samun rabo da yin sa da dawwama a cikin yin sa da yawaita shi.
Na hudu: Yabon ma'abutan sa da bada labari game da tanadin da Allah Ya yi mu su na Aljanna da gafara.
Na biyar: Bada labari game da hasarar wanda ya wani abu ya shagaltar ga barin sa (watau zikiri)
Na shida: Allah (سبحانه وتعالى) Ya sanya ambatonSa gare su (ya zama) sakayyar ambatonsu gare Shi.
Na bakwai: Bada labarin cewa ya fi komai girma.
Na takwas: Ya sanya shi (zikiri) a karshen kyawawan ayyuka kamar yadda ya kasance shi ne farkonsa.
Na tara: bada labari cewa ma'abutansa su ne ma su amfanuwa da ayoyinSa kuma su ne ma'abuta hankali koma bayan waninsu.
Na goma: Ya sanya shi abokin tafiya ga dukkan ayyuka na kwarai kuma ruhi gare su, saboda haka duk sa'adda aka rasa shi (wato zikiri a cikin aiki), sai (aikin) ya zama tamkar gangan jiki ne babu rai.
Fasali: Bayanin wadannan fuskokin na zikiri a cikin Alkur'ani dalla - dalla.
Na Daya: Kamar fadinSa –Maxaukaki

ﯺ ﯻ ﯼ ﯽ ﯾ ﯿ ﰀ ﰁ ﰂ ﰃ ﰄ ﰅ ﰆ ﰇ ﰈ ﰉ ﰊ ﰋ ﰌ ﰍ ﰎ ﰏﰐ ﰑ ﰒ ﰓ الأحزاب: ٤١ – ٤٣
Ma'ana: Ya ku wadanda su ka yi imani! ku ambaci Allah Ambato mai yawa (41) kuma ku tsarkake Shi safiya da maraaice (42) Shi ne wanda Ya ke yi muku salati da mala'ikunSa domin Ya fitar da ku daga duffai zuwa haske, kuma Ya kasance mai jin kai ga muminai (43) Ahzab 41-43
Da faxinSa – maxauakaki
ﯢ ﯣ ﯤ ﯥ ﯦ ﯧ ﯲ الأعراف: ٢٠٥
Ma'ana: Kuma ka ambaci Ubangijinka a cikin ranka kana mai kankan da kai kuma kana mai boyewa Al'a'raf 205
An yi maganganu guda biyu (game da ma'anar wannan ayar) na dayansu; (ka ambaci Allah) ka na mai sirrantawa kuma cikin zuciyarka. Na biyu: (ka ambaci Allah) da harcenka ta yadda za ka jiyar da kanka.

Na Biyu Inda hani ya zo game da kishiyarsa (watau zikiri) kuma: kamar fadinSa
ﯮ ﯯ ﯰ ﯱ ﯲ الأعراف: ٢٠٥
Ma'ana: Ka da ka zamo daga cikin gafalallu. A'raf 205
Da faxinSa
ﭱ ﭲ ﭳ ﭴ ﭵ ﭶ ﭷ الحشر: ١٩
Ma'ana: Ka da ku kasance kamar wadanda suka manta da Allah sai Allah Ya mantaddasu kawukansu Hashr 19
Na Uku Inda aka rataya rabauta da yawaita shi kuwa kamar fadinSa
ﭲ ﭳ ﭴ ﭵ ﭶ ﭷ الجمعة: ١٠
Ma'ana: Kuma ku ambaci Allah da yawa tsammanin ku za ku rabauta. Jumu'atu 10
Na Hudu Yabon ma'abuta zikiri da (ambaton) kyakkyawan sakamakonsu kuwa, kamar fadinSa

ﮢ ﮣ ﮤ ……………إلى قوله ﯗ ﯘ ﯙ ﯚ ﯛ ﯜ ﯝ ﯞ ﯟ ﯠ الأحزاب: ٣٥
Ma'ana: Lallai Musulmai maza da Musulmai mata………. Har izuwa fadinSa ; da ma su yawan ambaton Allah cikin mazaje da ma su yawan ambaton Allah cikin mata Allah Ya yi musu tanadin wata gafara da sakamako mai girma. Ahzab 35
Na Biyar Amma (dalili akan) hasarar wanda ya shagala daga yin zikiri kuwa, kamar fadinSa – Madaukaki - :
ﮝ ﮞ ﮟ ﮠ ﮡ ﮢ ﮣ ﮤ ﮥ ﮦ ﮧﮨ ﮩ ﮪ ﮫ ﮬ ﮭ ﮮ ﮯ المنافقون: ٩
Ma'ana: Ya ku wadanda su ka yi imani! Kada dukiya da 'ya'yanku su shagaltar da ku daga ambaton Allah, wanda ya aikata haka to wadannan duk su ne ma su hasara. Munafiqun 9
Na Shida Amma dalili akan cewa Ya sanya ambatonSa gare su sakamako game da ambatonsu gare Shi, kamar fadinSa
ﯩ ﯪ ﯫ ﯬ ﯭ ﯮ ﯯ البقرة: ١٥٢
Saboda haka, ku ambace Ni, zan ambace ku, kuma ku gode miNi ka da ku butulce miNi. Baqara 152
Na Bakwai Amma ba da labarin cewa shi ne ma fi girma daga dukkan komai kamar fadin Allah – madaukaki - :
ﯚ ﯛ ﯜ ﯝ ﯞ ﯟ ﯠ ﯡﯢ ﯣ ﯤ ﯥ ﯦ ﯧ ﯨﯩ ﯪ ﯫ ﯬ العنكبوت: ٤٥
Ma'ana: Ka karanta abin da aka yi wahayin sa zuwa gare ka na littafi kuma ka tsai da salla, lallai salla ta na hana alfasha da abin ki, kuma wallahi ambaton Allah shi ne mafi girma. Ankabut 45
Akwai maganganu guda hudu (game da ma'anar wannan ayar)
(Magana) ta farko; cewa ambaton Allah ya fi komai girma, saboda haka shi ne mafificin da'a don abin da ake nufi da da'a dukkanin ta, shi ne tsayuwa da ambaton Allah, kuma (wannan) shi ne sirrin dukkanin biyayya kuma shi ne ruhinsa
(Magana) ta biyu: cewa ma'anar (ayar) ita ce; idan ku ka ambace Shi zai ambace ku, kuma ambatonSa gare ku ya fi ambatonku gare Shi (girma) akan haka kenan shi masdarin (wato Kalmar (ذكر ya na komaawa ne zuwa ga wanda ya yi aiki (wato bawa wanda shi ne ya ambaci Ubangijinsa, wanda sakamakon hakan ne sai Ubangijinsa Ya ambace shi da ambaton da ya fi nasa) akan ra'ayi na farko kuma zai zama masdarin (wato kalmar ذكر) ya na komawa ne ga abin da aka ambata kafin ita (wato tilawan abinda aka yi masa wahayin sa da tsaida salla)
(magana) ta uku: Cewa ma'anan ayar shi ne, ambaton Allah ya wuce ace wata alfasha ta saura a tare da shi ko abin ki, a a! idan har zikiri ya kai (zikiri), to zai shafe dukkan kurakurai da sabo, wadannan su ne maganganun da malaman tafsiri su ka ambata.
(Magana ta huxu) Kuma na ji Shekhul Islam Ibnu taimiyya – Allah Ya jikan sa - ya na cewa: ma'anan ayar ita ce; lallai a cikin salla akwai fa'idoji guda biyu ma su girma, na farkon su shi ne; hanin ta ga alfasha da munkari. Na biyun su shi ne; kasancewar ta na kunshe da dukkan nau'uka na ambaton Allah a cikin ta, kuma abin da ta ke kunshe da shi na ambaton Allah shi ya fi girma sama da hanin ta ga alfasha da munkari
Na Takwas - Amma sanya shi a karshen kyawawan ayyuka (wato rufe kyawawan ayyuka da zikiri a matsayin karshe gare su) shi ne kamar yadda aka cike aikin azumi da fadin Sa:
ﯟ ﯠ ﯡ ﯢ ﯣ ﯤ ﯥ ﯦ ﯧ ﯨ البقرة: ١٨٥
Ma'ana: Kuma domin ku cika adadin kuma ku girmama Allah a kan Ya shiryar da ku, kuma tsammanin ku za ku gode. Baqara 185
Kuma Ya rufe aikin hajji da shi cikin fadinSa
ﮞ ﮟ ﮠ ﮡ ﮢ ﮣ ﮤ ﮥ ﮦ ﮧ البقرة: ٢٠٠
Ma'ana: To idan ku ka kare ayyukanku (na hajji) sai ku ambaci Allah kamar ambatonku ga iyayenku ko kuwa ma fi tsanani ga ambato. (Bakara 200).
Kuma Ya cikata salla da ita, kamar fadinSa
ﮔ ﮕ ﮖ ﮗ ﮘ ﮙ ﮚ ﮛ ﮜ النساء: ١٠٣
Ma'ana: Sa'annan idan kun kare salla sai ku ambaci Allah daga tsaye da zaune da a kan sasaninku. Nisa'i 103
Kuma Ya cikata juma'a da shi kamar faxinSa:
ﭨ ﭩ ﭪ ﭫ ﭬ ﭭ ﭮ ﭯ ﭰ ﭱ ﭲ ﭳ ﭴ ﭵ ﭶ ﭷ الجمعة: ١٠
Ma'ana: Idan ku ka idar da salla, sai ku watsu a bayan kasa kuma ku nema daga falalar Allah, kuma ku ambaci Allah (Ambato mai) yawa tsammanin ku za ku rabauta. Jumu'atu 10

Saboda haka ne ma ya zama karshe na rayuwar Duniya, kuma idan ya kasance (shi ne) maganan bawa na karshe (wato zikiri) sai Allah Ya shigar da shi Aljanna.
Na Tara- Amma dalili a kan cewa ma su ambaton Allah su su ke amfanuwa da ayoyinSa, kuma (cewa) su ne Ulul'albab (wato ma'abuta hankula, shi ne) kamar fadinSa – Madaukaki
ﮉ ﮊ ﮋ ﮌ ﮍ ﮎ ﮏ ﮐ ﮑ ﮒ ﮓ ﮔ ﮕ ﮖ ﮗ ﮘ ﮙ ﮚ ﮛ آل عمران: ١٩٠ – ١٩١
Ma'ana: Lallai a cikin halittar Sammai da Kasa da sassabawar dare da yini akwai abin lura ga ma'abuta hankali (190) Wadanda su ke ambatan Allah a tsaye da zaune da kan sasaninsu (191) Ali Imran 190-191
Na Goma Amma kasancewar sa tare da dukkan ayyuka da alakantuwar sa da shi, da kuma cewa shi ne ruhinsa (wato zikiri shi ne ruhin ayyuka), saboda lallai (Allah) - Subahanahu – Ya alakanta shi da salla, kamar fadinSa
ﭟ ﭠ ﭡ ﭢ طه: ١٤
Ma'ana: Kuma ka tsaida salla saboda ambatoNa. Daha 14
Kuma Ya alakanta shi da Jihadi, Ya yi umurni da ambatonSa yayin haduwa da abokan gaba da fuskantarsu, sai ya ce:
ﯩ ﯪ ﯫ ﯬ ﯭ ﯮ ﯯ ﯰ ﯱ ﯲ ﯳ ﯴ ﯵ الأنفال: ٤٥
Ma'ana: Ya ku wadanda su ka yi imani! idan ku ka sadu da wata jama'a (abokan gaba) ku tabbata, kuma ku ambaci Allah (Ambato mai) yawa tsammanin ku za ku ci nasara. Amfal 45
Na ji Shekhul Islami Ibnu Taimiyya – Allah Ya tsarkake ransa – ya na kafa hujja da shi, kuma na ji shi ya na cewa;
Masoya suna alfahari da ambaton wanda su ke so a cikin wannan yanayin (wato a halin yaki) kamar yadda Antara ya ce;
ولقد ذكرتك والرماح كأنها ... أشطان بئر في لبان الأدهم
Wani kuma ya ce
ذكرتك والخطي يخطر بيننا ... وقد نهلت منا المثقفة السمر
Wani kuma ya ce
ولقد ذكرتك والرماح شواجر ... تحوي وبيض الهند تقطر من دمي

Kuma wannan ya na da yawa a cikin wake wakensu, kuma shi, ya na daga cikin abubuwa ma su nuni zuwa ga karfin soyayya, domin lallai ambaton masoyi ga wanda ya ke so a wannan irin yanayi da bawa bai sanin komai face kansa ya na nuni zuwa ga cewa matsayin Sa a wurinSa kamar shi kansa ne ko ma sama da haka, kuma wannan dalili ne akan soyayya ta gaskiya. Allah Shi ne mafi sani.