تسجيل الدخول

مشاهدة النسخة كاملة : عشرة أسباب لمغفرة الذنوب ومحْو آثار السيئات


هيئة الإشراف
_16 _January _2014هـ الموافق 16-01-2014م, 12:34 AM
عشرة أسباب لمغفرة الذنوب ومحْو آثار السيئات


قال رحمه الله في كتابه "عدة الصابرين": (باب المنهيَّات يَمْحُوهُ الله سبحانه ويبطل أثرَه بأمورٍ عديدةٍ من فِعْلِ العَبْدِ وغيرِه؛ فإنه يبطلُه بالتوبةِ النَّصوحِ، وبالاستغفارِ، وبالحسنات الماحيةِ، وبالمصائبِ المكفِّرةِ، وباستغفار الملائكة، وبدعاء المؤمنين؛ فهذه ستة في حال حياته.
- وبتشديدِ الموتِ وكَرْبِهِ وسياقِه عليه؛ فهذا عندَ مفارقته الدنيا.
- وبهَوْلِ المُطَّلَعِ، ورَوْعَةِ الملَكين في القبر، وضغطته وعصرته له، وشدَّةِ الموقفِ وعنائه وصعوبتِه، وبشفاعة الشافعين فيه، وبرحمةِ أرحمِ الراحمين له.
فإن عجزت عنه هذه الأمور؛ فلا بدَّ له من دخولِ النار، ويكونُ لُبْثُهُ فيها على قدرِ بقاءِ خُبْثِهِ ودَرَنِهِ؛ فإنَّ الله حرَّمَ الجَنَّةَ إلا على كل طيَّبٍ؛ فما دامَ دَرَنُه ووَسَخُه وَخُبْثُه فيه فهو في كير التطهير حتى يتصفَّى).

وهو ملخَّص من كلام لشيخ الإسلام ابن تيمية رحمه الله كرره في مواضع من كتبه، ومنها قوله في رسالة "أمراض القلوب وشفاؤها" : (المؤمن إذا فعل سيئة فإن عقوبته تندفع عنه بعشرة أسباب:
- أن يتوب فيتوب الله عليه؛ فإن التائب من الذنب كمن لا ذنب له.
- أو يستغفر فيغفر له.
- أو يعمل حسنات تمحوها؛ فإنَّ الحسنات يذهبن السيئات.
- أو يدعو له إخوانه المؤمنون، ويشفعون له حيا وميتا.
- أو يهدون له من ثواب أعمالهم لينفعه الله به.
- أو يشفع فيه نبيه محمد صلى الله عليه وسلم.
- أو يبتليه الله في الدنيا بمصائب تُكفِّرُ عنه.
- أو يبتليه في البرزخ والصعقة؛ فيكفَّر بها عنه.
- أو يبتليه في عرصات القيامة من أهوالها بما يكفَّر عنه.
- أو يرحمه أرحم الراحمين.
فمن أخطأته هذه العشرةُ فلا يلومنَّ إلا نفسَه كما قالَ تعالى فيما يروي عنه رسوله: (يا عبادي إنَّما هي أعمالُكم أُحصِيها لكم ثمَّ أوفِّيكم إيَّاها؛ فمن وجدَ خيراً فليحمدِ الله، ومن وَجَدَ غيرَ ذلك فلا يلومنَّ إلا نفسَه).

ولشيخ الإسلام بسط طويل في شرح هذه الأسباب في كتاب الإيمان الأوسط.

طاهر جبريل دكو
_22 _November _2014هـ الموافق 22-11-2014م, 05:03 PM
SABUBBAN KANKARE ZUNUBBAI DA SHARE MUNANAN AYYUKA GUDA GOMA DA
Ibnul Kayyim a cikin littafinsa mai suna UDDATU-SSABIRIN ya ce: "Babi; zunubbai da laifuffuka Allah kan shafe su Ya bata tasirin su da abubuwa masu yawa daga aikin bawa da waninsa.
Lallai Shi Ya kan bata su da; kyakkayawr tuba, da istgfari, da kywawan ayyuka masu share munana, da musibu masu kankare zunubbai, da istigfarin mala'iku, da addu'o'in muminai. Wadannan guda shida kenan a halin rayuwarsa.
Da magagin mutuwa da zafinta. Wannan a yayin barin sa Duniya kenan.
Da tashin hankali yayin shiga kabari, da firgicin mala'iku biyun nan a cikin kabari, da kuncin kabari da matsarsa, da tashin hankali na tsayuwar kiyama da wahalarsa da ceton masu ceto a filin kiyama da jin kan mafi jin kan masu jin kai (watau Allah (سبحانه وتعالى).
Idan wadannan abubuwan suka kasa samar masa da gafara, to babu makawa sai ya shiga wuta. Zamansa a cikinta zai kasance gwargwadon wanzuwar zunubbansa da daudarsa, domin Allah Ya haramta Aljanna face ga dukkanin wani tsarkakakke, saboda haka matukar daudarsa da kazantarsa na nan tare da shi to shi zai kasance a cikin zugazugin tsarkakewa (watau wuta) har sai ya tsaftata.
Wannan kulasa ce ta maganar Shekhul Islam Ibnu taimiyya – Allah Ya yi masa rahama- ya maimaita shi a wurare dabam dabam a cikin littattafansa, daga ciki akwai fadinsa a cikin littafinsa mai suna ; (AMRADUL KULUB WA SHIFA'UHA) watau cututtukan zuciya da magungunansu. Ya ce: Mumini idan ya aikata mummunan aiki zai kubuta daga horo da sabubba guda goma:
Ko dai ya tuba sai Allah Ya karbi tubansa. Domin mai tuba daga zunubi kamar wanda ba shi da zunubi ne.
Ko kuma ya yi istigfari sai Allah Ya gafarta masa.
Ko ya yi kyakkyawan aiki da zai share shi, domin kyawawan ayyuka suna tafiyar da munana.
Ko 'yan uwansa muminai su yi masa addu'a su nema masa ceto a halin rayuwarsa da bayan ya mutu.
Ko kuma su bashi kyautan ladaddakin ayyukansu don Allah Ya amfanar da shi da su.
Ko Annabinsa Annabi Muhammadu (صلى الله عليه وسلم) ya cece shi.
Ko Allah Ya jarrabe shi a Duniya da musibu sai su zama kaffarar zunubbabnsa
Ko Allah Ya jarrabe shi a rayuwar barzahu haka ma da somewa sakamakon firgici sai Ya kankare masa zunubbansa da shi.
Ko Ya jarrabe shi da tashin hakalin da zai zame masa
Kaffara a filin kiyama.
Ko kuma mafi jin kan masu jin kai (watau Allah) ya ji kan sa.
To duk wanda wadannan sabubba goman suka kubuce masa ka da yazargi kowa sai kansa kamar yadda Allah (تعالى)Ya ce a cikin abin da ManzonShi ya ruwaito daga gare shi:
Ma'ana: "Ya ku bayiNa! Kawai ayyukanku ne Na ke kididdige muku, sa'annan in saka muku a game da su, saboda haka wanda ya samu alheri sai ya gode Allah, wanda kuma ya samu koma bayan haka, to ka da ya zargi kowa face kansa.
Kuma Shekhul Islam Ya fadada cikin fashin baki da shrhin wadannan sabubban a cikin littafinsa mai suna (AL'IMANUL AUSAT).