المساعد الشخصي الرقمي

مشاهدة النسخة كاملة : عشرة أسباب لانشراح الصدر


هيئة الإشراف
_16 _January _2014هـ الموافق 16-01-2014م, 12:35 AM
عشرة أسباب لانشراح الصدر

قال رحمه الله في "زاد المعاد": (فصل: فى أسباب شَرْحِ الصّدورِ، وحصولِها على الكمالِ له صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ
- فأعظم أسباب شرح الصدر: التوحيدُ وعلى حسب كماله، وقوته، وزيادته يكونُ انشراحُ صدر صاحبه، قال الله تعالى: {أَفَمَن شَرَحَ اللهُ صَدْرَهُ لِلإسْلامِ فَهُوَ عَلَى نُورٍ مِّنْ رَبِّه} [الزمر: 22]. وقال تعالى: {فَمَنْ يُرِدِ اللهُ أَن يَهْدِيَهُ يَشْرَحْ صَدْرَهُ لِلإسْلاَمِ، وَمَن يُرِدْ أَن يُضِلَّهُ يَجْعَلْ صَدْرَهُ ضَيِّقًا حَرَجاً كَأَنَّمَا يَصَّعَّدُ فِى السَّمَاءِ} [الأنعام: 125].
- فالهُدى والتوحيدُ مِن أعظم أسبابِ شرح الصدر، والشِّركُ والضَّلال مِن أعظم أسبابِ ضيقِ الصَّدرِ وانحراجِه.
- ومنها: النورُ الذى يقذِفُه الله فى قلب العبد، وهو نورُ الإيمان، فإنه يشرَحُ الصدر ويُوسِّعه، ويُفْرِحُ القلبَ؛ فإذا فُقِدَ هذا النور من قلبِ العبدِ، ضاقَ وحَرِجَ، وصارَ فى أضيقِ سجنٍ وأصعبه.
وقد روى الترمذى فى جامعه عن النبى صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، أنه قال: (( إذا دَخَلَ النور القلبَ، انْفَسَحَ وانشرحَ )).
قالوا: وما عَلاَمَةُ ذَلِكَ يَا رسُولَ اللهِ؟ قال: (( الإنَابَةُ إلى دارِ الخُلُودِ، والتَجَافِى عَنْ دَارِ الغُرُورِ، والاسْتِعْدادُ للمَوْتِ قَبْلَ نُزوله )).
فيُصيب العبد من انشراح صدْرِه بحسبِ نصيبِه من هذا النُّورِ، وكذلكَ النورُ الحِسِّى، والظلمةُ الحِسِّية، هذه تشرحُ الصدْر، وهذه تُضيِّقه.
- ومنها: العلم، فإنه يشرح الصدر، ويوسِّعه حتى يكون أَوسعَ من الدنيا، والجهلُ يورثه الضِّيق والحَصْر والحبس، فكلما اتَّسع علمُ العبد، انشرح صدره واتسع، وليس هذا لكل عِلم، بل للعلم الموروث عن الرسول صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، وهو العلمُ النافع، فأهلُه أشرحُ الناس صدراً، وأوسعهم قلوباً، وأحسُنهم أخلاقاً، وأطيبُهم عيشاً.
- ومنها: الإنابةُ إلى الله سبحانه وتعالى، ومحبتُه بكلِّ القلب، والإقبالُ عليه، والتنعُّم بعبادته، فلا شيءَ أشرحُ لصدرِ العبدِ من ذلك؛ حتى إنه ليقولُ أحياناً: إن كنتُ فى الجنة فى مثل هذه الحالة، فإني إذاً فى عيش طيب، وللمحبة تأثيرٌ عجيبٌ فى انشراح الصدر، وطيبِ النفس، ونعيم القلب، لا يعرفه إلا مَن أحسَّ به، وكلَّما كانت المحبَّة أقوى وأشدَّ، كان الصدرُ أفسحَ وأشرحَ، ولا يَضيق إلا عند رؤية البطَّالين الفارِغين من هذا الشأن، فرؤيتُهم قَذَى عينِه، ومخالطتُهم حُمَّى روحه.
ومِنْ أعظم أَسباب ضيق الصدر: الإعراضُ عن الله تعالى، وتعلُّقُ القلب بغيره، والغفلةُ عن ذِكره، ومحبةُ سواه، فإن مَن أحبَّ شيئاً غيرَ الله عُذِّبَ به، وسُجِنَ قلبُه فى محبة ذلك الغير، فما فى الأرض أشقى منه، ولا أكسف بالاً، ولا أنكد عيشاً، ولا أتعب قلباً، فهما محبتان: محبة هى جنة الدنيا، وسرور النفس، ولذةُ القلب، ونعيم الروح، وغِذاؤها، ودواؤُها، بل حياتُها وقُرَّةُ عينها، وهى محبةُ الله وحدَه بكُلِّ القلب، وانجذابُ قوى الميل، والإرادة، والمحبة كلِّها إليه.
ومحبةٌ هى عذاب الروح، وغمُّ النفس، وسِجْنُ القلب، وضِيقُ الصدر، وهى سببُ الألم والنكد والعناء، وهى محبة ما سواه سبحانه.
- ومن أسباب شرح الصدر: دوامُ ذِكرِه على كُلِّ حال، وفى كُلِّ موطن، فللذِكْر تأثير عجيبٌ فى انشراحِ الصَّدْرِ، ونعيم القلبِ، وللغفلةِ تأثيرٌ عجيبٌ فى ضِيقِه وحَبْسِه وعذابه.
- ومنها: الإحسانُ إلى الخَلْق ونفعُهم بما يمكنه من المال والجاهِ والنفع بالبدن، وأنواع الإحسان؛ فإن الكريمَ المحسنَ أشرحُ الناس صدراً، وأطيبُهم نفساً، وأنعمُهم قلباً، والبخيلُ الذى ليس فيه إحسان أضيقُ الناسِ صدراً، وأنكدُهم عيشاً، وأعظمُهم همَّاً وغمَّاً.
وقد ضربَ رسولُ الله صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ فى الصحيح مثلاً للبخيلِ والمتصدِّق، كمَثَل رَجُلينِ عليهما جُبَّتانِ مِنْ حديدٍ، كلَّما هَمَّ المُتَصَدِّقُ بصَدَقَةٍ، اتَّسَعتْ عليهِ وانبسَطَتْ، حتَّى يَجُرَّ ثيابَهُ وَتعفّيَ أثَرهُ، وكلما همَّ البخيلُ بِالصَّدَقَةِ، لَزِمَتْ كُلُّ حَلْقَةٍ مَكَانَهَا، وَلَمْ تَتَّسِعْ عَلَيْهِ.
فهذا مَثَلُ انشِراحِ صدر المؤمن المتصدِّق، وانفساح قلبه، ومثلُ ضِيقِ صدر البخيل وانحصارِ قلبه.
- ومنها: الشجاعة، فإنَّ الشجاعَ منشرحُ الصدر، واسع البِطَان، متَّسِعُ القلبِ، والجبانُ: أضيقُ الناس صدراً، وأحصرُهم قلباً، لا فرحةَ له ولا سرور، ولا لذَّةَ له، ولا نعيمَ إلا منْ جنس ما للحيوانِ البهيميِّ، وأما سرورُ الرُّوحِ ولذَّتُها ونعيمُها وابتهاجُها، فمحرَّمٌ على كل جَبانٍ، كما هو محرَّم علِى كل بخيلٍ، وعلى كُلِّ مُعرِضٍ عن الله سبحانه، غافلٍ عن ذِكرِه، جاهلٍ به وبأسمائه تعالى وصفاته ودِينه، متعلِّق القلبِ بغيره.
وإنَّ هذا النعيمَ والسرورَ يصير فى القبرِ رياضاً وجَنة، وذلك الضيقُ والحصر ينقلبُ فى القبر عذاباً وسجناً؛ فحال العبد فى القبر. كحال القلب فى الصدر، نعيماً وعذاباً وسجناً وانطلاقاً، ولا عبرةَ بانشراح صدر هذا لعارض، ولا بضيق صدرِ هذا لعارض، فإن العوارِضَ تزولُ بزوال أسبابها، وإنما المعوَّلُ على الصِّفة التى قامت بالقلب تُوجب انشراحه وحبسه، فهى الميزان.. والله المستعان.
- ومنها بل من أعظمها: إخراجُ دَغَلِ القَلْبِ من الصفات المذمومة التى تُوجب ضيقه وعذابه، وتحولُ بينه وبين حصول البُرء، فإن الإنسان إذا أتى الأسباب التى تشرحُ صدره، ولم يُخرِجْ تلك الأوصافَ المذمومة من قلبه، لم يحظَ مِن انشراح صدره بطائل، وغايته أن يكون له مادتان تعتوِرَانِ على قلبه، وهو للمادة الغالبة عليه منهما.
- ومنها: تركُ فضولِ النظر، والكلام، والاستماع، والمخالطةِ، والأكل، والنوم، فإن هذه الفضولَ تستحيلُ آلاماً وغموماً، وهموماً فى القلب، تحصُرُه، وتحبِسه، وتضيِّقهُ، ويتعذَّبُ بها، بل غالِبُ عذابِ الدنيا والآخرة منها، فلا إله إلا اللهُ ما أضيقُ صدَر مَن ضرب فى كل آفةٍ من هذه الآفات بسهم، وما أنكَدَ عيشَه، وما أسوأ حاله، وما أشدَّ حصرَ قلبه، ولا إله إلا الله، ما أنعمَ عيشَ مَنْ ضرب فى كل خَصلةٍ من تلك الخصال المحمودة بسهم، وكانت همتُّه دائرةً عليها، حائمةً حولها، فلهذا نصيب وافر مِنْ قوله تعالى: {إنَّ الأَبْرَارَ لَفِى نَعِيم} [الانفطار: 13] ولذلك نصيب وافر من قوله تعالى: {وإنَّ الفُجَّارَ لَفِى جَحِيمٍ} [الانفطار: 14] وبينهما مراتبُ متفاوتة لا يُحصيها إلا الله تبارك وتعالى.
والمقصود: أن رسولَ الله صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ كان أكملَ الخلق فى كلِّ صفة يحصُل بها انشراحُ الصدر، واتِّساعُ القلب، وقُرَّةُ العين، وحياةُ الروح، فهو أكملُ الخلق فى هذا الشرح والحياة، وقُرَّةِ العين مع ما خُصَّ به من الشرح الحِسِّىِّ،
وأكملُ الخلق متابعة له، أكملُهم انشراحاً ولذَّة وقُرَّة عين، وعلى حسب متابعته ينالُ العبد من انشراح صدره وقُرَّة عينه، ولذَّة روحه ما ينال، فهو صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ فى ذُروة الكمال مِن شرح الصدر، ورفع الذِكْر، ووضع الوِزْر، ولأتباعه من ذلك بحسب نصيبهم من اتِّباعه.. والله المستعانُ.
وهكذا لأتباعه نصيبٌ من حفظ الله لهم، وعصمتِه إياهم، ودفاعِه عنهم، وإعزازه لهم، ونصرِه لهم، بحسب نصيبهم من المتابعة، فمستقِلُّ ومستكثِر، فمَن وجد خيراً، فليحمد الله. ومَن وجد غير ذلك، فلا يلومنَّ إلا نفسه).

طاهر جبريل دكو
_6 _February _2015هـ الموافق 6-02-2015م, 05:25 PM
عشرة أسباب لانشراح الصدر
SABUBBA GOMA DA SU KE BUDE ZUCIYA
Ibnul Qayyim – Allah Ya jikan sa – acikin Zadul ma'ad ya ce:
Fasali game da sabubban da su ke bude zukata, da samun kamalarsu.
Mafi girma daga abubuwan da ke buda zuciya shi ne:
Tauhihdi, kuma da gwargwadon cikansa da karfinsa da karuwarsa ma'abucin sa zai samu buduwar zuciyarsa, Allah (madaukaki) Ya ce:
{أَفَمَن شَرَحَ اللهُ صَدْرَهُ لِلإسْلامِ فَهُوَ عَلَى نُورٍ مِّنْ رَبِّه} [الزمر: 22].
Ma'ana: "Shin fa wanda Allah Ya bude kirjinsa don musulunci sa'annan shi ya na kan haske daga Ubangijinsa" Suratuz Zumar aya ta 22.
Kuma Allah Ya ce:
{فَمَنْ يُرِدِ اللهُ أَن يَهْدِيَهُ يَشْرَحْ صَدْرَهُ لِلإسْلاَمِ، وَمَن يُرِدْ أَن يُضِلَّهُ يَجْعَلْ صَدْرَهُ ضَيِّقًا حَرَجاً كَأَنَّمَا يَصَّعَّدُ فِى السَّمَاءِ} [الأنعام: 125].
Ma'ana: "Domin haka wanda Allah Ya yi nufin shiryar da shi sai Ya budi zuciyarsa don musulunci. Wanda kuma Ya yi nufin Ya batar da shi sai Ya sanya kirjinsa ya zamo mai kunci matsattse kamar dai ya na takawa ne a cikin sama" Suratul An'am aya ta125.
Saboda haka da shiriya da tauhidi suna daga cikin mafi girman sabubban da ke buda zuciya, kamar yadda shirka da bata su ke su ne mafi girman sabubba da ke jawo kuncin zuciya da matsinsa.
Daga ciki akwai hasken da Allah ke jefawa a zuciyar bawa wanda shi ne hasken imani, domin ya na buda kirji ya yalwata shi kuma ya yaye kuncin zuciya. Idan aka rasa wannan hasken a zuciyar bawa, sai ya yi kunci ya shiga cikin halin takura kuma ya kasance a cikin kurkuku mafi kuncin kuma mafi wahalarsa.
Imamu Ttirmidhi ya ruwaito a cikin littafin sa Jami'u daga Annabi (salla Allahu alai hi wa sallam) ya ce:
(( إذا دَخَلَ النور القلبَ، انْفَسَحَ وانشرحَ )). قالوا: وما عَلاَمَةُ ذَلِكَ يَا رسُولَ اللهِ؟ قال: (( الإنَابَةُ إلى دارِ الخُلُودِ، والتَجَافِى عَنْ دَارِ الغُرُورِ، والاسْتِعْدادُ للمَوْتِ قَبْلَ نُزوله )).
Ma'ana: "idan haske ya shiga zuciya sai ya bude ya yalawata" sai su ka ce menene alamar hakan ya ma'aikin Allah? Sai ya ce:"mai da hankali zuwa ga gidan dawwama, da nisantar da zuciya daga gidan rudi, da yi wa mutuwa tanadi kafin saukarta"
Sai bawa ya samu buduwar zuciyarsa da gwargwadon kasonsa a wannan hasken. Haka nan ma haske wanda ake gani da ido da duhun da ake gani, hasken ya na buda kirji duhun kuma ya na kuntata shi.
Daga ciki akwai ilimi, lallai shi (ilimi) ya na bude zuciya ku ma yalwata shi har sai ya fi duniya fadi, shi kuma jahilci ya na gadar masa da kunci da killacewa , saboda haka duk sa'adda ilimin bawa ya fadada sai kirjinsa ya kara buduwa ya fadada, kuma wannan ba ko wane irin ilimi ba ne ke gadar da hakan sai dai ilimin da aka gado daga manzon Allah (sallallahu alaihi wa sallam) kuma shi ne ilimi mai amfani, saboda haka ma'abota wannan ilimin su su ka fi budadden kirji da yalwatacciyr zuciya cikin dukkan mutane, kuma su su ka fi kyakkyawan hali da kyan zamantakewa.
Daga cikin abubuwan da ke bude zuciya: akwai komawa ga Allah subahanahu wa ta'ala, da kaunarSa da zuciya dukkaninta da fuskanta zuwa gare shi, da ni'imtuwa da bautarShi, domin babu wani abu da ya fi wannan bude zuciyar bawa, har zaka same shi wani lokaci ya na cewa; ko cikin aljanna na samu irin wannan yanayi na jin dadi, to lallai ina cikin rayuwa mai dadi.
Kuma lallai kaunar Allah na da tasiri mai ban mamaki a cikin bude zuciya da kwanciyar hankali, da sanyin rai babu wanda ya san shi sai wanda ya tsinkaye shi, kuma duk sa'adda kaunar Allah ta fi karfi da tsanani, zuciya ma ta fi fadada da buduwa, ba ta kuntata har sai ta ga yan zaman banza wadanda su ka shantake ga barin wannan sha'anin. Kallon su kwantsa ne ga idonsa cudanya da su kuma zazzabi ne ga ransa.
Daga cikin mafi girman sabubban da ke jawo kuncin zuciya akwai kawar da kai daga Allah ta'ala da rataya zuciya ga waninSa, da gafala daga ambatonSa, da kaunar waninSa domin duk wanda ya kaunaci wani abu koma bayan Allah sai an azabtar da shi da wannan abin, kuma a kunkume zuciyarsa a cikin kaunar wannan wanin Allan, don haka duk fadin kasa babu wanda ya fi shi rashin rabo, kuma babu wanda ya fi shi shiga bakin ciki, kuma babu wanda ya fi shi kuntatacciyar rayuwa, kuma babu wanda ya fi shi gajiyayyar zuciya, saboda haka soyayya ce kala biyu, daya daga cikinsu ita ce aljannar duniya, da farin ciki a rayuwa, da jin dadin zuciya, da ni'imar ruhi kuma abincinsa, da maganinta, bugu da kari! Ita ce ma rayuwarta da natsuwar ido gare ta, ita ce kaunar Allah Shi kadai da dukkan zuciya, da karkata da nufi da dukkanin soyayya zuwa gare Shi.
Wata soyayyar kuma ita ce azaba ga rai da bakar rayuwa da kurkukun zuciya da kuncinta, kuma ita ce sababin radadi da rashin albarka da wahala, watau kaunar wanin Allah mai tsarki.
Kuma daga cikin sabubba masu bude zuciya; akwai dawwama a kan ambatonSa cikin ko wane hali kuma a ko wane wuri, don zikiri ya na da tasiri mai ban mamaki a cikin buduwar zuciya, da ni'imtuwarta. Haka nan kuma gafala daga zikiri ya na da tasiri mai ban mamaki cikin sanya kuncinta da daure ta da azabtar da ita.
Daga ciki akwai kyutata wa halittu da amfanar su da abin da mutum ke iyawa na kudi da matsayi da taimako na jiki da karfi da nau'uka na kyutatawa, domin lallai mai yawan kyauta da kyautatawa ya fi kowa budaddiyar zuciya a cikin mutane da kuma dadin rai da ni'imar zuciya. Marowaci kuma wanda babu wata kayutatawa a tare da shi ya fi kowa kuntatacciyar zuciya da rayuwa mara albarka kuma ya fi kowa shiga bakin ciki da damuwa.
Hakika Manzon Allah Ya buga misalin marowaci da mai bada sadaka kamar yadda ya zo a cikin sahihul Bukhari, misalinsu kamar wasu mutane ne guda biyu wadanda su ke sanye da riguna manya wanda aka yi da bakin karfe, duk sa'ilin da mai bada sadaka ya himmatu zuwa ga bada sadaka sai rigar ta kara yalwa ta fadada har sai tufafinsa ya ja kasa ya share gurabun takunsa. Amma shi ko marowaci duk sa'adda ya yi nufin ya yi sadaka sai ko wane karfe ya kankame a gurbinsa ba zai fadada masa ba.
To wannan shi ne misalin yalwar zuciyar mumini mai bada sadaka, da fadadar kirjinsa, sannan kuma misalin kuncin zuciyar marowaci da dabaibayin da ke zuciyarsa.
Daga ciki akwai jarumta, lallai jarumi ya na da faffadar zuciya, da zurfin ciki. Shi ko matsauraci ya fi kowa matsattsen kirji da killatacciyar zuciya, babu farin ciki a cikinta haka nan ma babu jin dadi babu ni'ima sai dai gwargwadon abin da ke zuciyar dabbar gida, amma farin cikin rai da jin dadinsa da ni'imtuwarsa da annashuwarsa duk haramtattu ne ga duk wani matsauraci kamar yadda su ke haramtattu ga duk wani marowaci da duk wani wanda ya juya baya ga Allah mai tsarki, ya gafala daga ambatonSa wanda ya ke jahili game da sunayenSa da sifofin zatinSa wanda zuciyarsa ta rataya ga wanin Allah.
Kuma wannan ni'imar da farin ciki da annashuwa zai zame dausayi kuma aljanna. Shi wannan kunci da dabaibayin zai rikida a cikin kabari ya zama azaba kuma kurkuku. Saboda haka halin bawa a cikin kabari kamar halin zuciya ce a cikin kirji, game da ni'imtuwa ko azabtuwa ko fursuna, da. Ba a la'akari da annashuwar da ke bijirowa ga wannan zuciyar haka ma abin da ke bijirowa ga zuciyar (mai sadaka, jarumi masanin Allah da sifofinSa) na kunci a wasu lokuta, domin abubuwa masu bijirowa suna gushewa ne da gushewar sabubbabansu, saboda haka abin la'akari kawai shi ne sifar da zuciya ke kai, wannan shi ne zai tabbatar da yalwar zuciya ko dabaibayewarta don haka wannan shi ne ma'auni. Allah Shi ne wanda ake neman taimako daga gare Shi.
Daga ciki kai! Mafi girmansu ma ke nan; akwai fitar da zuciya daga sifar da ke jawo zargi ya wajabta azabtuwarta kuma mai shamakancewa tsakaninta da waraka, domin lallai mutum idan ya aikata sabubban da za su fadada masa zuciya amma bai fitar da wadannan sifofin abin zargi ba daga zuciya, to ba zai samu wani kaso ba na fadadar zuciya, kurewar abin da zai samu shi ne abubuwa biyu masu gasa akan zuciyarsa duk wanda ya yi galaba akan shi zai ginu.
Daga ciki akwai barin yawan kallo da magana da sauraro da cudanya da ci da bacci (sama da bukata), domin abin da ya karu akan bukata cikin wadannan ya na mamaye zuciya da radadi da damuwa, za su killace ta, su tsakace ta, su kuntace, ta kuma ta azabtu da su, ba haka kawai ba ma! Galibin azabar duniya da lahira daga wadannan abubuwan su ke. La'laha illallahu! Ka yi mamakin kuncin da ke zuciyar wanda cikin dukkanin wadannan illoli ya na da kaso, ka yi mamakin kuncin rayuwarsa! Ka yi mamakin munin halinsa! Ka yi mamakin tsananin taskatuwar zuciyarsa, la'ilaha ilallallahu! Ka yi mamakin girman ni'imar rayuwar wanda ya samu kaso daga cikin ko wace dabi'a cikin wadancan kyawawan dabi'un kuma himmarsa ta kasance ta na gewayawa a kanta ta na kai komo a gefenta, wannan ya na da rabo cikakke cikin fadin Allah madaukaki:
{إنَّ الأَبْرَارَ لَفِى نَعِيم} [الانفطار: 13]
Ma'ana: "lallai managarta suna cikin ni'ima" suratul Infidar aya ta 13.
Shi kuma wancan ya na da rabo cikakke cikin fadinSa madaukaki:
{وإنَّ الفُجَّارَ لَفِى جَحِيمٍ} [الانفطار: 14]
Ma'ana: "Kuma lallai fajirai suna cikin wutar jahima"
Tsakanin su akwai martabobi masu tazara babu mai iya kididdige shi sai Allah madaukaki mai yawan albarkatu.
Abin nufi anan shi ne lallai manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam ya kasance mafi kamalan halittu cikin dukkanin sifar da ke jawo fadin zuciya da yalwan kirzi, da abin da ke sa nutsuwar ido da aanshuwar rai, saboda haka shi ne mafi kamalan halittu cikin wannan fadin zuciya da rayuwar, da natso ido tare da abin da aka kebance shi da su na yalwar zuciya ta fili.
Kuma mafi kamala cikin biyayya gare shi su ne mafiya kamala cikin fadin zuciya da jin dadi da natso ido, kuma bawa ya kan samu yalwar zuciya ne da natso ido da dadin rayuwa gwargwadon biyayyar sa gare shi, saboda haka shi manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam shi ne kololuwar kamala cikin yalwar zuciya da daukakar Ambato da sauke nauyi, kuma mabiyansa cikin haka suna da kaso gwargwadon kasonsu cikin biyayyarsu gare shi, Allah Shi ne abin neman taimako.
Kuma haka nan mabiyansa su ke da kaso cikin kiyayewar Allah da kariyarSa da tunkudewar musibu daga barin su da karfafawarSa da taimakonSa gare su, da gwargwadon kasonsu a cikin koyinsu da Annabi sallallahu alaihi wa sallam, wani ya yawaita wani kuma ya karanta, saboda haka duk wanda ya samu alheri sai ya gode Allah, wanda kuma ya samu wanin haka to kada ya zargi kowa sai kansa.